Chapter 96
Chapter 96
yake turata mata wanda ya sanya Suhaima sakin jikinta ta biye mishi ba tare da ta sani ba. Wannan daren sun faranta shi ya zame musu tamkar daren su na farko, Sabeer ya nuna mata tsantsar son da yake mata yana kuka yana rokanta kada ta rabu dashi, bayan komai ya kammalu ne ta fara zum6ura baki tana k'unk'uni, abin ma dariya ya bashi sosai nan ya 6ige da aikin rarrashi kan su wuce suyi wanka suna kwanciya bacci mai dad'i yayi awon gaba dasu, zuciyar kowa fes da farinciki ga kuma yanayin garin da yayi dad'i suna rungume da junan su suka yi bacci............ Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [5/4, 2:18 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 112* Washe gari tun safe da wuri Aunty Aliyah ta kammala abin karin safe ta aikawa da Baban su Aliyu, har Aliyu ya fita schl bata ji motsin Suhaima ba, ganin ta gama komai ne ya sanya ta zura hijab ta d'auki Ameer suka tafi gidan su don gaida Baba Umaru. Suhaima wadda tsabar gajiyar da tayi ya hanata tashi da wuri tun sallahr asuba da tayi ta koma bacci ko shima Sabeer yana dawowa daga masallaci ya rungume kayar shi suka cigaba da baccin su hankali kwance. Suna tsaka da baccin su mai dad'i ne Jiddah ta k'araso gidan cikin d'oki da zumud'i take rafka sallama, kamar a mafarki Suhaima taji muryar Jiddah na sallama don haka da sauri ta sauko daga gadon ta fito zuwa waje, had'a ido suka yi da juna wani ihun murna suka saki tare da nufar juna da gudu suka rungume junan su cikin farinciki kamar wad'anda suka shekara basu ga junan su ba. Ihun sune ya farkar da Sabeer daga baccin da yake gane muryar Jiddah ne ya sanya shi jan d'an k'aramin tsaki yasan yanzu zata zo ta dame su bayan yau yana son kasance wa da Babyn shi kusa dashi, don ba k'aramin kewarta yake ba wannan Jiddah duk zata 6ata mishi planning d'in shi tashi yayi ya shiga toilet don yin wanka. Sakin junan su sukayi tare da k'urawa junan su ido na tsayin mintuna can Suhaima tace "Jiddah kin k'ara k'iba da kyau ko dai an samu k'anin Islam ne? " Dariya Jiddah ta saki tare da cewa "Tabbb lallai yarinya don bakisan wahalar haihuwar bane ai sai na huta sosai kafin na sake, ke dai muna jiran naki nan da 'yan watanni " Murmishi Suhaima tayi tare da juya eye's ball d'in ta tace "Ni dai yanzu amarci muke ci sai mun gama tukunna " Kama ha6a Jiddah tayi tare da cewa "Iyyyyeee! Lallai yarinyar nan naga alama Yah Sabeer ya koya miki rashin kunyar shi " Murmishi kawai Suhaima ta sake yi kan tace "Ina zamu zauna d'aki ko waje? " "Kaiii bari nasha iska a waje tukunna ina Aunty Aliyah da Yah Aliyu, hala ma yanzu kika tashi daga bacci? " Kallon kanta Suhaima tayi sai yqnzu ta tuna da sleeping dress d'in da yake jikinta don ma cotton ce kuma doguwa, "Sallamar ki ce ta tashe ni fah, Aunty Aliyah ina tunanin ta fita Yah Aliyu kuma schl ya tafi" "Yah Aliyu ya koma makaranta ne? " "Eh an d'an jima ma da komawar shi, wai ni ina Islam ne? " Dariya Jiddah tayi kafin tace "Zamu shigo kenan muka had'u da Babaa Lantana ta dawo daga wata barka shine ta kar6e ta " "Okay na d'auka baki zo da ita ba nace nayi fushi dake " "Haba ni na isa Besty na, na taho miki da ita " Murmishi Suhaima tayi tana cewa "Kin kyautawa kanki ba don haka ba da sai dai ki koma gida " Suna tsaka da hirar su Sabeer ya fito daga d'aki yayi wankan shi ya sanya wata T-shirt yellow da jeans black, suna had'a ido da Jiddah ya watsa mata harara abin sai ya bata dariya aikuwa ta kwashe da dariya tare da cewa "Ohh ni Yah Sabeer me nayi haka daga zuwa na sai harara " Kallon Suhaima yayi tare da cewa "Baby nah tashi kije ki wanka ki rabu da wannan mai zuwan sassafe gidan mutane " Murmishi Suhaima tayi ta tashi tare da wuce wa d'aki, sai da ta fara gyara d'akin tsaf sannan ta wuce toilet ta wanke shi sannan ta fara wanka. "Allah Yaya kana tak'ura min yanzu fah 11:50 kace nayi zuwan sassafe " Rage murya yayi kafin yace "Saboda zaki hanani hutawa da mata ta ne na tsayin yini guda " "Tabbb Yaya yanda nayi missing d'in Suhaima dasu Aunty Aliyah ai kwana zanyi anan sai dai ka koma kwanan zaure har na tafi " Ta k'arasa maganar da tsokana tana dariya, harara ya dalla mata kafin ya murd'e 'yan yatsun ta kad'an yana cewa "Kin fah rainani yarinyar nan amman zan sanya Khaleel yi miki kishiya ko zaki yi hankali " "lallai ma Yayan nan an fad'a maka ina tsoron kishiya ne tazo mana ba'a kaina zata zauna ba " Hirar su nan suka cigaba dayi har yana fad'a mata dawowar Baban su Suhaima tayi murna sosai da farinciki, da haka Suhaima ta fito har tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga ta atampha tayi kyau sosai sai tashin k'amshi take, tun da ta fito Sabeer ya kafeta da eyes, cikin dariya Jiddah tace "Yah Sabeer irin wannan kallo ai sai kasa ta fad'i " Murmishi kawai yayi indai Jiddah ce bakin ta baya shiru idan taga abu, zama tayi nan kusa dasu bayan ta d'auko musu abin karyawar su anan take taya Suhaima murnar dawowar mahaifin su, murmishi kawai Suhaima tayi tare da cewa nagode, nan suka karya bayan sun gama ne Sabeer ya fita bai dad'e da fita ba Aunty Aliyah ta dawo da Islam a hannun ta d'ayan hannun kuma Ameer ne ta rik'e mishi hannu da yake ya fara tafiya, kar6ar Islam Suhaima tayi tana fad'in Masha Allah ganin yanda tayi 6ul6ul da ita gwanin sha'awa, cikin jin dad'i Aliyah suke gaisawa da Jiddah, suna gama gaisawa ne Aunty Aliyah da Jiddah suka fara kok'arin girkin rana yayin da Suhaima ta baiwa hankalin ta kan su Islam da Ameer tana musu wasa suna dariya. Sunsha hira sosai tsayin yini guda don tun da suka ci abincin rana akayi sallahr azahar suka k'ule a d'aki suna fama zuba hira, sai wajen biyar driven Jiddah ya k'araso suka yi sallama dasu Suhaima ta tafi gida ko had'uwa da Yah Aliyu bata yi ba. AFTER 3 MONTH'S Acikin wad'annan watannin abubuwa da d'an dama sun faru daga cikin abubuwan da suka faru akwai warkewar mahaifin su daga lalurar da ta same shi da kuma samun cikin da Suhaima tayi, sosai Sabeer yayi matuk'ar farinciki da wannan cikin tsabar murna har kuka sai da tayi don yana masifar son yara, sai dai kuma wannan cikin akwai shi da laulayi fiye da na baya sosai Suhaima take shan wahalar shi duk ta rame tayi fari koda yaushe cikin amai abinci kuwa sai ta kusan yini batasa komai a bakin ta ba, duk abin da tayi sha'awar ci Yah Aliyu da Sabeer suna kok'arin nema mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104