Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 97

Chapter 97

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,189 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shi kulawa sosai take samu daga mijinta, Yayanta da Aunty Aliyah ga su Babaa Lantana nan har Baban ta ma kullum sai ya shigo dubata kuma sai ya taho mata da d'an abin kwad'ayi gaba d'aya yayi wani sanyi kamar ba Umaru ba, Jiddah tayi farinciki sosai da albishir d'in da Sabeer yayi mata na Suhaima tana da ciki. "Baby nah yau me zaki ce ne? " Sabeer ya tambaye ta yana sanya kaya fitowar shi daga wanka kenan. Kallon shi tayi idanun ta tap da kwalla tace "Ni bana sha'awar cin komai " K'arasa sanya kayan yayi sannan ya zauna kusa da ita tare da d'ago ta ya d'aura ta kan k'afafun shi, kallon ta yake cikin tausayi yace "Bazan barki baki ci komai ba Baby ki fad'a min please " Shiru tayi na d'an mintuna kafin tace "Zan sha fruits toh sun ishe ni " D'an murmishi yayi kan yace "Yawwa Baby nah haka nake son ji bari naje na samo miki " Kwantar da ita yayi saboda jikin ba k'arfi, ya bud'e mata curtains d'in window da na k'ofa don ta samu iska tana shigowa, sannan ya dawo yayi kissing nata a goshi ya fita, ya dad'e tsaye a k'ofar gida yana tunani don duk kud'in da yazo dasu sun k'are ragowar d'ari biyar ce dashi yanzu ya siyowa Suhaima fruit's da ita sun k'are, gashi gobe ko anjima idan tana son wani abu baisan yanda zai yi ba kuma shi bazai ta6a neman kud'i wajen Aliyu ba wanda shima fama yake da hidimar karatu ga d'aukan ciyar su abin da yawa gaskiya gashi duk master card d'in shi da atm card's nashi duk suna gida bai taho dasu ba da wannan tunanin ya tafi. Wajen 30 minute's da fitar shi ya dawo lokacin Aunty Aliyah ta shiga duba ta kuma tana tambayar ta abin da zata ci, d'auko wani bowl na silver yayi da wuk'a bayan ya wanke fruits d'in zama yayi saman carpet din d'akin zai fara yanka mata Aunty Aliyah tace "Sabeer kawo na yanka mana " Murmishi yayi yana cewa "Mamin Ameer ki barni aiki nane kije ki huta kawai " Itama murmishi tayi kafin ta wuce ta fita, Suhaima na kallon shi har ya gama yanka rabi iya yanda zata iya sha anjima sai ya yanka mata sauran. Kusa da ita ya dawo tare da tashin ta zaune ya jingina bayanta da pillow ya fara bata fruit d'in a hankali take bud'e bakin yake bata, duk da Sabeer yana iyakar d'auke damuwa akan fuskar shi ta rashin kud'i da kewar iyayen shi da 'yan uwan shi ga kuma rashin lafiyar Suhaima duk dashi wannan laulayi ne sai anyi hak'uri na d'an wani lokaci amman lalurar ta tsaya mishi a rai har wani d'an rame wa yayi amman duk da haka sai da Suhaima ta gane akwai wani abin da yake damun shi koda ta tambaye shi baya sanar da ita abin da ke damunshi sai dai ya fad'a mata rashin lafiyar tace take damunshi kyale shi kawai tayi amman tasan da wani abin sai dai ta dage da addu'a Allah ya yaye mishi koma mene. Bayan ya gama bata ta shanye shi gaba d'aya cikin tausayin ta ya kalle ta tare da cewa "Na k'ara miki wani? " Murmishin yak'e tayi kafin ta girgiza kanta kawai. "Okay ni zan fita Baby zamu fita da Ashiru amman bazan dad'e ba" Cikin sanyin murya irin ta mara lafiya tace "Allah ya kiyaye hanya ya dawo min da kai lafiya " Cikin murmishi yace "Amin Sweetie nah " Ya k'arasa maganar yana bata peck a kumatu itama tayi mishi a saman lips d'in shi daga haka ya fita daga d'akin Suhaima tabi shi da kallon tausayi. Haka lokaci ya cigaba da tafiy har aka shiga watan ramadan zuwa wannan lokacin jikin Suhaima ya d'an warware zata ci kowann abinci sai dai har idan ita zata dafa da kanta ba zata iya ci ba, kulawa babu irin wadda bata samu, har azumin ma tun da aka fara take jarumtar yinshi batason tasha, Sabeer kam matsalar kud'i ta yi mishi sauk'i don Daddyn shi ya sanya Jiddah kawo mishi atm card nash duk lokacin da yake buk'ata zai je ya cira amman sai dai idan ya kasance muhimmiya ce saboda yana ganin Aliyu bazai ji dad'i ba zai yi tunanin ya raina duk kulawar da yake bashi. Da haka suka cinye wata ramadan aka shiga hidimar sallah, Yah Aliyu yayi matuk'ar kok'arin yi musu d'inkunan sallah haka aka cinye bikin sallah lafia, sosai cikin Suhaima yake girma zama dakyar tashi dakyar sosai cikin yake da girma. Sabeer ba k'aramin tausayin ta yake ji ba haka da dare zai sanya ta a gaba yana faman kallonta tare da shafa cikin kafin ya tashi ya d'aura alwala yana kai kukan shi gun mai dukka akan ya sauki Suhaima lafiya, har wata rama yayi ta fargaba idan ya tuna yasha jin labarin haihuwa akwai wahala, daman tana zuwa awo amman a asibitin cikin gari duk ranar awo shi yake kaita ya jira ta gama su shiga adaidaita sahu ko taxi su dawo gida. Cikin haka cikin Suhaima ya shiga watan haihuwar shi sai zuba ido ake ana jiran haihuwa shiru, yayin da Jiddah da siyo duk wani abin daya danganci kayan jariri unisex da duk wani abin buk'ata Sabeer ya bata atm card nashi taje ta ciri kud'i ta siyo, duk an gama shirin komai sai jiran haihuwa duk wani masoyin Suhaima yana mata addu'a ta Allah ya rabata lafiya da abin da yake cikinta saboda girman cikin kadai ya isa firgita mutum duk ta wani kumbura tayi wani iri kamar ba ita ba kaya sai dai ta zura dogowar riga saboda riga da siket ko da zani bata jin dad'in amfani dasu dogowar rigar ma irin buba nan mara shape, Baba Adamu kullum cikin yi mata rubutu yake na sauk'in nakuda tana sha. Sai da cikin Suhaima ya shiga wata goma cif cikin wata safiya ta monday ta tashi da azababben ciwon nakuda Allah yaso Yah Aliyu da Sabeer duk suna gida basu fita ba nan da nan aka samo taxi suka tafi asibitin da take zuwa awo, suna zuwa aka kar6eta cikin gaggawa suka wuce da ita labour room Sabeer ji yake kamar ya bita ciki amman Yah Aliyu ya rik'e shi gam ganin yanda jikin shi yake rawa yace "Sabeer addu'a kawa zaka yi mata " Nan ya zube akan benci kawai yana faman yin addu'ar duk wadda tazo cikin bakin shi. Suhaima kuwa abin ba'a cewa komai iyakar wahala tasha ta kamar bazata iya haihuwa da kanta ba ma, tasha kukan har hawayen suka daina fita daga idonta saboda azaba addu'a kowacce yin ta take tana fatan Allah ya rabata da cikin nan lafiya, tun safe ake abu d'aya har zuwa k'arfe 9 na dare sannan wahalar ta tazo k'arshe inda ta haifi kyawawa yaran ta guda biyu duk maza wanda suka kasance lafiyayyu masu koshin lafiya, tana gama haihuwar su da taja wani numfashi sai ta zube nan nurse suka yi kok'arin wajen farfad'owar ta sannan suka gyara mata jikinta tsaf bayan sun gama suka sanya mata drip na k'ara k'arfin jiki da kuma allurar

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});