Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,184 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

"Mumy nah! Ki yafe min kisa min albarka tare da yi min addu'ar samun nasara tafiya da fushin ki ba k'aramin barazana zai zame min ba" Juyar da kanta gefe tana share hawayen fuskar ta, Daddy da shigowar shi kenan shima yabi sahun yanda Sabeer yayi yana cewa "Sweetheart kiyi hak'uri ba laifin Sabeer ba ne so ne kiyi mishi fatan samun nasara please " Jiyowa tayi ta kalli Sabeer da Daddy da suke durk'ushe a gaban ta wani kwarjini da cika ido d'a da uban suka yi mata ta rasa me zata ce bakin ta yayi mata nauyi ta kasa bud'e shi tayi magana. Rarrashin ta da lalla6awa Daddy ya dunga yi wa Mumy sun dad'e a haka kafin Sabeer cikin dashashshiyar murya yace "Mumy ki taimaka wa rayuwata please kada na mutu" Kallon shi tayi da sauri gaban ta yana fad'uwa idanun shi sun yi ja suna fitar da hawaye, "please Mumy nah! " Ya fad'a can k'asan mak'oshi, Mumy ta gaji da jin wannan maganar a wurin Sabeer ta gaji da ganin fitar hawaye a idanun d'anta, hannun ta yana rawa kamar mai jin tsoron ta6a abu ta d'ora hannunta saman gashin kan Sabeer tace "Ka tafi Sabeer kaje Allah ya kare min kai " Basu yi tsammanin jin wannan maganar a bakin ta ba don haka sai suka tsaya suna kallonta kamar was7 sokaye, d'an murmishin yak'e tayi hawaye na fita a idanun ta tace "Ka tafi kada yamma tayi maka ka kula da kanka " Rungume ta yayi cikin farinciki shi da Daddy suna zuba godiya kafin Daddy ya rik'o hannun ta zuwa compound d'in gidan Sabeer na rik'e da d'ayan hannun Mumyn, gaba d'aya family na D'an fillo sun fito suna sallama da Sabeer, sai da Sabeer ya bisu one by one yana rungume na sallama, sannan daga k'arshe driver ya bud'e mishi kofa ya shiga mota idanun shi akan iyayen shi yana kallon yanda Mumy ta fad'a jikin Daddy tana kuka. Kauda kanshi yayi suna nan tsaye driver yaja motar suka fita daga gidan, kowa yana mamakin saukowar Alhj Ahmad d'an fillo har ya amince da buk'atar Sabeer wasu sun tausayawa Sabeer don sunsan Sabeer bazai jure zaman k'auye ba yayin da wasu kuma suka cika da farinciki daman a rayuwa dole ka samu mai tausaya maka idan kana cikin damuwa wasu kuma a lokacin zasu yi farinciki da ganin ka cikin haka..... Hmmm fan's ya kuka ga wannan page d'in? Anya Mumy da D'an fillo da Hajjah har cikin zuciyar su suka aminta da tafiyar Sabeer kuwa?. Sai ku biyo ni next chapter don jin yanda zaman shagwa6a66en nan zai kasance cikin karkarar k'auye koya zata kasance? Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/8, 7:15 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey SaNaz Ina kike Khadijah Neenah cool wannan shafin naki ne kyauta na murnar taya ki kammala littafin ki mai suna WASU MAZAN.. Hak'ik'a kin fad'akar damu ya kuma nishad'antar Allah ya k'ara basirah da k'arfin ido, ina miki fatan Alkhairi! ❣ PAGE 49-50 Bayan tafiyar Sabeer Mumy kasa danne kukan ta tayi da gudu ta wuce side d'in su bedroom ta shige ta hau kuka sosai na tausayin halin da Sabeer zai shiga da kuma kukan takaici da bak'in ciki akan wata banza 'yar k'auye d'anta kamar Sabeer zai tafi neman soyayyar ta. Da haka Daddy ya shigo ya fara rarrashin ta bayan ya janyo ta jikin shi, dakyar ta shiru tana sauke ajiyar zuciya, sai da Daddy yaga tayi bacci sannan ya kwantar da ita ya fita duk jinshi yake babu dad'i na tafiyar Sabeer. Daddy yana fita daga bedroom d'in Mumy ta bud'e idanunta tare da sakkowa daga saman bed dama tayi hakan ne don Daddy ya fita ya bata waje, tana son ta samu nutsuwar da zatayi tunani na d'aukan mataki akan shegiyar yarinyar nan da zuri'ar ta don sam bazata ta6a amince wa Sabeer ya auro mata d'iyar talakawa ba, talakawan ma na k'auye wanda basusan komai ba sai nemo da kiwo inaaa abin da bazai ta6a yiwuwa ba, daman ta barshi ne don kafin ace za'a yi auren tasamu mafita haka ta tsunduma a tunani sosai na samun mafita kuma bazata yi abin da Sabeer da Daddyn shi zasu zargeta da hana wannan auren ba. ***** ***** ***** Suna tafiya a mota Sabeer kuma ya kwanta tare da tukunkune jikin shi waje d'aya tamkar mai jin bacci, hawaye ne suke fita a idon shi yana kewar iyayen shi yana kuma tunanin yanda zaman shi anan zai kasance shin Suhaima zata kar6e shi matsayin masoyin ta sannan ya 'yan uwanta zasu kar6e shi matsayin mai son 'yarsu, wannan tunanin shi yake dad'a dagula lissafin Sabeer kada su kore shi su hanashi Suhaima tsoron shi d'aya kada su hanashi neman soyayyar Suhaima. Sai da driver yazo wurin da suka ta6a had'uwa da Suhaima anan Sabeer ya bashi umarnin tsayawa, bayan yayi parking ne sosai Sabeer ya tsaya yana kallon wurin yana tuna wani al'amari da ya ta6a faruwa a wajen har wani murmishi ne ya su6uce mishi. Nan Sabeer ya yiwa driver magana akan ya fito mishi da kayan shi, bayan driver ya fito dashi ne nan Sabeer yace mishi ya koma gida, yana nan tsaye driver yaja motar ya tafi zuciyar shi fal tausayin Sabeer don yasan bazai ta6a iya zaman wannan k'auyen mai kama da daji ba nan cikin zuciyar shi yayi mishi addu'ar fatan dacewa. Sabeer ya d'an jima a wajen yana dad'a nazarin wajen gaban shi na fad'uwa saboda ganin garin ya fara d'an duhu don dab ake da akirawo sallahr mangarib. Wani d'an saurayi ne yazo zai shige Sabeer ya rasa ta yaya zai mishi magana da yaga yana kok'arin wuce shi ne yasa shi yin kar6in hali yace "Assalamu Alaikum" D'an jiyowa yayi ya kalli Sabeer kafin ya tsaya nesa kad'an dashi yace "Waalaikumussalam " "Ammm inason zan yi mata tambaya please " Saurayin cikin mamaki ya ke kallon shi don bai zaci Sabeer yana jin hausa ba ya d'auka bature ne ko balarabe yazo yin wani abin a k'auyen nasu. "Allah yasa na sani" D'an sauke numfashi Sabeer yayi tare da cewa "Don Allah ko kasan gidan wani uhm... " Ya d'an yi shiru kad'an yana tuna sunan Yayan Suhaima da Jiddah ta sanar dashi d'an murmishi ya saki tare da ya tuna sunan yace "Yawwa sunan shi Aliyu yana da k'anwa Suhaima kuma manomi ne " D'an murmishi saurayin yayi kafin yace "Na gane shi nasan gidan " Wani sanyin dad'i ne ya kwararanya cikin zuciyar Sabeer cikin murna yace "Yawwa don Allah taimaka min ka kaini gidan " "To shikenan " Nan saurayin yayi gaba Sabeer kuwa sai ya tsaya kamar an dasa shi ta ina zai iya d'aukar trolley d'in nan, ganin Sabeer ya tsaya yasa saurayin dawowa yace "Lafiya? ". "Ko zaka iya taimaka min da trolley d'in bazan iya d'auka ba please " Saurayin bai yi mamaki ba don kallo d'aya zaka yiwa Sabeer kasan cewa d'an hutu ne, d'an murmishi yayi tare da kinkimar jakar, nan Sabeer ya rataya jakar laptop d'in shi suka tafi, tun ana tafiya ba'ayi nisa ba Sabeer

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});