Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sakarwa junan su a lokaci d'aya, tukunna Daddy yace "Hey Mrs Hussein d'an fillo thanks for ur fantastic kiss" Fari da eye's nata Mummy tayi tare da kama hannun shi suka nufi upstairs don ta shirya shi zuwa fita office. WANE NE SABEER HUSSEIN D'AN FILLO? SORRY FANS BAN DA CHARGE NE, MU HAD'U A NEXT PAGE DON SANIN WANE SABEER. AISHAT A MUH'D ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 13-14 Family d'in Alhj d'an fillo asalin su irin fulanin nan ne wanda suke da arzik'i sosai na dukiya da ababan kiwo, Alhj Ahmad d'an fillo shine d'a d'aya a wajen mahaifin shi da mahaifiyar shi sai 'yan uba k'annen shi su uku dukka mata shi d'aya ne namiji mazauna garin adamawa state, shi yasa mahaifin shi ya tsaya akan bashi ilimin boko, duk da su ma matan ya sanya su a makarantar iyakar su secondary ya aurar dasu. Bayan Ahmad ya kammala karatun shi na fannin Lafiya ya samu aiki sai iyayen shi suka aura mishi wata Hauwaa wadda ta kasance 'yar uwar shi ce, watannin su uku da aure iyayen shi suka yi accident a hanyar su ta zuwa airport don zuwa k'asa mai tsarki domin gabatar da hajji, dukannin su suka rasu, mutuwar ba k'aramin girgiza Ahmad da matar shi Hauwaa tare da sauran 'yan uwan su tayi ba, sosai mutuwar ta shige su amman haka suka rungume hak'uri don sunsan haka Allah ya tsara zata faru. Bayan shekara d'aya da rasuwar iyayen shi matar shi Hauwaa ta haihu 'yan biyu suka samu, sunyi matuk'ar murna da farinciki, inda suka bar musu sunan su na Hassan da Hussein, sun cigaba da rainon yaran su cikin kulawa, watan su uku da haihuwa Hassan ya rasu sakamakon zazza6i mai zafi da ciwon ciki da yayi wanda kwanaki biyu yayi yana jinya a hospital ya rasu, sosai mutuwar Hassan ta bige su don sai zafin mutuwar iyayen shi ta dawo mishi sabuwa a lokacin, haka suka dangana suna masu bawa Hussein kulawa. Hussein yana da shekara hud'u Dr Ahmad d'an fillo ya samu transfer zuwa Malam Aminu kano teaching hospital, ba 6ata lokaci ya tattara komai nasu suka dawo garin Kano, sai da ya fara zama a gidajen hospital d'in kafin ya gina nashi gidan, don zaman garin Kano yayi mishi dad'i. Bayan an gama mishi ginin suka dawo cikin sabon gidan su a lokacin Hauwaa ta haifi d'an ta na biyu Omar, bayan shekara biyu ta sake haihuwar Usman, daga Usman sai Aminu sannan autar su Fadilah, sun cigaba da rainon yaran su cikin kulawa da k'auna makarantu masu kyau da tsada Dr Ahmad d'an fillo ya sanya yaran shi, sai dai sun fi bawa boko mahimmanci fiye da ilimin Islam, a lokacin Dr Ahmad d'an fillo ya tsunduma harkar business sosai wanda nan da nan kud'i sosai suka fara samuwa ba kad'an ba. Haka lokaci ya cigaba da tafiya yaran shi dukka sun girma kowannen su ya gama karatun shi yana aiki, Hussein business d'in da mahaifin shi yake ya tsunduma a ciki, Omar kuma yana aikin Bank, Usman kuma a wani babban company na abokin Dr Ahmad d'an fillo yake aiki a matsayin GM na company d'in, sai Aminu da yake lecturing a BUK, sai k'aramar su Fadilah da take karatun degree a wannan lokacin, wanda gab take da ta kammala har an sanya lokacin auren ta da wanda zata aura, iyayen shi masu kud'i ne shima haka yana da kud'i abokin yayan ta Omar ne, lokacin da ya nuna yana son ta sosai iyayen ta suka yi farinciki da hakan, saboda suna da kud'i don Dr Ahmad d'an fillo da 'ya'yan shi basa harka da talakan mutum sai ta kama, don akwai su da kyamar talaka harkokin shi sai da masu kud'i 'yan uwan shi. Shiyasa ba 6ata lokaci aka sanya lokacin auren Fadilah da Mustapha, bayan ta kammala degree d'in ta aka yi biki sosai sun kashe kud'i a bikin, bayan auren Fadilah suma Yayannin ta kowanne ya fito da matar aure duk yaran masu kud'i ne daman gashi akwai su da kyau irin na fulani ga kud'i kuma da wayewa, sai da ban da Babban Yaya Hussein don shi harkar neman kud'in shi ya sanya a gaba bai fiye, kuma iyayen nashi sam basu tak'ura mishi ba da yayi aure, kafin bikin ne Dr Ahmad d'an fillo ya gina k'aton gida mai d'auke da part's biyar kuma kowanne part babba ne sosai kuma upstairs ne, an kashe kud'i sosai a wannan gidan kafin bikin suka koma can da zama abin su. Sai da Omar, Usman da Aminu suka haifi yara kowanne biyu biyu kuma kowanne yaro da tazarar shekara wajen uku a tsakani,tukunna Hussein ya kawo matar da zai aura Dr Faridah cikakkiyar likitar mata ce wato gynecology a k'asar India tayi karatun ta, iyayen ta masu kud'i ne sosai ne kuma abokin Dr Alhj Ahmad d'an fillo ne sosai da sosai, lokacin da Dr Ahmad d'an fillo yaji d'an shi Hussein Dr Faridah zai aura ba k'aramin farinciki suka yi ba shi da Hajja Hauwaa, nan aka sanya lokacin biki two weeks kawai, an kashe kud'i bana wasa ba a wannan auren, don su kansu matan Omar, Usman da Aminu sun san an auro matar so kuma ta gaban goshin surukan nasu don yanda suka ga ana ji da ita tun kafin ta shigo gidan. Dr Faridah Bashir kyakkyawa ce kuma wayayyiya ce sai dai akwai ta da wulak'anci ba kad'an ba, gata kuma ta tsani wani talaka ya ra6e ta, kanta kawai ta sani, ga nuna tak'ama da tsantsar ak'idar Boko, kuma mahaifin ta hospital babba ya bud'e mata nata na kanta don su biyu kad'ai Allah ya bashi daga Faridah sai k'anwar ta Zahra, ga zata auri mai kud'i don Hussein duk yafi 'yan uwan shi kud'i, wad'annan halayen nata su suka k'ara mata matsayi cikin zuciyar surukin ta Dr Ahmad d'an fillo fiye da sauran surukan nashi, yana ji da ita matuk'ar gaske. Bayan auren Hussein da Dr Faridah sai da suka yi wajen shekara uku ko 6atan wata bata ta6ayi ba, sosai hankalin su ya tashi nan aka shiga ziyartar asibitocin k'asashen waje domin bincikar lafiyar su, amman k'alau suke lokaci ne bai yi don komai kud'in ka sai lokacin da Allah ya nufa zaka samu abu zaka same shi, balle haihuwa da lafiya wanda kud'i baya ta6a siyan su sai lokacin da Allah yaso zai baka, gajiya sukayi da zuwa hospitals suka zubawa sarautar Allah ido tare da tsananta addu'a sosai a wajen Ubangiji, Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suma duk'ufa da addu'a suka yi sosai don suna k'aunar son ganin jikan su na wurin Hussein da Dr Faridah. Sai da suka kwashe shekara hud'u da aure kafin Allah ya bawa Faridah ciki, murna da farinciki bazai fad'u ba irin wanda suka yi, nan suka dunga rainon cikin cikin so da k'auna. Bayan wata tara Faridah ta haihu an samu baby boy kyakkyawan yaro dashi, anyi murna da farinciki sosai, ranar suna ansha taro an kashe kud'i duk wanda yaje sunan yasan an haifi

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});