Chapter 37
Chapter 37
ya kawo ka inda bazaka iya rayuwa mai dad'i ba kamar yanda ka saba rayuwar jin dad'i da hutu maganin iyayin mutum kad'an ma ka gani" duk da a d'an tsorace take sai da ta saki murmishi mugunta sauran kad'an dariya ta kubce mata ta mugunta. "Malam Sabeer muna son sanin kai waye? Me ya kawo ka kuma nan gidan? " Sabeer d'an had'iyar yawu yayi kafin ya motso kusa da Yaya Aliyu cikin sanyin muryar shi yace "Kamar yanda ka sani Sunana Sabeer Hussein d'an fillo Yaya ga k'awar Suhaima wato Jiddah " Nan take Yaya Aliyu yayi murmishi da jin Yayan Jiddah ne ko ba komai d'an uwan Jiddah bai cancanci wulak'anci a wajen su ba. "Masha Allah ashe d'an uwan Jiddah ne kai yarinya mai hankali da nutsuwa, toh Malam Sabeer muna son sanin lafiya kazo inda muke?". Sai da yayi shi na d'an minutes kafin ya bud'e baki yace "So da k'aunar Suhaima ne yasa ni zuwa nan domin na sami soyayyar ta, na kasance tun lokacin da na ganta naji inason ta so na tsakani da Allah kuma ba yaudarar ta zanyi ba wallahi auren ta zanyi " "Ikon Allah! " Fad'in Aliyu kenan, Suhaima da Aunty Aliya kuma sun baza kunnuwan su suna sauraren abin da yake fad'a. "Shine idan baza ku damuwa ba ina son ku koma can birni zan baku gida, mota da kuma aikin yi sannan zan...... " Kasa k'arasa maganar shi yayi ta mak'ale a fatar bakin shi ganin irin yanda fuskar Aliyu ta rikid'a ta koma wata iri na yanayin fusata ga wani d'an iskan kallo da yake jifan Sabeer jin yazo mishi da wani banzan magana. Sabeer kuwa kasa magana yayi yana kallon Aliyu yanda yake mishi wani irin kallo alhalin a girmi bazai girme shi sai ma watak'il ya bashi shekara biyu. "Gaskiya tun da ka biyo ta wannan hanyar ba lallai Suhaima taso ka koda ta so ka ni kuma bazan yarda ta aure ka, mu ba makwad'aita bane duk da mu talakawa ne muna rayuwa a karkara muna jin dad'i yanda muke rayuwar mu bama hangen wani abin don haka ka sake tunani Sabeer baza mu ta6a yarda da wannan maganar taka ba " Nan Aliyu ya cigaba da masifa don ya d'auka Sabeer ya raina musu arzik'in su ne, baisan Sabeer ko kad'an ba haka bane cikin zuciyar shi da yasan yayi wannan tunanin amman sai ya watsar daga baya tun da iyayen shi sun amince da auren Suhaima a haka amman sai Daddy ya sanya shi furta hakan wanda yayi dana sanin fad'in haka. Ana cikin haka sai ga Babaa Lantana nan da Baba Adamu sun shigo domin kwana biyu basu lek'o ganin jikin Aliyah ba, suka tarar da wannan hatsaniyar har Aliyu yana cewa Sabeer ya kwashi kayanshi ya koma inda ya fito, sosai hankalin Sabeer ya tashi tuni hawaye sun fara zuba a idanun shi. Aunty Aliya ya bata tausayi sosai Suhaima kuwa ko a jikin ta, nan Babaa Lantana da Baba Adamu suka shiga zancen dakyar Aliyu ya hak'ura sai lokacin kuma yaga hawayen da Sabeer yake fitarwa sai kuma jikin shi yayi sosai, bai kamata ya wulak'anta jinin Jiddah ba yanda taso su ba tare da kyamatar su ba. Suhaima kuwa dad'i ya kamata tasan yanzu Yaya Aliyu zai kore shi addu'a take cikin zuciyar ta Allah yasa kada Yaya Aliyu ya amince da dad'in bakinshi. "Kayi hak'uri idan ka bani dama zan zauna a gidan ka na nemi soyayyar Suhaima " Fad'in Sabeer yana goge hawayen fuskar shi. Nan jikin Aliyu ya Kara sanyi sosai mene laifin Sabeer anan Allah ne ya jarrabe shi da son Suhaima bai kamata yayi mishi haka ba kodan 'yar uwar shi Jiddah wadda ko d'azu da safe sai da sukayi waya da ita gaba d'ayan su don haka cikin sanyin murya yace "Nima kayi hak'uri da abin da nayi maka kuma na amince da hakan Allah ya taimaka" Wani sanyi dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Sabeer wanda har sai da ya rungume Aliyu yana godiya, yayin da Aliyu, Aliyah, Babaa Lantana da Baba Adamu suka yi dariyar farinciki, Suhaima kuwa wani bak'in ciki ne ya turnik'e ta sai kawai taja tsaki ta wuce d'akin ta da sauri duk suka bi ta da kallon mamaki. "To kai gaka d'an birni anya zaka iya cin abincin mu ka kwanta a irin d'akunan mu kuwa " Cewar Babaa Lantana, dariya Sabeer yayi kafin yace. "Me zai hana kuwa Babaa " Nan aka d'an ta6a hira cikin farinciki wanda a lokacin Sabeer ya shiga ransu saboda sauk'in kanshi. Tashi Babaa Lantana da Baba Adamu suka yi da zummar tafiya nan Aliyu ya dage sai sun ci abinci aikuwa k'in yarda suka yi tare da tafiya. Bayan sun tafi Aliyu ya umarci Aliyah da ta kawo musu abinci, babu dad'ewa ta shirya musu sannan ta wuce d'aki don yin sallah. Bud'e kwanon Aliyu yayi tuwan biskin gero ne da miyar taushe tasha gyad'a da manshanu sai tashin k'amshi yake, nan Aliyu yayiwa Sabeer Bismillah ba don Sabeer ko yasan mene ba ya tsunduma hannun shi ya fara ci dakyar ya iya had'iye lomar da yayi saboda rashin sabo da cin irin wannan abincin . Kasa cigaba da ci yayi fahimtar hakan da Aliyu yayi yasa shi girgiza kai yana tausayin Sabeer yasan wahala ce sai yasha don birni da karkara akwai banbanci musamman a irin gidajen da Sabeer ya taso. Ruwan Sabeer ya runtse ido yasa ba don yayi mishi irin yanda yake so ba gashi cikin shi sai k'arar yunwa yake don rabon shi da abinci tun breakfast na safe saboda zumud'i ma bai ci abinci sosai ba. "Zaka iya shan fura? " Cewar Aliyu yana kallon shi d'an sosa k'eya yayi kafin yace "Eh zan sha kasan mu ma family's d'in mu Fulani ne muna sha amman ni ba sosai ba " Gid'a kai Aliyu yayi yana cewa "yanzu don duhu yayi zuwa gobe sai mu fita kaga yanda garin namu yake " Tashi yayi ya shiga d'aki babu jimawa ya fito shi da Aliyah nan ta wuce kitchen tana kok'arin damawa Sabeer fura, babu dad'e wa ta dama shi ta kawo mishi a cikin k'ok'o da ludayi had'e da kofin roba ta ajiye mishi. "Sannu Aunty Aliyah na had'a ki da aiki " Murmushi tayi tare da cewa "laaa ba komai wallahi dafatan zaka iya shan wannan furar " "Zan iya mana " Murmishi tayi ta wuce d'aki, nan Sabeer ya janyo furar ya fara sha da ludayin gard'in gero da kindirmon nono ya ratsa shi sosai furar tayi mishi dad'i. "Da ka zuba a kofi koh" Yana lumshe ido yace "Barni kawai Yaya nasha a haka don na saba " Dariya kawai Aliyu yayi, bayan sun gama ne Aliyu ya shiga wani d'aki na kusa da zaure ya fara gyarawa nan Aunty Aliya ta fito itama ta bishi d'akin tana tayashi aikin, Sabeer najin dariyar su da magana suna yi k'asa k'asa lumshe idanun shi yayi sun birge shi sosai yana fatan su yi irin wannan zaman da Suhaima idan ya shawo kanta ta kar6i soyayyar shi. Tsaf suka gyara d'akin bayan sun share sun bud'e window na d'akin nan suka sanya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104