Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 84

Chapter 84

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,230 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kawai tare da zabga tagumi abin duniya yayi mishi yawa, bayan su Baba Adamu sun gama ta6a hirar su ne suka yi sallama suka tafi nasu gidan. Tashi Sabeer yayi ya koma zaure saman wani dutse ya zauna wanda ake tokare k'ofa dashi duk kayan jikin shi sunyi squeezing gashi sunyi datti wanka yake son yi sai dai babu fuskar hakan, had'e kai da gwiwa kawai yayi ga wani zafi, kukan sauro da cizon shi da suka addabi Sabeer dashi. Yah Aliyu ne ya shigo gidan ya dawo daga rakiyar su Baba Adamu kenan, rufe k'ofar gidan yayi sannan ya wuce cikin gidan ko kallon inda Sabeer yake bai yi ba. Sabeer na zaune anan yaji motsi d'ago kanshi yayi suka had'a ido da Aliyah saboda akwai hasken farin wata, tabarma ta mik'a da pillow tace "Gashi nan Sabeer kayi hak'uri " Girgiza kanshi yayi kan yace "Auntyn mu nine da baku hak'uri don ku nayiwa laifi, nagode da kulawar ki agare ni ina rok'an ki da ki cigaba da bawa Suhaima hak'uri har ta huce " Girgiza kanta tayi cikin tsananin tausayin shi don kallo d'aya zaka yi mishi kasan yana tattare da damuwa sosai, kar6ar tabarmar yayi da pillown yayin da Aunty Aliyah tace "Insha Allah zanyi kok'arin daidaita ka da Suhaima da Yayanta " Tana gama fad'in haka ta wuce da sauri don fakar idon Aliyu tayi ta fito ta kawowa Sabeer tabarmar, kallon ta yake irin kallon tuhumar nan d'an 6ata fuska itama tayi kan tace "Lafiya kake kallo na haka kamar wadda tayi mata sata? " D'an girgiza kanshi kawai yayi baice komai ba ya kwanta, ajiyar zuciya Aliyah ta saki ganin bai fahimci inda taje ba, kwanciya ita ma tayi gefen shi tana tunanin yands zata 6ullo wajen ganin Aliyu ya sassautawa Sabeer............ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/18, 8:32 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 104-105* Cikin wannan daren Suhaima bacci kasa d'aukan ta yayi ta rasa abin da yake damunta tun da Sabeer yazo ta rasa nutsuwar ta wanda har takai da yiwa kanta tambayoyi tana son Sabeer ne har yanzu, tausayin shi take ji ko kuma har yanzu zuciyar ta na son sake zama da shi a matsayin mijinta. Ta 6angaren Sabeer kuwa kusan kwanan zaune yayi saboda zafi da cizon sauro ga duhu dulum ko'ina sai buge bugen sauro yake ya rasa inda zai sanya kanshi yaji dad'i, yayi dana sanin abin da yayiwa Suhaima sau ba iyaka yayi nadama sosai akan tsayawa binciken da bai yi ba gashi ya janyo kanshi shiga cikin tashin hankali. Wajen k'arfe 3:25 ne gari hadari ya had'o sosai sai walk'iya da cida wato tsawa ake yi ga wata irin iska mai k'arfi da take kad'awa sosai, nan Sabeer ya shiga mugun tashin hankali sosai don yasan idan ruwa ya tsinke babu shakka sai yayi mishi jagab musamman idan mai feshi ne, kawai sai ya fashe da wani irin kukan tausayin kanshi, yana cikin kukan ne ruwa ya zuge kamar da bakin kwarya kafin Sabeer ya ankare ruwa ya jik'e shi jagab tunda kanshi har k'afafun shi. Tak'urewa yayi waje d'aya ya had'a kai da gwiwa yana faman shashshak'ar kuka da rawar sanyi, ga ruwan sai zubo mishi yake jikin shi amman ya kasa tashi daga wajen toh idan ma ya tashi ina zai je bashi da wajen zuwa a yanzu wanda ya shige inda yake zaune. Tun da aka fara walk'iya Suhaima ta farka tana zaune tsakiyar gado ta zabga tagumi duk ta rasa abin da yake mata dad'i, don tasan irin yanayin zauren gidan nasu ruwa zai jik'a mutum Yah Aliyu yana da niyyar gyaran shi cikin satin nan, amman tasan halin Yayanta sai yak'i gyara shi saboda Sabeer, kasa jurewa tayi ta sakko daga kan gadon ta nufi bakin window wanda za'a iya hango filin tsakar gidan zuwa cikin zaure. Hannu ta sanya ta yaye labulen window wani irin mugun sanyi tare da feshin ruwa ne ya ratsa ta, bata hango Sabeer sosai ba saboda duhu sai kyallin farin kayanshi da ta hango, sakin labulen tayi tare da dawowa ta zauna kan gado kusan har aka gama ruwan gabannin asubah Suhaima na zaune ta kasa komawa bacci, da yake tana da toilet aciki ya sanya ta yin alwala tayi sallah tana idarwa ta fara addu'a tana cikin yi ne wani bacci mai k'arfi ya d'auke ta. "Suhaima! Suhaima!! Ki tashi haka baccin ya isa " Cewar Aunty Aliyah tana bubbuga k'afar ta, cikin nutsuwa take bud'e idanunta akan agogo ta d'ora eyes nata taga har 10:40 da sauri ta mik'e zaune daman haka lokaci yaja lallai tayi bacci mai nauyi. "Aunty gaskiya nayi bacci mai nauyi haka lokaci yaja " "Naji shirun yayi yawa har mun karya shine nazo duba ki ko lafiya?" D'an murmishi tayi sannan tace "Lafiya qlau Aunty kawai bacci ne " "Kiyi sauri ki shirya kizo ki karya don ina son mu gama aiki da wuri zan fita suna da yamma " "Laaa Aunty zan raka ki don Allah " Cewar Suhaima cikin shagwa6a, 'yar dariya tayi kan tace "Waiii rufa min asiri sai dai ki tambayi mijin ki tukunna " Had'e fuska Suhaima tayi kan ta mik'e da sauri ta shige bathroom da kallo Aunty Aliyah ta bita kan ta girgiza kanta kawai fita tayi daga d'akin. Agurguje Suhaima tayi wanka ta shirya cikin wata blue d'in jallabiya ire iren kayan da Yayan ta ya siya mata ne tunda bata taho da kaya ko d'aya ba, bata yi wani kwalliya ba wet lips ne sai powder kawai ta shafa duk da haka tayi kyau kuwa, d'an perfume ta shafa kan ta had'e gashinta da ribbon ta fito daga d'akin. Hankalin ta akan hanyar zaure amman bata hango shi ba nan taji hankalin ta ya d'an tashi kaddai ya tafi, har tana yin tuntu6e saboda lek'e ashe Aunty Aliyah na kula da ita girgiza kanta tayi kawai tana murmishi don tasan Suhaima nason Sabeer haka shima yana sonta don haka zatayi bakin kok'arin ta wajen daidaita su. "Lek'en me kike har kina yin tuntu6e " Wani kunya ne ya kama Suhaima sai kawai ta sunkuyar da kanta tana shafa kai ta wuce kitchen da d'auko abin karyar ta tana cewa "Ni babu abin da nake kallo fah Aunty " Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/18, 10:27 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 104-105* Cikin wannan daren Suhaima bacci kasa d'aukan ta yayi ta rasa abin da yake damunta tun da Sabeer yazo ta rasa nutsuwar ta wanda har takai da yiwa kanta tambayoyi tana son Sabeer ne har yanzu, tausayin shi take ji ko kuma har yanzu zuciyar ta na son sake zama da shi a matsayin mijinta. Ta 6angaren Sabeer kuwa kusan kwanan zaune yayi saboda zafi da cizon sauro ga duhu dulum ko'ina sai buge bugen sauro yake ya rasa inda zai sanya kanshi yaji dad'i, yayi dana sanin abin da yayiwa Suhaima sau ba iyaka yayi nadama sosai akan tsayawa binciken da bai yi ba gashi ya janyo kanshi shiga

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});