Chapter 28
Chapter 28
"Banason ki k'ara tafiya ba tare da na fad'a miki wani abu ba ina son kizo ki shiga mota akwai maganar da zan fad'a miki please " D'an jim Suhaima tayi daman ko da zai barta ta tafi batasan inda zata nufa ba gashi ta bar wayar Jiddah a cikin mota. "Na rok'e ki please " Sabeer ya furta hakan yana kallon ta, juyawa tayi ta fara tafiya kawai shima bin ta yake a baya har suka k'arasa inda yayi parking motar shi ya bud'e mata seat na gaba ta shiga ta zauna sannan ya rufe ya koma ya shiga mazaunin driver ya zauna yana nai mamakin kanshi yau wai shine yake bud'e wa wata mace k'ofar mota ta zauna lallai so ya canja shi daga d'abi'un halayyar shi na da zuwa wasu daban. "Suna na Sabeer Hussein d'an fillo, ke mene sunan ki? " Shiru Suhaima tayi bata yi mishi magana ba shima bai k'ara cewa komai sai da suka yi nisa da tafiya ta bud'e baki tamkar batason magana tace "Suhaima " A hankali ta furta hakan bata d'auka yaji ba sai da taji yace "Nice name " Jingina kanta tayi jikin kujerar da take zaune ta lumshe idanun ta, dan kallon ta Sabeer yayi ganin ta rufe idon ta ne yasa shi jan wani birki, a rikice Suhaima ta bud'e idon ta har ta buge kanta ta kalli gaban su ta d'auka wani abin ya faru sai taga ya cigaba da tuk'in shi ko kallo inda take bai yi ba, hararar shi tayi ta gefen ido tare da murgud'a bakin ta kad'an kafin ta koma ta sake lumshe idon ta. Dariya ce taso kubce mishi amman ya danne cikin zuciyar shi yana cewa wanna yarinyar akwai tsiwa huh, gaban wani gida yayi parking mai kyau da gani gidan kasan sabo ne tun daga wajen kasan an kashe kud'i sosai idan ka kalla. Jin an tsaya da motar yasa Suhaima bud'e idon ta ganin ba irin yanayin unguwar gidan su Jiddah ba ne yasa jiyowa ta kalle shi na alamr tambaya nan ina ne. Bai ce mata komai ba ya fito daga cikin motar ya bud'e mata ita ma sai tak'i fitowa tace "Nan ba gidan su Jiddah ba ne don Allah ni ka kai ni gidan su... " "Zan mayar da ke gida Suhaima but ina son ki bani wasu minute's akwai maganar da zamu yi " D'an kallon shi tayi sai taga babu wasa saman fuskar shi duk da a tsorace take dashi haka ta fito daga motar ya rufe sannan suka nufi cikin gidan duk takun d'aya da Suhaima zata yi gaban ta fad'uwa yake. Tura k'ofar gate d'in yayi ya shiga tana biye dashi, gate man na ganin shi ya zube yana gaida su Sabeer ne ya iya amsawa dakyar Suhaima kuwa bakin ta ne yayi mata nauyi ta kasa bud'e shi, gidan babba ne ya had'u sosai cikin parlourn gidan suka shiga. Zama yayi akan kujera ya d'ago kanshi yana kallon Suhaima wadda take tsaye k'ik'am tamkar wata soja yace "Suhaima ki zauna ina son ki ban hankalin shi da nutsuwar ki " Ba tare da ta kalle shi ba ta zauna don ta k'osa ta ganta a kusa da Jiddah. Shiru suka yi tamkar babu mutane a cikin parlourn har sai da Suhaima ta k'osa da shirun nashi tace "Kai nake jira fah " Tashi tsaye yayi ya dawo gaban ta ya zauna akan carpet d'in dake shimfid'e a k'asa, tsugunna wa yayi tamkar mai neman afuwa yace "Suhaima kin tuna ranar da muka fara had'u wa da ke tun daga lokacin na kasa manta ki zuciya kullum cikin tunanin ki take haka idanuna kullum cikin son sake ganin ki suke, na je wajen sau uku k'auyen ku neman ki but ko mai kama da ke ban sake gani ba sai ajiya Allah ya nufa zan sake ganin ki " Dan shiru yayi yana kallon Suhaima wadda take kallon shi take kuma sauraren abin da yake cewa cikin mamakin shi, ajiyar numfashi yayi kafin ya cigaba da cewa "Naji dad'i Sosai a lokacin da na ganki a takaice Suhaima zan sanar miki zuciya ta ta kamu da son ki! I luv U Suhaima i really luv U, ban ta6a son wata mace a duniyar nan ba sai ke ina son ki bani had'in kai na nemi soyayyar ki auren ki nake son yi da gaske Suhaim..... " Kasa k'arasa abin da zai fad'a yayi sakamakon ganin Suhaima da yayi a tsaye tana girgiza kanta cikin wani irin yanayi wanda na kasa banbance na tsoro ne ko na firgita da tayi daga jin abin da Sabeer ya fad'a mata. Mik'e wa tsaye shima yayi tare da cewa " ina son ki! Ina son ki Suhaima zaki aure ni? " Toshe kunnen ta Suhaima tayi da dukka hannun ta biyu don batason jin abin da Sabeer yake ce mata tana cewa "Bana son ka Sabeer bazan iya auren ka zaka iya neman wata " Tana gama fad'i haka ta juya zata fita daga parlourn da tasan wannan shirmen maganar zai fad'a mata da bata biyo shi ba balle ta tsaya sauraren shi don ko a mafarki bazata ta6a aminta da abin da Sabeer ya fad'a mata balle ido biyu. Fisgo hannun ta yayi da k'arfi wanda ya sanya ta fad'a wa cikin jikin shi ta buge kanta da faffad'an k'irjin shi, d'ago kanta yayi da dukka hannun shi biyun ya matse kan nata da k'arfi wanda ya sanya d'an kwalinta ya fad'i lallausan dogon gashin kanta ya bayyana a sarari, kallon shi Suhaima take wanda taga idanun shi sun yi ja sosai idan ba gizo idanun ta suke tamkar ruwan hawaye take hangowa cikin eye's nashi, ko kwakkwaran motsi ta kasa saboda rik'e mata kan da yayi cikin kakkausar murya yace "K'arya kike Suhaima dole ki soni tun da har na soki, ina son ki fad'a min kina sona? " Duk da tsoro da fad'uwar gaban da Suhaima take ga kuma zafin matse mata kan da yayi sai da ta bud'e baki tace "Sabeer na fad'a maka bana son ka ba'a so dole ka rabu da ni please you're hurting me" Idanun shi na zubar hawaye yace "Are you sure baki sona? " "Yes I'm very sure " Cikin tabbatar wa Suhaima ta fad'a ba tare da shakka ba, a hankali taji ya cika ta ya koma ya zauna jagwab saman kujera kafin ya had'e kan shi da gwiwa hawaye ne masu zafin gaske suna zuba a idon shi yau wai Shi Sabeer Hussein d'an fillo mace yarinya k'arama take cewa bata son shi why? " Suhaima kuwa ranta a 6ace ta d'auki d'an kwalinta ta daura tana me shafa wuyanta da d'an k'age, ko kallon inda Sabeer yake bata yi ba ta fita daga gidan ta barshi. Ta d'auki wajen 10 minutes a tsaye ta rasa inda zata nufa sai ta ga motar Sabeer wanda yayi amfani da ita yanzu kauda kanta tayi gefe guda ganin an tsaya. "Yalla6ai yace ki shigo na mayar da ke gida " Wata murya ta daban ta furta mata hakan, kallon wajen tayi ta ga wani bak'on fuska ne ba Sabeer ba ne, ajiyar zuciya ta sauke
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104