Chapter 59
Chapter 59
da ya rage musu ya mallaki Suhaima yayi mishi nisa, haka suka tafi duk jikin shi yayi sanyi har Musaddiq na tsokanar shi. Bayan kwana 2 Jiddah ta dawo gidan su Suhaima tare da mai yin gyaran jiki wanda zata yi mata na tsayin kwanaki 5, sannan ta taho mata da d'inkunan ta gaba d'aya, a lokacin duk suka fitar da wanda zata yi amfani dasu komai da komai aka had'e su bag guda 2, sauran kayan lefen kuma Jiddah zata tafi dasu ta kai su gidan Suhaima, bayan duk sun gama shirye shiryen su sannan Jiddah ta tafi baza ta dawo ba sai ana gobe za'a yi kamu zata kai Suhaima wajen lalle da gyaran gashi ta tafi ta bar mai gyaran jikin anan. Nan mai gyaran jikin nan ta cigaba da yiwa Suhaima duk da kyau da Suhaima ta k'ara wannan karon kuwa da Sabeer zai ga Suhaima mybe ya rud'e iya rud'ewa don kuwa wani irin laushi da santsi da fatar ta take yi na daban ne ga wani ni'imtaccen k'amshi da take fitarwa ta ko'ina a wajenta fatar ta har wani yellow yellow yake tsabar gyaran da tasha, ban da wanda Aunty Aliya take mata wanda fulani suke yi idan zasu aurar da yaran su. **** **** **** *KOMAI NISAN LOKACI....* Kamar yau aka sanya bikin Sabeer da Suhaima tsayin 3 month's sai gashi lokaci yazo kamar kiftawar ido, tun ranar talata da safe wajen 10am Jiddah tana gidan su Suhaima har Yaya Aliyu yana mata fad'an yawan zirga zirgar ta yayi yawa kada ta cutar da Babynta ko ita kanta don gashi cikin nata ya d'an fito kad'an ana ganin shi don ma dogowa ce shi yasa ya 6oye a jikinta, zum6ura baki tayi tana cewa "Ni dai Yaya Aliyu ka kyale mu nan da kwana 3 ma fah har angama bikin " Murmishi kawai yayi ya girgiza kai sannan ya fita daga gidan soyayya tsakanin Suhaima da Jiddah daga Allah ce had'in Ubangiji ne. Agurguje suka gama breakfast sannan suka tafi zuwa cikin gari har da mai gyaran jikin suka tafi zasu ajiye ta a gidanta, suna ajiye ta kuwa suka nufi wajen wani katafaren shago wanda ake gyaran gashi, kunshi da komai ma wanda ya kunshi gyaran jiki. Suna zuwa mai shagon musulma ce nan ta tar6e su cikin fara'a bayan ta basu wajen zama sun zauna suka gaisa sannan Jiddah tace "Sister gyaran gashi da lalle irin na amare zaku yi mata wanda zaku zage iyakar fasahar ta ku yi mata, don inason Yah Sabeer ya ganta ya rud'e da yawa " Dariya suka yi Jiddah da mai shagon tare da tafawa tace "Kada ki damu Hajia Jiddah kinsan mu ba yabon kai ba mun iya abubuwa na kwarewa a wajen nan don haka zaki sha mamaki da kaina zan yi mata ma don nasan Yalla6ai Sabeer ya cika miki bag da money" "Kamar kuwa kinsani don ba k'aramin ji da Babyn nan nashi yake ba" "Naga alama ai gashi sun dace da junan su kyawawa dasu " Daga nan aka fara yiwa Suhaima gyara tun daga wankin k'afa zuwa manicure and pedicure, sannan aka fara yaryad'a mata lalle ja da bak'i irin na amare, amaren ma 'yan gata. Bayan an gama yin lallen ne ya kama iya lokacin da ake buk'atar shi aka wanke shi, wow masha Allah kowa awajen haka yake fad'i ganin irin wani mugun kyau da yayi wa Suhaima tamakar lik'ashi aka yi ba zanawa shi aka yi ba. Daga nan aka fara yi mata gyaran gashi shima an d'auki tsayin lokaci ana yin shi Suhaima ta fito tsaf da ita gwanin sha'awa ko mace ta ganta zata birge ta balle uban gayyar ya ganta ai ba magana, itama Jidda sai da akayi mata lallen da gyaran gashin tukunna suka biya ta. Har sun fita Jiddah ta dawo tace "Sister gobe fah kizo gidan nawa wajen 4pm zaki mata makeup don gobe ne kamu bama son african time ne" "Kada ki damu Hajia Jiddah zan zo akan lokaci " "Okay sai anjima " Fitowa tayi daga shagon ta shiga bayan motar inda Suhaima take zaune nan driver yaja su sai gidan Jiddah , suna zuwa sallah suka yi sannan suka ci abinci suka zauna hutuwa. "Washhh! Allah na gaji Jiddah sosai " Cewar Suhaima tana yatsina fuska, dariya Jiddah tayi kafin tace "Yarinya ai agajiya baki yi komai ba sai an fara event's don ma ba wani event's da yawa zamu yi ba" D'an zaro ido Suhaima tayi kan tace "Ke ce sai k'asusuwa na sun kusa 6a66alewa" Tuntsire wa da dariya Jiddah ta sake sannan tace "Idan ma sun 6alle Yayana zai gyara su" Murmishi kawai Suhaima tayi nan suka suka cigaba da hirar su, kafin kuma suka k'ara fita zuwa wajen da zasu gabatar da event na kamu wajen yayi kyau sosai duk da ba'a yi mishi decoration ba sai gobe da safe wad'anda aka d'auko zasu yi, bayan sun gama ganin wajen ne suka dawo gida. Sai wajen 5 na yamma Suhaima ta fito drive zai mayar da ita gida, nan Jiddah tace "Gobe fah da safe za'a zo a d'auke ki ke da kawayen ki wad'anda zasu je nasan Aunty Aliya ma zata zo da Babaa Lantana ma duk su zo" Gid'a kai kawai Suhaima tayi ta rufe murfin motar suka tafi sai after ishsha su iso gida tana fita daga motar driver ya juya ya tafi yayin da Suhaima ta k'arasa shiga gidan agajiye take lik'is. Wanka kawai ta iya yi tabi lafiyar katifa ko takan abinci bata bi don a k'oshe take, bacci mai nauyi ne ya d'auke ta don ko kiran da Sabeer yayi bata ji ba, shima a nashi 6angaren yasan gajiya tayi kawai don haka shima ya kwanta amman yaso jin muryar ta kuwa. Washe gari da safe kuwa Suhaima kusan makara tayi ma don lokacin da take breakfast ma wajen 11 na safe a lokacin Jiddah ta kirata ta shirya driver ya taho, tana kashe wayar ne ta lalubo number Sabeer ta kirawo shi don taga kiranshi na jiya da dare, bai d'aga ba sai ya kashe kiran nata shi ya kirawo ta. "Amaryar ta ina son ganin beautiful face naki nayi kewar ki da yawa kodan anjima zamu had'u a wajen kamu zan ga yanda Baby na ta koma tsayin kwanaki 6 ban gan ki ba nasan kin k'ara girma ta ko'ina koh? " Shiru tayi mishi murmishi yayi don yasan bazata amsa ba, kafin kuma su d'an ta6a hirar su irin ta masoya daga k'arshe suka yi sallama da junan su, tashi tayi ta zura hijab nata fari mai hannu kawai ta fito don taji Aunty Aliya tana ce mata ga driven yazo. "Yanzu Aunty babu da wanda zan tafi ni kadai zan tafi" "Eh Suhaima ki tafi kawai zamu taho da yamma kafin a fara kamun kin ji " Gid'a kanta tayi cikin sanyin jiki ta fice daga gidan. Suna zuwa gidan Jiddah mota nayin parking Jiddah ma ta shigo gidan ita take driving d'in ma. "Amaryar mu kin ganni ko wallahi daga wurin da za'a yi kamun nake naje naga yanda suka shirya wajen yayi kyau " Cewar Jidda tana rik'o hannun ta suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104