Chapter 34
Chapter 34
da zai bi ya shawo kan Mumyn shi ta hak'ura ta kar6i Suhaima matsayin surukar ta. Bayan ta gama gasa mishi k'afar ne ta d'auko wani cream ta shafa mishi a k'afar sannan ta sauke ta a hankali daga kan k'afar ta kafin ta yunkura ta mik'e tsaye ta kwashe kayayyakin da tayi amfani dasu zata wuce kenan. "Mumy! " Taji saukar muryar d'an nata mafi soyuwa cikin zuciyar ta, runtse ido tayi wasu hawaye na kok'arin zubo mata amman sai ta had'iye su ta wuce toilet da sauri ta ajiye bowl d'in da towel kafin ta fito tabar d'akin da sauri. "Kada kayi kuka Son zan rarrashi Mumyn ka" "Daddy Mumy tana fushi da ni " Cikin rarrashi Daddy yace "Mumyn ka bazata iya fushi da d'anta ba abin da yake sone baiyi mata shi yasanya ta 6acin rai but nasan zata huce bazata iya jure fushi da yaron ta ba kamar yanda nima na kasa jurewa" Gid'a kai Sabeer yayi kawai, suna cikin haka Alhj Ahmad d'an fillo ya shigo d'akin sannu yake yiwa Sabeer amman bai kalli inda yake ba da yaga yana kok'arin ta6a shi ma sai ya tashi yana d'ingishi ya bud'e kofar baya ya fita ko kallon shi bai yi ba. Da kallo duk suka bishi na mamaki kafin Alhj Ahmad ya zauna yana goge gumi na tashin hankali yace "Hussein anya yarinyar nan ba asiri tayiwa Sabeer ba? " D'an murmishi Daddy yayi kafin yace "Abba ba wani asiri asali ma yarinyar bata son shi " D'an zaro ido Alhj Ahmad yayi kafin yace "Batason shi kamar yaya? Kana nufin Sabeer ne kawai yake son ta? " "Ehh Abba so yake yaje neman soyayyar ta " Cire hular kanshi d'an fillo yayi yana firfita da ita don wani gumi da ya keto mishi na tashin hankali, daman ashe Sabeer son maso wani yake wanda ake ce mishi k'oshin wahala innallahi, tuni jikin Alhj Ahmad yayi mugun sanyi da yaji jarrabar da Allah ya d'orawa jikan shi na son maso wani gashi yarinyar 'yar k'auye shi yanzu mene mafita?. Shiru suka yi gaba d'aya babu mai yin magana a tsakanin su har wurin 10:30 suna zaune jigum jigum suna jiran shigowar Sabeer amman bai shigo ba haka suka tashi suka bar bedroom d'in kowanne zuciyar shi cike da tunani kala kala. Wasa wasa yanzu gaba d'aya Sabeer baya kula Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah, Daddy kawai yake kulawa kawai Mumy kuma bata shiga harkar shi sai dai zata zo ta gasa mishi k'afa sau biyu ta sanya mishi magani, tsakanin ita da Sabeer bansan wanda yafi wani ramewa ba a tsakanin su, ta 6angaren Daddy kuma yana ta kok'arin shawo kan Mumy ta amince don samin farincikin tilon d'an su amma tak'i yarda da maganar tashi ko baccin kirki bata iyayi saboda tunanin tilon d'anta ta rasa samun mafita don mafitar ta d'aya ta bari Sabeer auren Suhaima kuma sam abin da bazai ta6a yiwu ba. Alhj Ahmad d'an fillo kuwa ya rasa samun sukuni don Sabeer bayayi mishi koda shi yayi mishi magana bazai kalli inda yake ba balle ya amsa mishi k'arshe ma sai Sabeer ya bar mishi wurin, duk yanda ya so Sabeer ya saurare shi yak'i bashi had'in kai da wani cikin jikokin shi da tuni yayi watsi da al'amarin amman Sabeer kuwa na daban ne son shi cikin zuciyar shi mara adadi ne, tun kafin a haifi Sabeer yake nuna wa cikin so har aka haife shi a kullum son Sabeer k'ara yawa yake cikin zuciyar shi. Duk yabi ya rame ya fad'a ga mafarkin da yake da Sabeer da wata kyakkyawar yarinya duk mafarkin da zai yi da wannan yarinyar yake ganin su da Sabeer, gashi Sabeer yana kuka yana rok'an ta da ta so shi amman sai tayi tafiyar ta, gaba d'aya d'an fillo ya hankalin shi a matuk'ar tase yake don ganin irin mafarkin da yake. A haka aka d'ibi sati biyu cikin wannan yanayin alokacin Sabeer k'afar shi ta warke sosai duk babu kumburin ya koma tafiyar shi normal babu d'ingishi, har zuwa lokacin Mumy bata yi magana ba Daddy kullum cikin lalla6a ta yake. "Daddy tun da na warke kayi min izinin tafiya wajen Suhaima " Sabeer ya fad'i hakan cikin marairaice fuska, d'an shiru Daddy yayi yana tunani don rasa ta inda zai fahimtar da Sabeer cewa Mumyn shi bata amince da hakan ba da kuma Abbah da Hajjah, yana shirin bud'e baki yayi magana yaji ance "Hussein basai kayi tunani ba ni na bawa Sabeer izinin tafiya wajen masoyiyar shi neman soyayyar ta na amince Sabeer ya tafi domin samun farincikin shi " Da sauri suka jiyo suna kallon D'an fillo a tsaye yana murmishi daga ni na yak'e ne ba'a son ranshi ya fad'i hakan ba, ba har cikin zuciyar shi ya furta hakan ba amman Sabeer da Daddy saboda farinciki sam basu d'ago shi ba, da gudu Sabeer yaje ya rungume D'an fillo yana dariyar farinciki wata ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali D'an fillo ya sauke jin Sabeer rungume dashi yaushe rabon da Sabeer ya rungume shi, yaushe rabon da yaga dariyar shi haka duk so ya canja shi tamkar ba Sabeer d'in da ya sani ba. "Thank U so much kakanah! " Ya k'arasa fad'i yana bashi peck a kumatun shi, dad'i ya ishi D'an fillo jin Sabeer d'in shi cikin farinciki kamo hannun shi yayi ya rik'e tare da cewa "Ka yafe min marin da nayi maka Sabeer nayi regretting akan haka" Girgiza kai Sabeer yayi yana murmushi yace "Kada ka damu Abbah ya wuce " Sake rungume Sabeer yayi yana bubbuga bayan shi. "Ni an mance da ni da.... " Daddy ya k'arasa maganar da hannun shi na alamar shima ayi hugging nashi, da sauri d'an fillo ya janyo shi ya had'asu ya rungume su acikin jikin shi. Sun jima a haka kafin su rabu da juna nan Sabeer ya mak'ale jikin D'an fillo yana zuba mishi shagwa6a son ranshi shi kuma yana lalla6a shi, dariyar yak'e kawai D'an fillo yake yi, sun jima suna hira kafin kowa ya tafi ya kwanta zuciyar Sabeer fal farinciki a wannan daren yayi baccin da ya jima bai yi ba. Washe gari da safe ya tashi saboda d'oki da kanshi yake had'a kayan shi cikin trolley bags nashi saboda zumud'i saboda a yau yake son tafiya zuwa k'auyen su Suhaima ya fara fayyace mata abin da yake damun shi. Bayan ya gama had'a kayan ne ya d'auki phone nashi ya kirawo Jiddah maganar mintuna biyar yayi da ita ya kashe wayar, saboda tsananin mamaki Jiddah kusan sumen zaune tayi na jin inda Sabeer yake neman address a wurin ta na gidan su Suhaima, tura mishi tayi ta message saboda ita ma sauri take a yau jirgin su zai tashi zuwa yawan honeymoon wanda gama wayar ta da Suhaima kenan Sabeer ya kirawo ta kanta ya d'aure sosai amman ta bar komai sai sun dawo tukunna. Zaune Sabeer yake durk'ushe gaban Mumy cikin bedroom nata, gwiwar shi a k'asa ya sanya hannun shi saman k'afar ta idanun shi hawaye ne yake fitar wa, gama shiryawar shi kenan zai tafi ya shigo bedroom d'in ta cikin rawar murya ta kuka yace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104