Chapter 7
Chapter 7
bata dad'e ba tace wa k'awayen ta zata tafi gida, don kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata dawo ba yayi mata fad'a, aikuwa suka ce sai dai tayi gaba su ba yanzu ba, haka Suhaima ta kamo hanya tana tafiya ita kad'ai cikin sauri. Sauri sauri take gaba d'aya hankalin ta yayi gida, tana tsoron kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata nan. D'ago kan da zatayi ta hango wata kyakkyawar yarinya a tsaye kusan sa'ar ta, sai dai zata ba Suhaima wajen shekara biyu, sai wani dattijo a tsaye shima a gefen ta a tsaye da alama sun k'agu da tsayuwar da suka yi. A hankali Suhaima ta k'arasa inda suke tsaye har zata wuce su, da sauri yarinyar nan ta k'arasa wurin Suhaima tace " 'yar uwa idan baza ki damu ba don Allah muna son ki taimaka mana da ruwa zamu sanya a mota " D'ago kanta Suhaima tayi ta kalle ta sannan tace "Toh ba matsala bari na k'arasa gida na d'ebo muku" Murmishi yarinyar tayi tare da cewa "Idan baza ki damu ba zan bi ki don na gaji da tsayuwar " "Ba komai mu je " "Ngde 'yar uwa " Kallon dattijon nan tayi tare da cewa "Malam Habu bari mu je gidan su mu kawo ruwan " Sai da dattijon nan da yarinyar ta kirawo da Malam Habu yayi d'an jim kad'an kafin yace "Toh amman kada ki dad'e kinga kada yamma tayi mana a hanya " Gid'a kanta tayi sannan ta juya wajen Suhaima tace "Mu tafi koh? " A nutse suka fara tafiya yarinyar tana yiwa Suhaima hira sai dai bata fiye bata amsa ba daga ehh sai a'a, can sai kuma tace "Ni sunana Hauwaa amman 'yan gidan mu na kirana da Jiddah saboda sunan kakar mu ne " Murmishi Suhaima tayi tare da cewa "Sunan ki mai dad'i " "thank you, ke fah what's your name? " "My name is Suhaima Umar" "Wow nice name, daman kina jin turaci? " "Yeah but kad'an kad'an." "Good, kin gama primary ne " "Ehh na gama ina jiran result ya fito na cigaba " "Amman kin birge ni Suhaima, zamu iya zama friends? " "Why not " Cewar Suhaima, nan kowacce ta bada d'an yatsan ta suka k'ulla friendship, tukunna suka k'arasa shiga gidan da sallama. Gaban Suhaima ne ya fad'i ganin Yaya Aliyu a tsaye yana safa da marwa, ga Yaya Aliyah ma a tsaye fuskar ta d'auke da damuwa da alama dai ita ake nema. Suna ganin ta gaba d'aya sukayo inda take Aliyu ya sanya hannun shi saman kafad'ar ta ya rik'e da d'an k'arfi yace "Ina kika zauna Suhaima, ba na hana ki fita kasuwa ba " Idanun tane yayi raurau kamar zata yi kuka, batason ganin damuwar Yayan nata ko kad'an, don haka sai tace "Kayi hak'uri Yaya bazan sake ba " Kallon ta kawai yake bayason wani abu ya samu tilon k'anwar tashi. "I'm so sorry Yayah bazata sake ba " Aliyu da Aliyah suka ji saukar muryar Jiddah, da sauri suka kallo inda take don sam basu kula da ita ba hankalin su gaba d'aya yana kan Suhaima. Kallon Suhaima Aliyu yayi irin na neman k'arin bayanin ina ta samu wannan yarinyar, fahimtar hakan da Suhaima tayi ne ya sanya ta bud'e baki tayi mishi bayanin had'uwar su. Ba wanda yayi magana sai da Jiddah ta gaida su sannan suka amsa, kallo d'aya zaka yiwa Jiddah kasan ta samu tarbiyya mai kyau a wajen manyanta. Babu 6ata lokaci Aliyu ya samu jarka ya zuba ruwa taf a ciki, sannan ya d'auko ta Suhaima da Jiddah na bin shi a baya har zuwa wajen da motar su tayi parking. Bayan sun k'arasa ne Aiyu suka gaisa da Malam Habu sannan ya kar6i ruwan ya zuba a mota yana godiya, mik'a wa Aliyu jarkar ruwan yayi yana sake godiya, girgiza kai Aliyu yayi tare da cewa "A'a ka barshi a wurin ka idan buk'atar hakan ya taso muku a gaba kwayi amfani dashi " Malam Habu cikin girmama karamcin Aliyu yace "Mun gode d'an samari Allah ya saka da alkhairi " Daga haka Malam Habu ya shiga cikin mota yayi mata key ya tasar da ita, sannan ya d'ago kanshi ya kalli Jiddah da bata da alamun shigo wa motar yace "Jiddah taho mu tafi yamma nayi " Maimakon ta bawa Malam Habu amsa, sai ta juya wajen Aiyu ta rik'e hannayen shi duk biyun tace "Don Allah Yaya Aliyu zan na zuwa nan ganin Suhaima, Allah tun da na ganta naji ina sonta sosai, gashi mun k'ulla k'awance da ita, kuma ina son ka zama Yaya nah " D'an murmishi Aliyu yayi shi duk wanda yake k'aunar 'yar k'anwar shi, to shima yana son shi, dafa kan Jiddah yayi tare da cewa "Kada ki damu Jiddah na d'auke matsayin k'anwa, kuma duk lokacin da kike son zuwa wajen Suhaima ki zo ki ganta " Dariya Jiddah ta sanya ita da Suhaima kafin tace "Nagode sosai Yaya Aliyu " Sannan ta jiyo wajen Suhaima suka rungume junan su, dakyar ta iya sakin Suhaima ta shiga mota har da d'an hawayen ta, don ji tayi kamar ta zauna a wurin su, suna tsaye Aliyu da Suhaima suna d'aga musu hannu har suka daina hango motar su. Sannan Aliyu da Suhaima suka juya zuwa gida, sosai Suhaima ta fara jin kewar Jiddah kamar wad'anda suka shekara da sanin junan su, ita haka kawai taji Allah ya sanya mata son Jiddah kamar irin 'yar uwar nan ta jini... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM DEDICATED TO MY SADEEY SANAZ PAGE 9-10 Haka lokaci ya cigaba tafiya, zumunci tsakanin Suhaima da Jiddah ya k'aru sosai wanda takai duk weekend sai ta zo ganin Suhaima, sai dai Aliyu sam yak'i bata fuskar ta tambaye shi taje gidan su Jiddah, sai dai ita duk weekend k'afar ta yana hanyar zuwa gidan su Suhaima ko kad'an bata damu da rashin zuwan Suhaima gidan su ba, tasan komai lokaci ne akwai lokacin da zata zo mata gidan su, aminci sosai suke yi. Haka Aliyu, Aliyah dasu Babaa Lantana da Baba Adamu duk sun saki jiki sosai da Jiddah, saboda kirkin yarinya ga kuma yanda take girmamasu, duk da sun san daga gidan kud'i ta fito, don da ganin irin sutturar da take sanya wa da irin motar da ake kawo ta a ciki kasan iyayen ta ba k'aramin masu kud'i ba ne, gashi indai zata zo kowa a cikin su da irin tsarabar da take kawo mishi, musamman Suhaima k'awar ta, yini guda cur zata yi musu suyi ta zagaya gonar Yaya Aliyu da wurin da ya ke6en ce don yi kiwo a ciki, sam Jiddah ko a fuska bata nuna tana kyamar su. Ana cikin haka exam d'in su Suhaima ta fito taci wata makarantar secondary da take a birni, nan Yayan ta yayi mata ciko ciko ta samu gurbin karatu na jss 1. Cikin k'ank'anin lokaci Suhaima ta fara zuwa makaranta, Jiddah tayi murna sosai da cigaban makarantar Suhaima, gashi kuma Jiddah idan tazo wani lokacin tana k'ara fahimtar da ita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104