Chapter 6
Chapter 6
💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻£xclusive Writer's Forum Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 7-8 Babu wanda yayi k'arfin halin yi mishi magana a tsakanin Baba Adamu tare da Babaa Lantana, ganin haka ya sanya shi kutsa kai cikin d'akin, lokaci d'aya kuma gaban shi na bugawa da k'arfi sosai. Aliyu yana sanya k'afar shi cikin d'akin idanun shi suka hango mishi Umman shi kwance an lullu6e da zani, da sauri ya k'arasa wajen gaban shi na tsananta fad'uwa, hannun shi na rawa ya sanya akan zanin ya fara janye shi a hankali, fuskar Fatima ce ta bayyana kamar an kirata ta amsa, sai kace ba matacciya ba, tuni Aliyu ya durkushe tare da sakin wani irin kuka yana cewa "Umma ki tashi don Allah kada ki tafi ki barmu a wannan duniyar mu kad'ai" Kuka sosai Aliyu yake yana sumbatu, ganin haka ya sanya Baba Adamu ya janye shi daga gaban gawar Fatima dakyar don shima hawayen yake yi, Babaa Lantana kuwa da Aliyah Suhaima kuka suke yi sosai. Daga k'arshe Baba Adamu ya fita don sanar wa da jama'ar gari, cikin k'ank'anin lokaci mutuwar Fatima baiwar Allah ta zagaye cikin k'auyen nasu, sosai mutane sun jimanta rasuwar ta tare da yaba kyawawan halayen ta, da irin yanda take hak'uri da jure irin rashin mutunci irin na mijin ta wanda sam kanshi ya sani. Babu jimawa mutane suka taru akayi wa Fatima wanka aka had'a ta cikin likkafani, sannan daga k'arshe aka sadata da gidan ta na gaskiya, gidan da shi muke jira Allah ya jik'an wad'anda suka mutu mu kuma Allah yasa mu cika da imani Amin. Aliyu da Suhaima sun sha kuka kuwa, musamman Aliyu don yafi Suhaima hankali sai yafi jin rad'ad'in mutuwar fiye da ita, su Baba Adamu da Babaa Lantana ne suke tausar su tare da yi musu nasihar yarda da k'addara, lokacin Fatima ne yayi don haka Allah ya d'auki abarshi, kowanne mutum da iyakacin lokacin da Allah ya d'ibar mishi yanzu Fatima addu'a tafi buk'ata fiye da komai, Allah yasa mu dace duniya da lahira Amin. Haka Aliyu da Suhaima suka rungume maraicin su, sun koma abin tausayi, bayan sadakar bakwai ne 'yan uwan Fatima suka nemi tafiya da Suhaima shi kuma Aliyu ya zauna a wajen 'yan uwan uban shi, amman k'ememe Aliyu ya yak'i yarda da tafiya da Suhaima, anyi rarrashin sunyi fad'an amman ina yak'i aminta dole suka damk'a amanar su hannun Babaa Lantana da Baba Adamu, tukunna suka tafi bayan su bawa Aliyu wani d'an taimakon da zai nemi wata sana'ar ta domin kula da kansu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, inda Aliyu da Suhaima suka sake shak'uwa da junan su, komai Aliyu ya samu zaka ji bakin shi na ambatar Suhaima, kulawa sosai yake bata don shi yafi tausayin ta fiye da kanshi, sai dai ita Suhaima ta koma gidan Babaa Lantana da zama sai dai tana shigowa wajen Yayan nata tana tayashi 'yar hira. Aliyu ya dage da yin sana'a kowacce iri ce indai zai samu halal d'in shi, aiki yake yi sosai na k'arfi kuma, haka ya dunga tara kud'i har ya sanya Suhaima a makarantar primary tana nan cikin k'auyen nasu tare da islamiya, babu dad'e wa Suhaima ta fara zuwa makaranta hankali kwance, kullum shi zai kai ta a tsohon keken da Baba Adamu ya cika mishi kud'i ya siya, haka idan aka taso su zai zo ya d'auke ta. Ganin Aliyu ya fi karkata akan son yin noma da kiwo yasa Baba Adamu bashi aron gonar shi guda d'aya don yana yin amfani da ita, shi kuma ya rik'e guda d'aya, da yake gonakin nashi guda biyu ne manya, gashi gonar da ya bawa Aliyu aro a kusa da gidan su Aliyun take, idan ma mutum bai kula ba ya d'auka kamar gidan a tsakiyar gonar yake, sosai Aliyu yayi murna da wannan karamcin da Baba Adamu yayi mishi. **** **** **** Haka lokaci ya cigaba da tafiya watanni da shekaru na wuce wa kamar kiftawar ido, Suhaima an fara zama 'yammata an don har ta kammala makarantar primary sun zana commen interest tana gida ana jiran fitowar result sai makarantar islamiyya da take cigaba da zuwa. Yayin da Aliyu an zama matashin saurayi, ya zama cikakken manomi a yanzu, don ya rik'e sana'ar noma da kiwo, da wannan gonar da Baba Adamu ya bashi aro yake noman shi and cikin ta har zuwa yanzu da ta zama mallakin shi, don tuni Baba Adamu ya siyar mishi da ita, bayan aikin noma kuma yana yin kiwo irin su kaji, awakai da shanu sai kuma yana siyar da kwan kaji sosai yake samu bud'i a harkar shi, ga taimakawar wani amintaccen yaron shi da Baba Adamu ya sama mishi yana taimaka mishi. Ya gyara gidan su sosai yayi kyau, inda a lokacin kuma Baba Adamu ya nemi da yayi aure, babu 6ata lokaci ya sanar musu da Aliyah d'iyar shi yake sosai, babu wanda bai yi farinciki da hakan ba don haka babu 6ata Lokaci akayi aure amarya ta tare a gidan ta, nan kusa da gidan su tun da Aliyu a asalin gidan su ya zauna, a lokacin kuma Suhaima ta dawo hannun Yayan ta da zama, zaman su suke cikin kwanciyar hankali da farinciki, Aliyu ya mayar da hankalin shi sosai kan sana'ar tashi, ya dad'a zama wani babban mutum musamm da yanzu yayi aure. Kamar yau ne ranar laraba ranar da kasuwar garin nasu take ci, tun safe Aliyu ya bar k'auyen nasu ya tafi cikin birni kai wasu kwai masu yawa, wajen mutumin da yake kaiwa ya siya a kan machine d'in shi, don haka gidan ya rage daga Aliyah sai Suhaima a ciki. Ranar Suhaima cikin farinciki take saboda Yayan ta baya nan, zata je cin kasuwa don haka da wuri tayi wanka ta ci gayun ta cikin wata atampa mai kalar milk da brown a jiki, ta sanya hijab d'in ta k'arami kalar brown, sannan ta fito daga d'akin ta zuwa wajen da Aliyah take. Aliyah tana zaune tana gyaran kayan miya don tana son gama girki da wuri kafin Aliyu ya dawo, ta hango Suhaima tana tahowa zuwa wajen ta, fuskar ta d'auke da murmishi tace " Suhaima wannan gayun fa ina zuwa? " Cikin dariya Suhaima tace "Yaya Aliyah nayi kyau ne?" Itama Aliyah tana dariya tace "Sosai ma 'yar k'anwata kinyi kyau, ina zuwa? " "Cin kasuwa zan je " Zaro ido Aliyah tayi tare da cewa "Haba Suhaima kin mance Yayan ki baya son kina zuwa koh, yanzu idan ya dawo bakyanan nasan fad'a zai mana ni da ke " Shagwa6e fuska Suhaima tayi tare da cewa "Haba Yayah Aliyah kafin ya dawo fah na dawo, ba dad'e wa zanyi ba " "Toh shikenan amman don Allah kada ki dad'e " "Yawwa Yayah Aliyah nagode, kuma bazan dad'e ba " Murmishi suka yiwa junan su, sannan Aliyah ta d'auko kud'i ta bata, godiya tayi tukunna ta tafi cikin zuciyar ta fal farinciki. Tana fita waje ta tarar da k'awayen ta suna jiran ta, nan suka tafi kasuwar suna tarar ana tacin kasuwa ga mutane daban daban har da na maraya ma suna zuwa cin kasuwar. Suhaima
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104