Chapter 52
Chapter 52
fito ta shirya kanta cikin wani lace black and touch flower's pink colour d'inkin riga da skirt ne sunyi mata cif tayi kyau kam abinka da farar fata, tana cikin fesa perfumes ne ta jiyo muryar Aunty Aliya tana fad'in "Ashe kai ne tafe sannu da zuwa " D'an mamaki ne ya kama Suhaima ita dai tasan Sabeer baice mata zai zo ba, Jiddah ce ta sanar mata zuwan ta, amman bari taje ta duba ko bak'on Aunty Aliya ne, don haka sai ta janyo wani k'aramin veil pink tayi rolling dashi sannan ta fito. Kusan suman tsaye tayi ganin Sabeer da suka had'a ido dashi yana jifanta da wani sanyayyan murmishi har da wani d'aga mata gira. Tana kok'arin k'arasa wa inda yake ta jiyo sallamar Jiddah don haka sai kawai ta juya da sauri ta taro ta cikin farinciki, cikin tsokana tace "Maman twin's sannun ki da zuwa " "Yawwa Amaryar mu wallahi har kin fara kyallin amarcin gashi sai wani cika kike mene sirrin me Aunty Aliya da Yah Aliyu suke baki ne?" D'an murmishi Suhaima tayi tana sunkuyar da kai tare da cewa "Ke koh! Kin cika surutu" Ta k'arasa fad'i tana turo bakin ta, dariya Jiddah tayi kafin tace "Allah zan fad'awa Yah Sabeer idan ya kama wannan bakin kada yayi mishi ta sauk'i tunda aikin shi murgud'a baki da turo shi sai ya koya mishi h...... " Kafin ta k'arasa fad'in hankali sai kawai ta had'a ido da Sabeer yana faman kallon su, turus taja ta tsaya saboda mamaki kafin kuma ta wayance tana cewa "Ah Yah Sabeer kai ne?" Yana d'an hararar ta yace "A'a bani ba ne " Er dariya tayi tana k'arasa wa inda yake tana cewa "Ayyah Babban Yaya ban kula da kai ba ne " "Dole kice haka tunda gulma ta rufe miki idon tun da kika shigo kike gulmata ina kallon ki " "Kaiii Yaya ni ba gulmar ka ba fah nayi ba hirar mu muke ko Suhaima?" Ta k'arasa maganar da shagwa6a tana langa6e kai ta kalli Suhaima tana kifta mata ido alamar kada ta sanar shi abin da ce, batasan duk yaji ta ba d'auke kai kawai yayi yana murmishi shi dai kusan tsaf familyn shi sun d'an fi jituwa da Jiddah saboda kusan halayyar su d'aya, dariya Suhaima take kafin tace "Ni ba ruwana bansan me akai ba " "Auuu! Haka ma zaki ce shikenan " Tana gama fad'in haka ta mik'e fuuu tare da wuce d'akin Aunty Aliya, er k'aramar dariya Suhaima ta saki don Jiddah ta bata dariya, yayin da Sabeer yake binta da kallo cike da sha'awa don sosai dariyar tayi mata kyau dimples nata da yake so duk sun fito. Ganin yanda yake bin ta da kallo ne yasa ta d'an tsargu ta nutsu kafin tace "Au ashe bamu gaisa ba, ina kwana? " Ta fad'i tana rufe bakin ta da hannu, d'an murmishi yayi yana cewa "Baby bana cikin nutsuwata gaba d'aya " Gabanta ne ya d'an fad'i kafin tace "Subhanallah me yasa meka? " Fuskarta d'auke da damuwa ta furta hakan. "Baby abin da yake damuna lokacin auren mu yayi nisa da yawa, 2 month's fah aka sanya ni da nafison 3 week's, yanzu gaba d'aya fah 2 week's muka ci acikin wata 2 " Kallon shi take kawai idan banda abin Sabeer wata biyu nawa yake idan Allah ya basu aron rai, wasu ma shekara ake sanya wa ko wata 6 amman basu damu ba sai shi, amman sai ta danne mamakin ta saboda ganin yanda duk ya koma sai fitar da huci yake idanun shi har sun d'an canja launi saboda damuwa gashi ya wani kafeta da ido tamkar zai had'iye ta haka yake jin shi ga tsugunnawar da tayi ta k'ara wani sanya tunanin cikin zuciyar shi sai a lokacin ya sake tabbatar wa Suhaima yarinya ce k'arama. Anya bazai d'aga mata k'afa ba yana ganin tamkar zai iya cutar da ita a yanda yake jin shi, amman da wuya ya iya juriyar hakan don ma yau yaga ta k'ara cika kamar yanda Jiddah ta fad'i ga hips nata da boobs nata sun dad'a fitowa, wani had'iyar yawu yayi lokacin da ya kai idanun shi kai wanda ya sanya shi kusan kwarewa, da sauri ya kau da kai lallai Annabi yayi gaskiya da yace kada kana kallon matar da ba taka ba don bakasan inda idanun ka zasu kai gashi yau idanun shi sun ja mishi ganin abin da zai hanashi bacci cikin jin dad'i, daman can ba wani jin dad'in baccin yake ji ba tun lokacin da idanun shi suka fara ganin Suhaima. Muryar Suhaima da yaji ne yasa shi d'ago wa ya kalleta yana sauke ajiyar zuciya, sai da gaban ta ya fad'i da ganin yanda eyes nashi da face nashi suka canja, cikin kwantar da murya tamkar mai rad'a tace "Sabeer bana son kana sanya damuwa cikin ranka kada ya janyo maka wata matsalar please , wata 2 d'in kamar yau ne" D'an murmishin yak'e yayi kafin yace "Ba komai Baby na hak'ura amman ki tabbatar idan kika zo hannuna Hmmm.... " Yak'i k'arasa maganar tashi, cikin rashin fahimta tace "Kamar ya idan nazo hannun ka? " "A'a ba komai Baby " Ya k'arasa maganar da dariyar mugunta a d'an tsorace ta kalle shi don ta gama tsarguwa, ganin haka ya sanya shi danne dariyar shi don kada ya tsorata ta yace "Calm down Baby matsoraciya ba fah wani abun nake nufi ba, yanzu me zaki ba ni naci? " Ya fad'i hakan yana bagarar da zancen don baya son ta sanya shi a ranta. "Me kake so nayi maka? " "Baby fura ma ta isheni" "Ita kadai kawai? " D'an girgiza kai yayi kafin yace "Kaiii Baby anya zan iya shan furar nan kuwa kada ta dame ni fah " D'an zaro ido kad'an tayi sannan tace "Furar ce zata dame ka, me take maka? " D'an murmishi yayi sannan yace "zaki san kome take min amman ba yanzu " Ya fad'i yana d'aga mata gira kan ya cigaba da cewa "Eh Baby kiyi min kunun da kike min zan je na dawo " "To shikenan " Daga haka ya mik'e ya fita, ita kuma ta fad'a falon Aunty Aliya ta tarar da ita suna hira da Jiddah. Jiddah na ganin ta ta harare ta kan tace "Shine nace zan zo kika fad'a mishi yazo koh? " D'an murmishi Suhaima tayi tana cewa "Kinsan Allah Jiddah bansan da zuwan shi ba ko da safe munyi waya bai fad'a min, idan ya fad'a min zai zo ai zan fad'awa Aunty Aliya koh? " Murmishi kawai Aunty Aliya tayi, "Ni fah kinsan abubuwa zamu tattauna masu mahimmanci kin je kun wani lik'e kuna hira " Er kunya ce ta kama Suhaima don ga Aunty Aliyah a zaune a wurin, d'ago kanta tayi ta harari Jiddah tana tuna mata da akwai Aunty Aliya a wurin fah. Dariya Jiddah ta sanya kafin tace "Uhm sabon salo yau ke ake jin kunya Aunty Aliya fah " Dariya tayi sannan tace "Allah ya shirya ki Suhaima yau wani sabon salon aka fito dashi to wallahi tun wuri yarinya ki cire iyayin kunyar da kika yafa a toh" Cewar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104