Chapter 70
Chapter 70
_To fah reader's kunji tunanin Dr Faridah ko zata yi nasara akan Suhaima ta rabata da Sabeer, ina jiran comments naku yanzu labari zai fara, ƙų ¢ıɠąცą ɖą ცıŋą ɖơŋ ʝıŋ ყąŋɖą ʑąɬą ƙąʂąŋ¢ɛ_. Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/9, 6:30 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ *PAGE 85-86* Da kallon mamaki Sabeer da Suhaima suka bita dashi kawai kafin kuma Sabeer ya rik'o hannunta yace "Sorry Baby nah akan abin da Mumy take miki bana jin dad'in haka ko kad'an " Cikin rarrashi ya k'arasa maganar gashi fuskar shi d'auke da damuwa, d'an murmishin yak'e Suhaima ta saki sannan tace "Kada ka damu don Allah komai mai wuce wa ne, mu tafi ka ga Baby kada ka makara a office ". "Thank U Baby nah da yanda kike da fahimta i luv U " Suhaima na shirin bashi amsa kenan Jiddah ta lek'o da kanta tana cewa "Don Allah Yah Sabeer mene haka tun d'azu kuna tsaye anan ka hanata shigowa " Hannun shi ya sanya tare da janyo kunnen ta d'aya yace "Jiddah kin raina ni da yawa zan miki duka na tsayar da ita d'in mata ta ce ai " D'an ihu ta saki na jin zafi kafin ta marairaice fuska tace "Sorry Yah Sabeer na tuba na daina " Yanda tayi d'in dole yasan ya shi murmishi ya cika mata kunnen, kamo hannun Suhaima tayi suka wuce cikin gidan. Masha Allah abin da Sabeer ya fad'a lokacin da ya kar6i Babyn fara ce tas har wani ja ja take yi kyakkyawa da ita ta d'ebo kamannin D'an fillo family, wani son yarinyar ne ya shiga zuciyar Sabeer har yana imagine gashi Suhaima ta haifa mishi Baby yana d'auke da shi. Kallon Suhaima yayi wadda take zaune kusa dashi tana lek'en Babyn don itama kanta tayi mata kyau ba kad'an ba. "Baby kema kina so koh, ki haifa mana mu ma please " D'an murmishi tayi kafin tace "Toh my dear kayi addu'a Allah ya bamu masu albarka " "Amin Baby " Jiddah ya mik'awa Babyn don ya makara ma sosai, tashi Suhaima tayi ta rakashi har bakin mota suka yi sallama ta dawo cikin gidan, bayan ta gama ganin Babyn ne sai ta gyarawa Jiddah bedroom nata sannan ta wuce kitchen don shirya abincin rana. Tana tsaka da girkin 'yan uwan Jiddah suka fara zuwa gidan kasa fita tayi su gaisa tayi don gabanta sai fad'uwa yake, dakyar ta k'arasa girkin ta zuba a foodflaks sai kawai taja kujera a kitchen ta zauna tare da had'a kai da gwiwa tana tunani. Awannan yanayin Jiddah tazo ta same ta tausayin Suhaima ne ya kamata, dafa kafad'ar ta tayi a tsorace Suhaima ta d'ago kanta ganin Jiddah ce ya sanyata sakin ajiyar zuciya. "Suhaima ki rage tsoron su fah wallahi, taya zaki zauna a kitchen bazaki fito ba saboda su? " "Uhmmm Jiddah wallahi bana son kallon wulak'anci da k'ask'ancin da suke min, ina jin tsoron fita mu gaisa dasu kada su gwasale ni kamar yanda suke yi min " "Kada ki damu Suhaima komai zai wuce amman baza ki tak'ura kanki ba saboda su don haka ki fito daga kitchen " Babu yanda zatayi haka ta fito hannunta rik'e dana Jiddah, wani kallo na wulak'anci suka bita dashi kamar yanda Suhaima ta tsani ayi mata, babu wanda ya amsa gaisuwar ta sai ta6e baki da suke Jiddah ma sai da ta samu alakoran harara a wajen su. Bedroom d'in ta Jiddah ta kaita ta zauna amman duk da haka a tak'ure take har so take lokacin tashin Sabeer daga office yayi yazo su wuce gida, duk da ya kirawo ta awaya amman ba'a kwanciyar hankali ta amsa ba mishi ba, har tunanin ranar suna take batasan irin wulak'ancin da zasu yi mata cikin mutane ba. Atak'ure take har zuwa bayan mangarib sannan Sabeer yazo suka tafi gida, kallo d'aya yayi mata ya fuskanci tana cikin damuwa girgiza kanshi yayi yana yana sauke numfashi dole ya takawa 'yan uwan shi birki akan abin da suke yiwa Babyn shi bazai jure ba ko kad'an ganin ta cikin damuwa. Duk damuwar da take tattare da ita sai da Sabeer ya cire mata ita ya mayar da gurbin farinciki a wannan daren sosai Suhaima ta k'ara jin wani son mijinta cikin zuciyar ta yanda yake faranta mata rai itama tana addu'ar Allah ya sanya ta haihu don cika mishi burin shi. Ranar suna tun safe Sabeer ya kaita don yak'i barin ta ta kwana ko komawa bata sake yi ba sabida yana gudun kada a sake 6ata mata rai duk da kuwa nacin da tayi mishi, sosai Sabeer da Suhaima suka kashe kud'i wajen had'a wa Babyn kaya da kuma ita kanta Jiddah don duk abin da suka yi mata baza su biyata abin da tayi musu ba ita kadai ce mai kaunar ganin su tare sai Daddy adukkan familyn Sabeer. Sosai Jiddah taji dad'i abubuwan da suka kai mata tayi musu godiya tare da addu'ar Allah ya basu suma yaran masu albarka, Sabeer yaji dad'in addu'ar da tayi musu sosai duk cikin 'yan uwanshi yafison Jiddah fiye da kowa don itace mai kaunar abin da yake so. Baby taci sunan Babar Khaleel wato Khadijah suna ce mata Islam, ansha suna sosai don har walima da yamma sai da aka shirya an kashe kud'i sosai, amman duk wannan abun Suhaima bata shigaba tana zaune waje d'aya kanta ma yake masifar ciwo sosai, gashi tasha kukan habaici da wulak'ancin da su kayi mata. Sai bayan mangarib 'yan uwa suka fara tafiya, zaune Suhaima take kan abin sallah idar da sallahr ishsha da tayi kenan tana addu'a cikin zuciyar ta tana mai tunanin inda Sabeer ya tsaya baizo sun tafi ba don kanta sosa yake ciwo kamar ya cire ga idanun ta da suka kumbura saboda kuka, ta kirawo phones nashi basa shiga dukka, gashi hadari ya had'u sosai sai walk'iya ake. "Munafuka har yanzu zaman me kike da baki tafi ba, mun gaji da ganin fah ya kamata kisan nayi " Cewar Aunty Fadilah 'yar autar su Daddy kenan tana wani hararar Suhaima, sunkuyar da kanta Suhaima kawai tayi idanun ta suna zubar da hawaye. "Wallahi na tsani yarinyar nan kyau kamar aljanna duk tabi ta asirce mana Sabeer sai yanda tayi dashi daman 'yan kauyen nan da shegen yin asiri" Dariya aka kwashe da ita irin mai k'ulawar nan suna cewa "Sai Auntyn mu fad'a mata dai munsan asiri tayi ta mallake mana d'an uwa don Yah Sabeer bazai ta6a son wannan talakar ba yana cikin hayyacin shi" Cewar Zahra kenan, bak'inciki da takaici ya ishe Jiddah cikin d'aga murya tace "Ke Zahra wallahi ki kiyayi kanki Allah zan fad'awa Yah Sabeer yaci uban ki matar shi kike fad'awa haka " Make mata bakinta Aunty Fadilah tayi tana cewa "Ta fad'a d'in ya kashe ta idan ya isa " Kuka Jiddah ta sanya saboda make mata bakin da tayi don da ba k'aramin zafi taji ba, yayi da Zahra take danna mata harara. "Ni na rasa abin da zamu yiwa wannan mayyar yarinyar ta rabu da Sabeer ba irin wulak'anci da bamu yi mata ba amman ta lik'e mishi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104