Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 48

Chapter 48

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,186 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gani sai da ta mutsutstsuke idonta sannan tace "Sabeer! " Da mamaki da kuma rud'ewa da ganin shi ta sake ambatar sunan shi kafin wasu hawaye su fara zubowa daga idanun ta kallon shi take tamkar yau ta fara ganin shi. Shima wasu hawayen tausayin Mumyn tashi ne suka zubo mishi cikin sassarfa ya k'arasa ya tsugunna agabanta ya dire gwiwar shi a k'asa sannan ya d'ora kanshi saman cinyar ta, hannun ta take saman lallausan gashin kanshi tana shafawa ta kasa magana ma gaba d'aya. Muryar shi na rawa hawaye na zuba yace "Mumy baki yi murnar ganina ba koh, saboda ba'a son ranki na tafi ba, kina fushi da ni ne?" Girgiza kai take yi lokacin da yake magana, cikin sanyin murya tace "Bazan iya fushi da kai ba Son" "To gashi kin sanya damuwa a ranki kin rame ba" D'an murmishi tayi kafin tace "tunanin halin da d'ana yake ciki ne ya sanya ni ramewa da shiga tashin hankali,amman yanzu tun da nagan shi a gabana zan kwantar da hankali na " "Mumy kenan, nayi kewar ku ke da Daddy wai yana ina ne? " "I missed U too Son, Daddyn ka yana office bai dawo ba, yaushe ka dawo, zo kaci abinci " Duk ta rud'e da ganin tilon d'an nata sai faman tambaya take watsa mishi akan lafiyar shi don ta d'an razana da ramar shi da ta gani da duhun da D'an yi, hannun ta ya kamo yana kallon ta kafin yace "Mumy ki nutsu ni ina cikin lafiya sosai " "Okay zo kaci abinci, me zan zuba maka? " D'an shiru yayi kafin yace "ki ban duk abin da kika ci" Cikin farinciki tace "okay Son taso ka zauna " Haka ta kamo hannun shi ta zaunar dashi kusa da ita, kafin ta mik'e tsaye ta fara zuba mishi abincin, da kanta take bashi tana faman kallon shi tamkar wata sabon halitta a gabanta, ita kanta tasan tayi kewar d'an nata da yawa duk saboda matsiyar yarinyar nan d'anta yayi mata nisa. "Mumy tunanin me kike ne ba gashi na dawo ba" Da murmushi kan face nata tace "Son kawai ina tunanin irin wacce wahalar kayi a k'auyen da ko wutar nepa babu " "Haba Mum aikuwa suna da wuta sai dai ba'a fiye samu sosai ba" D'an ta6e bakin ta tayi sannan tace "kuma kana iyacin abincin su naga duk ka rame kayi bak'i " "Mum kibar wad'annan tambayoyin please " "Shikenan Son na bari " Tana gama bashi abincin suka koma parlor tana rik'e da hannun shi gane take tamkar zai sake guduwa ya barta, basu dad'e da zama ba Daddy ya dawo agajiye sosai yake, amman had'a ido da Sabeer yasa shi neman gajiyar tashi ya rasa nan suka yi hugging d'in junan su cikin tsananin k'aunar junan su. Nan babu dad'e wa Family d'in D'an fillo dashi kanshi Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suka samu labarin dawowar Sabeer, nan suka dunga shigowa ganin Sabeer kusan dukkanin su sunyi farincikin ganin shi, musammam Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah don rungume shi sukayi tamkar zasu mayar dashi cikin jikin su saboda tsabar son da suke mishi. Jiddah wadda agidan ta wuni ta d'ago kanta suka had'a ido da Sabeer wanda yake ta zuba musu shagwa6a su kuma sun shashance da lalla6a shi, dariya take son fashewa da ita amman ganin hararar ta da yake yi ne ya sanya ta kunshe dariyar ta, daga k'arshe sai ta faki idon shi tana mishi video don ta nunawa Suhaima ta shirya zama da shagwa6a66en miji..... Aishat A Muh'd ✍🏻 [3/14, 5:17 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz *PAGE 69-70* Tun bayan tafiyar Sabeer gida Suhaima ta shiga tsananin kewar shi ranar cikin kewar shi take duk ta sanyawa kanta damuwa ko abincin kirki ta kasa ci sai tunanin Sabeer, sam ta mance bata kunna wayar da ya bata ba duk a tunanin ta a kunne take. Sabeer kuwa duk ya shiga tashin hankali da ya kirawo ta yaji wayar a kashe yana son sanar da ita ya sauka lafiya sannan ya fad'a mata yanda yayi kewarta na tsawon yini guda, daga k'arshe dai sai kiran Yayah Aliyu yayi bayan sun gaisa yake fad'a mishi ya sanarwa da Suhaima ta kunna phone nata zai kirata tukunna suka yi sallama. Tana kwance still har yanzu har bacci ya fara fisgarta sai taji sallamar Yah Aliyu ya shigo d'akin, kallon ta yayi cikin kulawa kafin yace "K'anwata me yake damun ki duk kinyi wani iri yau kodai duk tafiyar Sabeer d'in ne ya sanya ki zama haka" Ya k'arasa maganar cikin zolaya, da sauri Suhaima ta rufe fuskar ta da hannayen tana 'yar dariyar jin kunya tace "Kaiiii Yaya! " "Eh mana gaskiya ce ina kula da ke fah ko abincin kirki baki ci ba sannan baki zo munyi hira ba " Kasa magana tayi don batasan da me zata kare kanta ba don kuwa maganar shi haka take, ganin haka yasa shi mik'e wa tsaye yana murmishi yace "Sabeer yace ki kunna wayar ki zai kirawo ki sai da safe " Yana gama fad'in haka ya fita, d'an waro ido tayi kad'an tare da cewa "Daman wayar a kashe take oops! " Bata tsaya 6ata lokaci ba ta janyo wayar ta kunna ta sannan ta zuba mata ido tana sauraren kiran Sabeer. Ko mintuna goma cikakku batayi da kunna phone d'in ba taji ta d'auki ringing, d'auka tayi ba tare da duba screen d'in ba saboda sauri da zak'uwan son jin voice d'in Sabeer. "Hello Baby nah ". Lumshe idonta tayi saboda jin saukar daddad'ar muryar Sabeer cikin kunnen ta har ta shagala ma sai da ta sake jin muryar shi yana mata magana sannan ta sauke ajiyar zuciya ta amsa mishi tare da gaida shi. Bayan ya amsa ne suka d'an ta6a hira ta tsayin wajen mintuna 30 sannan suka yi sallama da junan su don ganin dare ya fara yi, kowannen su cikin kewar d'an uwanshi suke. Bayan dawowar Sabeer da kwanaki uku ne ya buk'aci da iyayen shi su je neman mishi auren Suhaima, nan take Daddy ya aminta da hakan don haka ya had'a kan 'yan uwan shi maza suka had'u zuwa part din mahaifin su suka sanar mishi don ya tsayar musu da ranar tafiya neman auren Suhaima. Sam Alhj Ahmad d'an fillo ba'a son ranshi yayi magana ba don kana kallon fuskar shi zaka karanci hakan, don farincikin Sabeer kawai ya aminta da auren nan amman sam baya so Suhaima, nan ya yanke lokaci zuwa nan da sati biyu su Daddy zasu je, aikuwa Sabeer najin haka ya tubure bazai yadda ba don sati biyu sunyi mishi nesa shi fah da ason ranshi ne aranar a d'aura auren Babyn shi ta tare a gidan shi, ganin yanda ya tada rigima ne ya sanya shi tambayar shi yaushe yake son aje. Bud'ar bakin Sabeer yace shi gobe yake son aje kuma a tsayar da lokacin biki nan da sati uku, don fah shi har ga Allah satin ukun ya fad'a ne kawai amman sunyi mishi nisa, yanda ya buk'ata haka Alhj Ahmad d'an fillo ya

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});