Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 73

Chapter 73

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,182 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tabbatar babu lafiya don haka tashi yayi ya fito daga office hannun shi d'aya rik'e da coat nashi d'ayan hannun kuma jakar laptop da phone nashi, cikin sauri da sassarfa yake tafiya har ya k'araso compound na company d'in. Driver na hango shi yayi saurin shiga mota tare da yi mata ya kawo ta gabanshi bai jira ya bud'e mish ba kawai ya sanya hannu ya bud'e murfin motar ya shiga tare da cewa "Driver kayi sauri ka kaini gida " "Toh Yalla6ai " Tafiya suke cikin motar shiru gaban Sabeer ban da fad'uwa babu abin da yake yi lumshe eyes nashi yayi tare da jingina kanshi jikin kujera yana janyo addu'a cikin zuciyar shi. Tafiyar 20 minutes suka k'araso gida da yake driver yayi gudu ko gama parking bai yi ba Sabeer ya fito daga motar ya doshi cikin gidan. 'Yar aikin da ke la6e ajikin window na parlour wanda za'a iya hango farfajiyar gidan tana raba ido irin na munafukai tana hango Sabeer ne ya sanya ta saurin k'ak'alo kukan dole tare da nufar k'ofar parlour ta bud'e tana kuka sosai har da k'ara. Sauran kad'an ta bugi Sabeer tayi saurin ja baya ta tsaya cikin tashin hankali yace "Keee lafiya kuwa? " "Yalla6ai ka taimaka mana Aunty ce ina fitowa daga d'akina na ganta a parlour a kwance cikin jini kuma ta sume....... " Kan ta k'arasa fad'a tuni Sabeer yayi wurgi da ita gefe da gudu ya shiga cikin parlour yana rarraba ido ina zai hangi Babyn shi. Can idanun shi sukayi mummunan gani na ganin Suhaima a k'asa kwance saman carpet babu alamar numfashi a tattare da ita, da gudu ya k'arasa wajen tare da d'ago ta jikin shi yana cewa "Suhaima! Kada ki tafi ki barni ki tashi please" Wani irin kuka yake yana jijjigata amman ina batasan yana yi ba ma still har yanzu jini na zuba a jikinta. "Yalla6ai ko zamu kai ta asibiti " Cewar Larai mai aiki sai a time d'in Sabeer ya tuna da asibiti don tsananin rud'ewa ya hanashi yin wannan tunanin. Cikin sauri ya d'auke ta tare da fita daga palon duk jikin shi ya 6aci da jini da karfin shi yake kwallawa driver kira, nan ya taso a tsorace ganin matar Yalla6ai ahaka ya sanya shi saurin bud'e mishi mota ya shiga. Da gudu driver yake jan motar hanyar asibitin Mumy kawai driver yayi don yasan nan ne wurin zuwan su gaba d'aya 'yan gidan. Suna shiga compound d'in hospital d'in suka yi kici6is da Mumy ta fito daga ciki zata tafi don time d'in tashin ta yayi, ganin motar Sabeer tayi parking ne ya sanya ta sakin wani shu'umin murmishi don tasan komai ya faru a yanzu. Da sauri ta k'arasa wajen motar tun kafin ta k'arasa Sabeer ya fito daga motar cikin tashin hankali kamar gaske tace "Son me yasamu Suhaiman ne? " Idanun shi na zubar da hawaye yace "Mumy ki taimaka min kada Suhaima ta mutu please " Da sauri Mumy ta kirawo nurses suka taho da gadon daukan mara lafiya, kwantar da Suhaima Sabeer yayi nan suka nufi cikin asibitin da sauri, yayin da Mumy ta rik'e hannun Sabeer suka shiga ciki, saboda gujewa zargi ya sanya Mumy k'in shiga room d'in da Suhaima take don ta dubata. Sai kawai ta kirawo Dr Nabilah don ta tsaya akanta tunda Dr Aishat ta tashi, yayin da Mumy ta rungume Sabeer ajikinta tana shafa bayan shi idan ban da ajiyar zuciya babu abin da yake saki. Dakyar suka tsayar da bleeding d'in da Suhaima take duk yanda suka so cikin ya zauna amman hakan ya gagara sai da ya fita, gyara mata jikinta suka yi bayan sun samu nasarar dawowar numfashinta sannan suka sanya mata drip tare da yi mata allurar bacci don ta huta sosai. Fitowa suka yi daga room d'in Dr Nabilah ta nufi office d'in Dr Faridah sauran nurses d'in kuma suka nufi nasu office d'in, tura k'ofar tayi a hankali ta shiga Sabeer na ganin ta ya tashi da sauri ya matsa kusa da ita yace "Dr fad'a min awane yanayi Suhaima take, kada kice min ta mutu please" Kallon shi Dr Nabilah take cike da tausayi dakyar ta iya cewa "Yalla6ai munyi nasarar dawowar numfashinta yanzu haka nayi mata allurar bacci sai dai muna buk'atar jini don tayi bleeding sosai " Ajiyar zuciya ya saki tare da hamdala kafin ya kuma cewa "Cikin jikinta fah yana nan? " Kasa magana tayi tuni Sabeer ya shiga cikin wani yanayi na daban mara misaltuwa. "Am sorry Yalla6ai cikin ya fita duk iya kok'arin da muka yi bai zauna ba" Sauran kad'an Sabeer ya fad'i da jin abin da tace mishi jikin shi har rawa yake ya zauna kan kujera cikin rawar murya idanun shi tap da hawaye yace "Innalillahi wa'inna ilaihhir raji'un, Mumy.... Mumy shikenan d'ana ya tafi bazai dawo ba " Dr Faridah wadda ta sauke ajiyar zuciya na kwanciyar hankali jin cikin ya fita sai dai kuma ta tausayawa yaron nata, da hannu tayi wa Dr Nabilah alama da ta fita. Rungume Sabeer tayi wanda yake kuka sosai kafin daga karshe kuma ya daina kukan kiran Daddy yayi yana fad'a mishi kamar Daddy yayi wa Sabeer kuka haka yaji saboda yasan yanda Sabeer yake bala'in son ciki kodayaushe zancen shi Suhaima zata haihu ya samu Baby shima. Sabeer fita yayi zuwa room na Suhaima wanda aka kwantar da ita, kallonta yake duk ta rame tayi wani irin haske daga ni bata da ishashshen jini ajikinta, hannun ta mara drip ya rik'e gam yana kallon ta hawaye na fita a eyes nashi. Daddy ne ya shiga office d'in Mumy cikin fusata, kallon ta ya tsaya yi kawai har sai da Mumy ta tsorata sosai, kallon ta kawai yake amman sam bai yadda da zubewar cikin Suhaima ba sai da dalili don yasan halin Dr Faridah ciki da bai. Hannun ta ya damk'o da k'arfi har sai da ta saki k'ara tana cewa "Daddy da zafi fah " Idanun shi cikin nata yace "Faridah ki fad'a min gaskiya da sanya hannun ki cikin zubewar cikin matar Sabeer? " Afrigice Mumy ta d'ago da kanta tace "Ni..... Ni kuma Daddy ina ruwana da ita ne saboda me zan zubar mata da ciki gidanta nake zuwa kuma saboda irin haka na sanya Dr Nabilah ta tsaya akanta kada naje ace ni na zubar mata gashi nan ma duk da haka ban tsira ba " "Uhmm Faridah na sanki ciki da bai fah zan bincika dalilin faruwar hakan idan zargina ya tabbata gaskiya zakiyi nadama don daga ni har Sabeer zamu guje ki! " Yana gama fad'in haka ya tureta sauran kad'an ta kife akan table ya fice daga office d'in, Direct office d'in Dr Nabilah ya nufa. Bayan ya shiga ne ya samu waje ya zauna yana kallon ta sannan yace "Inason ki fad'a min gaskiya mene silar zubewar cikin matar Sabeer? " "Yalla6ai a iya bincike na na gano zamewa tayi ta fad'i a k'asa wanda ya zama silar zubewar cikin " "Kin tabbatar da hakan? " "Sosai ma Yalla6ai " Ta fad'a hakan tana k'ak'alo murmishin yak'e, don Dr Faridah ce ta tsara mata abin da zata ce idan ba

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});