Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,173 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wannan maganganun babu dad'i " Cewar Jiddah tana turo baki wata uwar harara Aunty Fadilah ta aikawa Jiddah kafin tace "Daman ina zaki ga rashin dacewar hakan bayan an shanye mana ke da Sabeer har da Yaya Hussein, idan ban da k'addara ina mu ina neman aure a irin wannan wurin " Ta k'arasa maganar tana jan tsaki, cikin rashin kunya Jiddah tace "Allah Aunty kika sake magana sai na gayawa Daddy tun da har kin mance abin da Daddy ya fad'a kafin mu taho " Wata hararar ta sake zabga mata tamkar idanunta ya fad'o amman bata sake magana ba don tasan sarai halin Jiddah tsaf zata fad'awa Daddy kuma tasan tsaf zai ci mutuncin ta. Sai bayan la'asar da suka yi sallah suka taho da tarin kayan snacks da drink's d'in da Jiddah ta bayar akayi, sai kuma cikin kud'in da suka kawo aka basu tukwicin dubu d'ari biyar, a wulak'anci suka kar6a kud'in babu sallamar arzik'i suka tafi. Sai bayan tafiyar su ne aka saki jiki ana kallon lefen akwatina har 15 kowacce cike da kaya damk'an dakyar bag's ake zuge zipe saboda cikar kayan. Duk kwakwkwafar mutum dai ya hak'ura da ganin kayan, k'arshe bayan an gama gani Aunty Aliya suka tattara su aka zuba su cikin d'akin Suhaima, daman Suhaima bata gidan tana can gidan Babaa Lantana ita da wasu kawayen ta biyu wad'anda suke shiri dasu. Sai dare Suhaima ta dawo gida kasa kallon kayan tayi sabida kunya sai da Aunty Aliya ta dunga fito mata dasu tana gani a haka shima Yah Aliyu ya tarar dasu ya d'an kalla sama sama kafin yace "Masha Allah kanwar tawa tayi goshi sai dai gaskiya kayan sunyi yawa sosai wallahi" "Gaskiya kam sunyi kyau sai dai yawan su mu muke ganin haka amman su ba wani abun ne rabon ta ne" Cewar Aunty Aliya kenan tana bud'e bag d'in da aka zuba sark'ok'i, sannan ta d'ora da cewa "Yanzu ya zamu yi da motar ta? " Sai lokacin Suhaima tasan har da mota haka ma Yah Aliyu. "Tabd'ijam har mota fah kika ce Aliyah? " "Kwarai kuwa baka ganta a waje ba? " "Naga mota na d'auka ko lalace musu tayi " "A'a ta Suhaima ce " "Yanzu yanda za'a yi idan Sabeer yazo sai ya tafi da ita ya ajiye mata acan gidan nashi ko kuma Jiddah ta tafar mata da ita ta ajiye " "Haka za'a yi kuwa don shine mafita nan ba wajen zaman ta ba ne " Suhaima tana jin su duk wannan tattaunawar da suke bata ce komai ba sai tagumi da ta yi, bayan su Yah Aliyu sun fita daga d'akin har Yah Aliyu yana tsokanar ta da "ke fah yanzu Suhaima kin zama matar manya koh? " Murmishi kawai tayi ta turo mishi baki dariya yayi ya fice abin shi Aunty Aliyah na taya shi. Suna fita wayar Suhaima ta d'auki k'ara ganin Sabeer ne ya sanyata d'auka had'e da yin sallama, lumshe idanun shi yayi kafin ya bud'e su yana amsa sallamar ta throughout yau bai ji wannan muryarta ta ba. "Amarya ta kinsha k'amshi nayi missing naki fah Baby yaushe zan zo? " D'an murmishi ta saki mai d'an sauti sannan tace "sai nan da 4 week's zaka zo " D'an zaro ido yayi kamar tana ganin shi yace "Washsh! Allah nah kice Baby sai dai ki zo dubiya ta asibiti don nasan sai Doctor ya kwantar dani " Dariya ta kyalkyale da ita tana cewa "Haba lallai da ka cika rago kuwa" Da sigar tsokana ta fad'a. "Baby nine ragon koh, tabbb yarinya zaki bayani ne idan na rik'e ki a hannuna a time d'in ne zaki fahimci irin jarumta ta " Gaban Suhaima ne ya d'an fad'i har ta kasa magana duk da bata fahimci maganar tashi sosai ba, jin tayi shiru ya sanya shi murmushi ya basar da zancen da cewa "Baby kaya sun yi miki kuwa? " "Laaa sunyi kyau sosai sai dai Sabeer gaskiya sunyi yawa, bayan haka har da mota fah sai kace wadda za'a siyar " Dariya ya d'an yi jin yanda ta k'arasa maganar cikin shagwa6a. "Baby nah kenan toh ai motar ba ni na baki ba Daddy nane ya baki, kuma zancen yawan kaya ki daina zancen su don kin cancanci fiye da haka " "Ina godiya sosai a mik'a min godiya ta wajen Daddy " "Toh Baby yanzu mene tsare tsaren bikin ne, mai kuke son yi, don ina son zan zo nida friend nawa Musaddiq " "Daman kana da aboki ne? " "Baby ina da aboki mana amman duk acikin su da d'aya na aminta dashi wato Musaddiq sai dai shi miskili ne na ajin k'arshe shi yasa baki san shi ba " "Ayyah amman wannan kafin ya samu macen aure zai sha wahala " "Baby ai yana da aure matar shi Mufidah da yaran shi twins sai dai yana rik'on d'iyar Yayan shi wanda ya rasu" (dafatan masu karatu baku manta labarin littafin YAYI SAKE ba), nan Sabeer ya bata d'an labarin shi a takaice sosai Suhaima ta matuk'ar tausaya musu jin irin gwagwarmayar da Musaddiq yasha a cikin rayuwar shi. "Allah ya jik'an Abubakar Sadeeq" "Amin ya rabbi Baby, yanzu kije ki kwanta dare yayi ranar friday ko Saturday zan shigo" "Okay Allah ya kawo ka lafiya " "Amin Baby nah kiyi bacci mai dad'i da sweet dreams dani aciki " D'an murmishi kawai tayi nan suka yi sallama abin su zuciyar kowannen su cikin farinciki. **** **** **** Bayan kwana 2 da kawo lefe Jiddah tazo ta d'auki Suhaima don kai d'inkin kaya, kaya da D'an yawa ta zazza6o cikin kayan lefen ta had'a da wanda zatayi amfani dasu ranar bikin sannan ta had'a da wanda Yah Aliyu da Aunty Aliya suka yi mata, wajen tailor d'in Jiddah suka kai bayan sun gama za6ar irin style's d'in da suke so aka yi total na kud'i bana wasa ba nan take Jiddah ta biya su ko ragi babu don tana son su cika mata alkawari don nan da 2 week's zata dawo ta kar6e su dukka, duk wannan kud'in d'inkin a wajen Sabeer Jiddah ta kar6o, sannan suka zarce zuwa gidan Jiddah yini Suhaima tayi acan sai yamma driven Jiddah ya dawo da ita gida, motar Suhaima kuwa tana gidan Jiddah a ajiye don tun washe gari Yah Aliyu ya fad'a mata a waya ta turo driven ta ya dauka sai ya hau taxi drop har k'ofar gidan sai ya koma da motar. Sai shirye shiryen biki ake ta koina duk da family d'in D'an fillo basa maraba da shigowar Suhaima cikin su hakan bai hanasu shirya bikin ba fiye ma dana kowanne d'a a gidan,har dinner suka shirya ta family da suke yi har da yin ankon su kamar irin gasken nan, haka ta 6angaren Suhaima ma sosai Yah Aliyu da Aunty Aliyah suka zage wajen shirya bikin nasu dai dai gwargwadon iyawar su, Jiddah sun gama tsara event's d'in da zasu yi dinner, walimah, kamu sai kuma dinner d'in family d'in Sabeer wadda zasu yi ranar da aka kawo amarya........ Ku cigaba da hak'uri da ni Fan's. Aishat A Muh'd ✍🏻 [3/29, 8:54 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI*

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});