Chapter 11
Chapter 11
d'an lele kuma d'an gata, anyi suna Lafiya an tashi Lafiya inda yaro yaci sunan shi Muhammad Sabeer wanda Dr Ahmad d'an fillo ya rad'a mishi sunan da kanshi, inda kuma ya bawa Dr Faridah kyautar wani gida babba mai kyau da wata had'add'iyar mota jeep duk gift ne na jin dad'in haihuwar Sabeer, Hajjah Hauwaa kuwa gift d'in sark'ar gold ta bata tsadaddu dasu tun daga sark'a, d'an kunne abin hannu (warwaro), sark'ar k'afa da kuma rings guda biyu kud'i sosai ta fitar ta siya mata su. Haka Sabeer ya cigaba da girma ana ji dashi sosai, makarantar shi dukka a k'asar waje yayi su, Sabeer kyakkyawan matashin saurayi ne d'an shekara 27-28 ya had'u ta ko'ina ga kyau ga kud'i, sai dai sangartacce ne na ajin k'arshe gashi d'an shagwa6a don iyayen shi da kakannin shi sunyi matuk'ar sangartashi, so suke nuna mishi sosai gashi daman shi kad'ai Allah ya basu ba kwa6a ba harara duk abin da yake so suna yi mishi sosai, Sabeer bai ta6a neman wani abu ya rasa ba, duk abin da yace yana so jiki na 6ari ake yi mishi don kada ranshi ya 6aci, gata sosai yake samu gashi yanzu ya kammala karatun shi ya dawo gida. **** **** **** CIGABAN LABARI... Yana fita daga side d'in nasu part's d'in kakannin nashi ya nufa yana wani yatsina fuska tamkar wani mai jin amai, ya sanyo kanshi cikin babban parlour d'in sai ga wata house girl ta taho fita hannun ta d'auke da tire wanda saman shi jug ne mai d'auke da so6o sanyaye sai k'ananun cups akai guda biyu da d'an wani bowl guda uku 'yan manya d'aya na d'auke da cup cakes, d'aya kuma egg rolls sai na k'arshen samosa, irin tazo zata wuce ta kusa da Sabeer sai tsautsayi ya sanya tsantsin tiles ya kwashe ta gaba d'aya tayi baya kayan hannun ta kuma suka yi kan Sabeer. Unexpected yaji saukar abu mai sanyi da d'umi a jikin shi sai wani cup d'aya da ya fad'o kan k'afar shi ya had'u da tiles ya tarwatse har ya yanki Sabeer a k'afa kad'an jini ya fito, baisan lokacin da ya bud'e baki ya kwalla wata k'ara mai k'arfi tare da yin wani tsalle don ba k'aramin firgita yayi ba don ko kula da tahowar ta bai yi ba, ga zafin yankewar da yayi. Hajjah Hauwaa tana bedroom d'in ta taji k'arar d'an lele da sauri ta tashi ko takan d'an kwalin ta bata bi ba tayo downstairs da d'an gudu irin na tsofaffi a rud'e. House girl d'in nan kuwa tuni ta tashi daga fad'uwar da tayi a k'asa duk da kuwa zafin da taji na fad'uwar haka ta daure ta tashi ta tsugunna tana kuka tare da bawa Sabeer hak'uri, don tun kafin ya dawo ake jan kunnen su da 6ata mishi rai su kiyayi 6acin ran shi, sai gashi yau tsautsayi ya ritsa da ita daga dawowar shi jiya. Sabeer tsalle da ihu kawai yake yi, a dai dai lokacin Alhj Ahmad d'an fillo ya sanyo kanshi cikin parlour ranshi a 6ace, saboda bak'on da yayi yana jiran a kawo musu abin ta6awa a baki ba'a kawo ba shine ya taso da kanshi, abin kamar a mafarki yaji ihun Sabeer aikuwa da sauri ya k'arasa parlourn jiki na 6ari. Lokaci d'aya Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suka shigo parlourn, wajen Sabeer gaba d'aya suka yi cikin matuk'ar tashin hankali don sam basu kula da house girl d'in da take durk'ushe tana zunduma kuka. Alhj Ahmad d'an fillo janyo Sabeer jikin shi yayi ya rungume shi cikin rawar murya ya fara cewa "Sabeer what happened to U? "waya ta6a min kai? " Duk wannan tambayar Alhj Ahmad d'an fillo yayi ta a rud'e. Cikin sangarta da salon shagwa6a Sabeer ya nuna jikin shi da k'afar shi da take fitar da jini, a kid'ime suka kalli jikin nashi da k'afar shi saboda tsabar rud'ewa sai yanzu suka kula, cikin tashin hankali Hajjah Hauwaa tace "wa yayi maka wannan rashin mutuncin Sabeer? " Ta fad'a tana mai dafe kirjin ta tare da zaro idon ta waje, Alhj Ahmad d'an fillo kuwa saboda tsabar tashin hankali kasa magana yayi sai zuciyar shi da take bugawa da k'arfi. Hajjah Hauwaa ta kama hannun Sabeer tare da cewa "Sabeer open your mouth and explain me please " Bai yi magana ba sai hannun shi da ya d'aga dakyar ya nuna saitin da 'yar aikin take tsugunne tana kuka jikin ta na rawa, zaro idanun su suka yi lokaci d'aya sannan Alhj Ahmad d'an fillo ya bud'e baki cikin tsawa mai matuk'ar firgita wa yace "keeee zo nan " 'yar aikin a kid'ime ta tashi ta nufi inda suke tsaye, jikin ta na matuk'ar rawa ga hawaye na zuba a idanun ta, hannun ta gaba d'aya a saman kanta don tasan ita yau ta ta, ta k'are.... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz _This page is for you my Namecy Ayusher Ilias writer d'in YA SAYYADI, ina tayaki murnar kammala littafin ki YA SAYYADI Allah ya k'ara basirah da k'arfin ido ina yin ki sosai Namecy Allah ya bar zumunci😍 PAGE 15-16 Tana k'arasowa inda suke Alhj Ahmad d'an fillo ya sanya hannun shi ya wanka mata mari a kumatu, kafin ta dawo hayyacin ta Hajjah Hauwaa ita ma ta wanka mata marin a d'ayan kumatun, ihun kuka kawai 'yar aikin take yi saboda ba k'aramin shigar ta marukan suka yi ba, kallon ta suke sai huci sukeyi cikin harara Hajjah Hauwaa tace "me kike kallo da zakiyi wa Sabeer haka, baki da hankali ne, ina so kafin cikar mintuna 5 Ki barmin gida " Duk da tsananin zafin marin da 'yar aikin tasha hakan bai hanata durk'usawa a k'asa ba cikin kuka take cewa "don Allah kuyi hak'uri tsautsayi ne amman kada ku kore ni bazan sake kwatanta hakan ba " Cikin 6acin rai Dr Ahmad d'an fillo yace "baki ji abin da aka ce miki ba sai na kira police sunyi gaba da ke, wlh kika bari na kirawo police gidan nan sai kin yabawa aya zak'in ta " A kid'ime 'yar aikin ta mik'e jikin ta na rawa ta fara kok'arin barin parlourn, Sabeer wanda yake jikin Dr Ahmad d'an fillo ya lafe yana sauke ajiyar numfashin ihun da ya gama ya bud'e baki dakyar yace "keee ki zauna kada ki tafi but ki kiyaye gaba, kika sake min haka bazan Kyale ki ba " Cikin mamaki Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suke kallon shi sun ma kasa furta komai, da sauri 'yar aikin ta tsugunna tana murmishin farinciki cikin rawar murya tace "Ngde yalla6ai Allah ya kare ka yanda ka taimake ni kai ma Allah ya taimake ka a duk inda kake, kuma zan kiyaye gaba insha Allah ngde ngde sosai " D'aga mata hannun shi yayi d'aya tare da cewa "is okay zaki iya tafiya " Jiki na 6ari ta bar wajen Sabeer ya bita da kallon tausayi don tabbas tausayin ta ne ya sanya shi barin ta don ta cigaba da aiki.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104