Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,192 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 *A SANADIN SON KI* 💝 *Written by* Aishat A Muh'd ✍🏻 ♻£xclusive Writers Forum *Dedicated to my Sadeey (saNaz)* *PAGE 1-2* Wata mata ce durk'ushe a filin tsakar gidan tana faman risgar kuka, har da shashshak'a kamar zata sume saboda tsabar kukan da take yi, sakamakon fad'an da mijin ta yake mata, gefe d'aya kuma yaran ta ne su biyu namiji da mace suna rungume da junan su, suna taya kan su da mahaifiyar su kukan tausayin kansu. Tsinkar muryar mahaifin nasu naji cikin tsantsar 6acin rai da rashin mutunci yake cewa " tun da abin haka ne zan tafi na bar muku garin gaba d'aya, na sha fad'a miki ni bana son haihuwa kwata kwata, ban shirya yin ta yanzu ba saboda bana son ta, ga kuma shegen bak'in talaucin da muke ciki, amman ke kamar kaza kina haihuwa babu dad'e wa ki dad'a samun wani cikin ni na gaji " Ya k'arasa fad'i yana wani sauke numfashi, sakamakon hayagagar fad'an da ya gama yi cikin d'aga murya da tsawa, hararar matar tashi yake da 'ya'yan nashi, zuciyar shi cike da mugun tsanar su, ji yake kamar ya shak'e su, su mutu ko ya huta da ganin su. Cikin shashshak'ar kuka matar tace "Kayi hak'uri maigida, ni kaina ba ni na bawa kaina haihuwar ba, Allah ne ya bani su taya zan butulce mishi wajen zubar da cikin da ba shege ba ne, ka tuna haihuwa rahma ce wasu da kud'in su nema suke basu samu ba, amman kai da Allah ya bawa kyauta kana neman butulce mishi" Ko gama rufe bakin ta bata yi ba ya d'auke ta da wani azababban mari har guda biyu bisa kyakkyawar fuskar ta, sake durk'ushe wa tayi tana rik'e da fuskar ta inda ya mare ta, hawaye ne kawai yake zuba a idanun ta. Nuna ta yayi da d'an yatsan shi, cikin masifa yace "bana buk'atar jin shawarar ki ko wa'azin ki, idan baki bi maganar da na fad'a miki na ki zubar da wannan cikin ba, to wallahi zan bar garin don ban shirya rainon 'ya'ya ba, naji ma da uban talaucin da ya dame ni" Yana gama fad'in haka ya juyo kan yaran, tsawa ya kwantsama musu ba shiri suka shige d'akin uwar ta su da gudu, jikin su na 6ari na tsoron mahaifin nasu. Tsaki yaja tare da cewa "shegun 'ya'ya da munafurcin tsiya da sun ga uwar su na kuka, su ma zasu fara kukan 'yan iska kawai " Yana k'arasa fad'in haka ya sake makawa matar tashi harara tare da jan tsaki ya kad'a rigar shi ya fice fuuuu a fusace kamar ya hantsila saboda sauri. A hankali yaran suka d'aga labulen d'akin suna lek'en ko mahaifin nasu ya tafi, saboda jin shirun da suka ji, ganin ya fita ne yasa su fito wa da sauri suka nufi inda mahaifiyar su take tsugunne tana kukan nata. Rungume ta suka yi suna rarrashin ta da tayi hak'uri ta daina kuka, daman sune masu rarrashin nata idan uban nasu ya gama yi mata rashin mutunci. Dak'yar ta iya mik'e wa tsaye suka shiga cikin d'aki, zama suka yi akan tsohuwar tabarmar su wadda ke shimfid'e a k'asa, kallon yaran nata tayi cikin matuk'ar tsantsar kaunar su tare da mugun tausayin su, ta kamo hannun su ta had'a waje d'aya tare da bud'e bakin ta tace "Aliyu ga amanar Suhaima nan ko da bayan rai na ina son ka kular min da ita, bana son tayi kukan maraicin na, ina son ku tsaya tsayin daka ku nemi ilimi saboda inganta rayuwar ku ko da bana raye, ina son mahaifin ku yayi alfahari da ku a gaba, ku kasance cikin yi wa mahaifin ku biyayya a duk abin da yace muku, ku cigaba da addu'a watarana sai labari komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba." Cikin kuka Aliyu yace " Umma ki daina furta cewa zaki mutu ki bar mu, zamu rayu da ke Umma insha Allah, kuma zan rik'e k'anwa ta da kyau zan kula ta da ita Umma duk wani kyautata wa da bata farin ciki zan bawa Suhaima a cikin rayuwar ta." Ya k'arasa fad'i hawaye na zuba a idanun shi, cikin zuciyar shi tsanar mahaifin shi taf a ciki, Suhaima da bani wayo ne da ita ba sosai, kallon su kawai take tana kuka. Nan Umma ta janyo Suhaima jikin ta, rarrashin ta take har ta yi shiru sai sauke ajiyar zuciya da take, kafin kuma ta bud'e baki tace "Umma ni yunwa na ke ji." Umma kallon Aliyu take shima kallon Umman yake, cikin zuciyar su suna tunanin me zasu bawa Suhaima a yanzu taci, don basu da komai a gidan daman wani lokacin Aliyu ne yake fita yin 'yar sana'a ta k'arfi ya nemo musu abin da zasu ci, idan kuwa ta uban nasu ne kuwa gwara su mutu da yunwa akan ya basu abin da zasu ci. Gaba d'aya ba wanda yayi k'arfin halin bawa Suhaima amsa, jin haka ya sanya ta fashe da kuka don ko karya wa basu yi ba gashi yanzu azahar tana kok'arin yi, cikin rarrashi Aliyu ya janyo hannun ta yana goge mata hawayen fuskar ta yace "yi hak'uri 'yar k'anwa ta yanzu zan fita na samo miki abin da zaki ci, amman kada kiyi wa Umma kuka kin ji " Gid'a kanta tayi tana mai had'iye kukan nata, da sauri Aliyu ya fita daga d'akin, yayin da Umman ta bishi da kallon tausayi, yaron da bai fi ace yana k'ark'arshin kulawar iyayen shi ba amman shine yake kula da kanshi, mahaifiyar da k'anwar shi, saboda rashin dace da samun managarcin uba a gare su. Tun Suhaima na jiran Aliyu har bacci yayi awon gaba da ita a jikin Umma tana mai tsotsan 'yan yatsun ta a bakin ta, sai da bacci yayi k'arfi sannan Umma tayi mata shimfid'a ta kwantar da ita. Tashi tayi ta fito zuwa tsakar gidan tsintsinya ta d'auka ta laushi ta fara share filin tsakar gidan, tana yin sharar idanun ta na zubar hawayen tausayin kansu, wani 6angare na cikin zuciyar ta addu'a take yi tare da godewa Allah a halin da ta tsinci kanta a ciki, k'addarar tace ta auren wannan mugun mijin nata mara tausayi, mai butulce wa Allah da baiwar 'ya'ya biyu da ya bashi ga cikin na uku a jikin ta. Tun da Aliyu ya fita bai dawo gidan ba sai daf da mangarib, hannun shi rik'e da 'yar k'aramar leda bak'a, Suhaima na ganin shi ta mik'e da gudu ta k'arasa inda yake tare da kar6ar ledar hannun shi tana duba wa. Garin kwaki ne a ciki sai k'ullin sugar, kallon shi tayi fuskar ta d'auke da murmishi tace "Yaya mun gode Allah yasa ka samu sana'a kana samun kud'i kamar yanda Yayan k'awata yake aiki yana samun kud'i yana siyo musu abin dad'i " Cikin murmishi ya shafa kanta tare da cewa "Amin 'yar k'anwa ta ki cigaba da yiwa Yayan ki addu'a da Umman ki ." "Toh Yaya ina yi kullum idan nayi sallah, amman bazan yiwa baba ba tun da shi mugu ne yana dukan Umman mu, kuma yana zagin mu da dukan mu kullum, nima

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});