Chapter 12
Chapter 12
Kallon Hajjah Hauwaa yayi wadda take mishi kallon mamaki ya yamutsa fuska yana cewa "a had'a min ruwa a toilet zan yi wanka " Sai lokacin bakin ta ya bud'e ta iya cewa "yanzu shikenan Sabeer an barta baza'a d'auki mataki a kanta ba " "ni tayiwa laifi koh, kuma nace ta zauna kada ta tafi ko'ina don haka ku Kyale ta idan kuma naji anyi mata wani abun raina zai iya 6aci kum......" Kafin ya k'arasa fad'i abin da zai fad'a Dr Ahmad d'an fillo yace "kayi hak'uri kada ranka ya 6aci Sabeer baza'a yi mata komai ba komai ya wuce " ya k'arasa fad'i yana shafa kanshi tamkar wani k'aramin yaro. Kan shi ya gid'a idon shi na kan ciwon da ya d'an ji akan k'afar shi, Dr Ahmad d'an fillo ya kalli Hajjah Hauwaa yace "ba'a haka yace a had'a mishi ruwa zai yi wanka ba? " Dafa kafad'ar Sabeer tayi tare da cewa "zo muje da kaina zan had'a maka " Kamo hannun shi tayi ta jashi zuwa upstairs inda bedroom d'in shi yake (da yake yana da bedroom a side d'in kakannin nashi), da kallo Dr Ahmad d'an fillo ya bi Sabeer har ya daina hango shi tukunna ya juya ya fita. Bayan Sabeer yayi wanka ya fito ya shirya cikin Kayan da Hajjah Hauwaa ta ajiye mishi saman bed, ya sanya su sannan ya kwanta kan sofa hannun shi d'auke da I pad d'in shi yana research a ciki. "Assshhh " Ya furta a hankali sakamakon maganin da Hajjah Hauwaa ta sanya mishi a d'an ciwon da glass cup ya ji mishi, bakin ta ta sanya tana hura mishi k'afar tare da cewa "sannu " Ta furta hakan tana rufe robar cream d'in da ta shafa mishi, d'an 6ata fuska yayi yana cewa "shine baki fad'a min zaki sa min ba koh? " Da shagwa6a ya fad'i hakan, nan ta fara rarrashin shi sai da ta ga ya hak'ura tukunna ta fita daga bedroom d'in don ta barshi ya huta. 8pm Sabeer ne tsaye gaban dressing mirror yana sake gyara necktie d'in suit d'in shi, yayi kyau sosai cikin blue d'in suit ba kad'an ba shoes d'in shi black ne haka watch d'in hannun shi samfur d'in Gucci yayi kyau gashin kanshi yasha gyara sai shek'i yake. Turo kofar bedroom d'in akayi Mummy ce ta shigo tasha gayun ta cikin wani tsadaddan black less mai adon flowers ash Sai ta nad'a laffaya ash colour mai kyallen duwatsun silver sai manya flowers black a jikin laffayar tayi kyau sosai baka d'auka ta haifi Sabeer ba gefen ta kuma wata matashiyar kyakkyawar yarinya ce tana sanye cikin wata gown na English wears sun kamata sosai daganin ta kasan idon ta a bud'e yake tasha wani uban hill shoes ga attachment da tasha sai farce daga ni sanya su tayi, fuskar nan tasha heavy make up sai wani iyayi take, kallo d'aya zaka yi mata kasan kusan sa'anni ce da Sabeer a shekaru. Kallo d'aya Sabeer yayi mata ya d'auke kai don bai ga alamun tana da hankali ba irin wannan haukan kwalliyar da tayi, matsalar shi da Mummy kenan jajibo irin wad'annan yaran marasa kamun kai. Cikin murmishi d'auke a fuskar Mummy ta k'arasa inda Sabeer yake tayi hugging d'in shi tare da cewa "Wow son ka ganka kuwa U look so cute " "Thanks Mumy" Ya furta tamkar baya son magana, cikin murmishi Mumy tace "Son ga Fadilah ko baka gane ta ba ne? " D'auke kanshi yayi tare da cewa "bansan ta ba" Yana gama fad'in yayi gaba, kunya ce ta d'an kama Mumy don bata zaci Son zai mata haka ba ya kunyatar da ita a gaban d'iyar k'awar ta, wayance wa tayi da cewa "Kyale shi Fadilah ranshi ne a 6ace don baya son wannan party da na had'a mishi " Sai lokacin matashiyar yarinyar da Mumy ta kirawo da Fadilah ta saki murmishi don ta shiga damuwa a time d'in da Sabeer ya nuna baisanta ba. Kamo hannun ta Mumy tayi suka fito zuwa compound d'in gidan friends d'in Mumy da yaran su zuwa 'yan uwan Sabeer ne sai shiga mota ake suna tafiya zuwa hall d'in da za'a yi party. Wata black Range Rover na hango a tsakiyar compound na gidan sai shek'i da d'aukar ido take daganin ta kasan sabuwa ce, nan na hango Sabeer ya nufi wajen cikin takun tafiyar shi kamar bayason taka k'asa, kafin ya k'arasa wajen tuni driver ya bud'e mishi bayan motar yana k'araso wa shiga yayi ya zauna sannan driver ya rufe murfin motar, cikin sauri ya shiga mazaunin driver ya yiwa motar key ya fara tafiya a hankali don Sabeer bai fiye son ayi gudu dashi a mota ba idan bashi yake driving ba. Suna k'arasa wa katafaren hall d'in da aka kama don yin partyn ko'ina yasha decorations na blue white, wajen yayi kyau sosai ta had'u ga wani cake mai hawa uku shima kalar shi blue and white ne yayi kyau sosai ya tsaru. Ga manyan hamshak'an masu kud'i friends na Mumy da yaran su, ga 'yan uwan Sabeer nan mazan su da matan su kowa yasha gayun shi na kece raini don kowa yana ji da kanshi ta fannin kud'i da gogewar ilimi da wayewa. Driver yana yin parking motar da Mumy take ciki tayi parking kusa da motar da Sabeer yake ciki, nan Mumy ta fito ita da wannan Fadilah suka k'araso inda Sabeer yake, Mumy ta bud'e kofar motar tare da cewa "Son fito mu tafi mutane na jiran mu " Cikin wani tak'ama da had'e fuska ya ziro k'afar shi d'aya waje sai da ya d'auki wasu seconds tukunna ya fito da d'ayar kafin kuma ya fito da dukka jikin shi zuwa waje. Kallon shi Fadilah take tamkar ta lashe shi saboda tsabar maitar son shi da take, ita fah da zai aminta da ko bazai aure ta ya yarda suna biyawa kansu buk'ata don tasan Sabeer irin shine wanda zai yi mata yanda take so, amman zata fara gwada sa'ar ta ko zatayi nasara... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz This page is for U my Momma na (Aunty Maijiddah Musa) thanks for luv nd support, Allah ya raya zuri'a Allah ya bar zumunci ❣ PAGE 17-18 Yana gama fitowa a mota ne Mumy ta kama hannun shi suka fara tafiya zuwa cikin hall d'in, sai da suka kusan shigewa hall d'in tukunna Fadilah ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad'a da sauri ta bi bayan su don tana Buk'atar jerawa da Sabeer. Bayan sun shiga ciki ne Mumy da Sabeer suka zauna waje d'aya sai wani 6a66ata rai yake, gaba d'aya hayaniyar duk ta isheshi ya gaji ga 'yammatan da suka dame shi da hayaniyar su kowacce tana kok'arin cusa kanta a wajen shi, amman yanda kasan da dutse suke magana haka yake share su, Gashi kowacce da nata gift's da takawo mishi, Mumy sai wani murmishin jin dad'i take ganin yanda ake son d'anta. Gaba d'aya Mumy ta mance da 30 minutes kawai Sabeer yace zai yi, bata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104