Chapter 83
Chapter 83
yayi hak'uri amman tana fara magana da ya buga mata wata tsawa batasan lokacin da ta tsallake Ameer ta wuce d'akin Suhaima da gudu ba, wanda har taso sanya Aliyu dariya amman ya matse dariyar. Afirgice Suhaima ta juyo jin an shigo d'akin ta da gudu ganin Aunty Aliyah ce ya sanya ta sauke ajiyar zuciya tana goge hawayen fuskar ta tace "Aunty lafiya kuwa " Zama tayi kan tace "Hummm Suhaima Yayan nan naki ya d'auka da zafi sosai wallahi don zuwa nayi na bashi hak'uri amman wata tsawa da kwantsama min bansan sanda na sanya gudu ba, ina tausayin Sabeer nasan ba laifin shi ba ne laifin shi d'aya da yace ki bar mishi gidan shi " Suhaima bata ce komai ba kawai sai ta zame ta kwanta tare da d'ora kanta saman k'afar Aliyah zuciyar ta a cunkushe take sam ta rasa abin da yake damunta. Sabeer kuwa tun lokacin da Yah Aliyu ya watsa shi waje kasa tashi yayi awajen kawai ya zauna tare da janyo bag d'in shi ya d'ora saman k'afar shi ya fad'a kogin tunanin yanda zai shawo kan wannan matsalar, gaba d'aya wuyan shi ya rik'e ko iya juyashi sosai baya yi sabida shak'ar da yasha a hannun Aliyu, wai shi Sabeer shine aka watso shi waje kamar shi da kud'in shi da gatan shi amman duk A SANADIN SO komai na rayuwar shi ya canja. Yana nan zaune aka yi kiran sallahr mangarib yana kok'arin tashi ya tafi masallaci ko zai samu ruwan alwala yaji an bud'e k'ofar an fito, sai da gaban Sabeer ya fad'i ganin yanda Aliyu ya tamk'e fuska tamkar bai ta6a dariya ba. Kallon Sabeer yake cikin mamaki kafin yace "Wai kai wanne irin mutum ne nace kabar min gidana bama buk'atar ba ana dole ne k'anwata ta tsane ka bata sonka ina son kawai ka rubuta mata saki ka bata tun muna mu biyu da kai kaji na fad'a maka " Yana gama fad'in haka yaja tsaki tare da wuce wa, wani bak'inciki ne ya lullu6e Sabeer ganin wanda a girme bazai girme shi ba yake fad'a mishi magana son ranshi, da zai iya cire son Suhaima ya ajiye shi gefe da yayi don kawai samun sauk'in halin da yake ciki da me zai ji abubuwa gaba d'aya sun hargitse mishi ya rasa samu mafita. Dakyar ya lalla6a yaje masallaci can ya samu ruwa yayi alwala tare da bin jam'in sallahr mangarib bayan an idar ne yana zaune a masallacin yana addu'ar Allah ya sassauta zuciyar Aliyu ya kyale mishi Suhaima kada ya rabasu, har aka kira sallahr ishsha bayan an idar da sallahr ne kowa ya watse sai shi kadai ya rasa wajen zuwa. Yana nan zaune har wurin 9 na dare ga wasu sauro da suke kai mishi cafka ga zafi da duhu dulum a wajen ga wata azababbiyar yunwa da take k'ulle mishi ciki, kamar a mafarki yaji ana kiran shi cikin mamaki da sauri ya tashi ya fito daga cikin masallacin. Baba Adamu ya gani tsaye da torchlight a hannun shi, tsugunnawa Sabeer yayi ya gaida shi amsa wa yayi kan ya kama hannun Sabeer suka doshi gidan Aliyu. Atsakar gidan ya tarar da Aliyu, Suhaima, Aliyah, Babaa Lantana suna zaune ran Aliyu a 6ace yake don sosai Aliyah ta shammace shi taje ta fad'a wa su Baba Adamu halin da ake ciki sai aika mata da harara yake yi saboda yaso ya kar6i takardar sakin Suhaima ya fatattaki Sabeer kafin su ankara, sai gashi Aliyah ta shammace shi. Zama Sabeer yayi gefen Baba Adamu sanann ya fara magana akan rashin kyautawar da Sabeer yayi na tsayawa yayi bincike kafin ya kori Suhaima, sanann ya d'ora da yiwa Aliyu nasiha tunda ya gane gaskiya bai kuma kyauta da abin da yayi ba har yazo domin ya nemi afuwar su ya kamata ya hakura kowanne d'an adam bai cika goma ba. "Baba ni kawai ya bata takardar ta kawai yayi tafiyar shi Suhaima bazata koma gidan shi ba" "Baza'a yi haka ba Aliyu a tambayi Suhaima tana son komawa tunda ya gane laifin shi har ya bada hak'uri kamata yayi ayi mishi afuwa " Kallon ta Baba Adamu yayi kan yace "Suhaima ina son ki fad'a min tsakani da Allah kina son komawa gidan Sabeer? " Da sauri ta d'ago kanta ta kalli Baba Adamu kafin ta mayar da kallonta kan Sabeer gaba d'aya ya wani marairaice fuskar shi ta koma kalar tausayi sosai yana rok'an ta da tayi hak'uri ta amince, d'auke idonta tayi akan shi ta mayar dashi kan Yah Aliyu sai taga yanda ya wani had'e fuska gashi ya tsattsare ta da ido, ta rasa yanda zata yi zata bi bayan Sabeer ko zata bi bayan Yayan ta idan bata mance ba Yayan ta shine uwa ubanta don bata da wanda ya fishi duk duniyar nan, idan matsala ta sameta shi zata tunkara taya zata dubi tsabar idon shi ta za6i miji wanda bashi da tabbas. "Kin shiru ke muke jira Suhaima " Cewar Babaa Lantana kenan. Kasa magana kawai tayi ta fashe da kuka sosai don batasan wanda zata bi bayan shi ba da gudu ta shige d'aki tare da sanya key. Wata ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yayin da Sabeer kanshi yake sunkuye wasu hawaye na zuba daga cikin su duk shi yajawa kanshi yayi wasa da damar shi gashi komai ya rikice mishi, tsugunnawa yayi tare da cewa "Ina rok'an ka Aliyu ka taimaka min kayi hak'uri akan abin da nayi wa Suhaima wallahi nayi nadamar korar ta da nayi bazan sake maimaita hakan ba insha Allah kuma zan sanya ido sosai tare da d'aukan mataki ga duk wanda yake kok'arin cutar min da ita " Tsaki Aliyu ya saki tare da d'auke kanshi yana cewa "Tun da Suhaima tak'i amincewa sai ka tashi ka koma inda ka fito " "Babu inda zanje har ina nan har sai lokacin da Suhaima ta yafe min ta amince zata koma gidana " Ta6e baki Aliyu yayi kan yace "Ba dai agidan nan ba kuwa " "Bashi da inda ya wuce nan Aliyu dole ya zauna tare da ku " Cewar Baba Adamu yayin da Aliyu yace "Baba ni bani da wani d'akin kwana anan gidan " "Ga d'akin matar shi nan " Fad'in Babaa Lantana kenan da duk tausayin Sabeer ya lullu6e ta. "Babaa kiyi hak'uri amman gaskiya ban amince mishi da ya kwana anan d'akin ba " Duk yanda yaso su Baba Adamu su taushi Aliyu yak'i basu had'in kai har sai da ran su Baba Adamu da Babaa Lantana ya 6aci sosai kafin dakyar ya amince da sai dai ya kwana a zauren gidan. "Kana ji Sabeer zaka iya kwana a zauren gidan? " Da sauri Sabeer yace "Eh Baba zan kwana nagode sosai Allah ya k'ara girma " "Amin Sabeer ba komai, yanzu Aliyah tashi ki zuba mishi abinci yaci " Aunty Aliyah da tunda aka zauna bata tsoma baki ba ta tashi ta nufi kitchen tana zuba mishi abinci, bayan ta zuba ta kawo mishi gaban shi ta ajiye tare da kawo mishi ruwa mai sanyi na randa ta ajiye mishi. Saboda yunwar taci ta cinye shi kad'an ya iyacin abincin yasha ruwa, zama yayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104