Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 71

Chapter 71

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

" Dariya aka sake kwashewa da ita, sannan Khairat tace "Ina fah zata rabu dashi Aunty taga kyakkyawan saurayi sabon jini ga kud'i da ilimi inace ko aji ma ta ta6a shiga wannan shegiyar Jiddah ce ta wayar da ita " Wani irin kuka mai tattare da bak'inciki Suhaima ta saki saboda ta kasa rik'e kukan nata, aikuwa ganin haka suka kwashe da dariya tare da tafawa, sannan Aunty Fadilah ta bud'e bottle d'in faro da yake hannun ta sai kawai Suhaima jin saukar ruwa mai sanyi da taji ajikinta har sai da ta saki ajiyar zuciya mai karfin gaske. "Shegiya mara zuciya idan kin cika ke mai zuciya ce kare bai d'auke ba ki rabu da Sabeer daga yau " "Aunty mu taya ki " Cewar Zahra da Khairat sarakan tsiwa. "Ku taho mana 'yan 'ya'yana masu kishin 'yan uwan su " "Don Allah Aunty kuyi hak'uri kada ku min haka " Cewar Jiddah tana kuka da karfi tana kare Suhaima, ture ta Aunty Fadilah tayi nan Zahra da Khairat suka dunga bud'e bottles na faro suna shek'a mata a jikinta suna zaginta da yi mata rashin mutunci duk gaba d'aya sun jik'e jikinta jagab da ruwa gashi don mugunta da ruwan sanyi suke amfani. Yusrah yayar Jiddah da batason hayaniya tabar dakin bata jin dad'in abin da suke mata ba amman da yake miskilace sai kawai ta bar wajen. Jiddah tana cikin kuka ne d'ago kan da zata yi sukayi 4 eye's da Sabeer tsaye ya hard'e hannun shi a kirjin shi eyes nashi sunyi ja tare da fuskar shi, sai da gaban Jiddah yayi mugun fad'uwa ganin yanda d'an uwan nata ya rikid'a kamar ba Sabeer ba, bata ta6a ganin shi cikin makamancin irin wannan yanayin ba. Zahra ce ta fara arba da Sabeer ta ankara dashi tuni tayi cilli da bottle d'in hannun ta jikinta ya fara rawa na tsoro, haka ma Khairat itama ta cillar da robar tana rarraba ido Aunty Fadilah kuwa sai da gabanta ya fad'i da suka had'a ido da Sabeer don bata ta6a ganin shi a haka ba batasan lokacin da ta saki nata robar ba. Cikin wani irin taku na fusata ya k'arasa shiga d'akin bai kalli inda suke ba ya k'arasa inda Suhaima ke zaune jikin ta jagab da ruwa har tsiyaya yake d'ago ta yayi tare da kallon Jiddah yace "Kai ta wani bedroom d'in ki bata kaya ta canja " Muryar shi dakyar take fitowa saboda tsananin 6acin rai jikin shi har wani rawa yake, da sauri Jiddah taja hannun Suhaima wadda take kuka sosai suka fita. Aunty Fadilah, Zahra da Khairat kuwa suman tsaye suka yi ko motsin kirki sun kasa yi, Zahra bata ankara ba taji saukar wani zazzafan mari mai saurin kurmanta mutum wani ihun k'ara ta saki da karfin gaske ya fara dukanta yana ball da ita cikin zafin nama, Khairat tun kafin azo kanta take rusa kuka sosai tana dana sanin biyewa zuciyarta da Aunty Fadilah. Bata ankara ba taji saukar nata marin wanda har sai da bakin ta ya fashe, belt d'in jikin shi ya cire ya fara narkar su cikin tsananin 6acin rai har wasu hawaye ne suke zuba a eyes nashi zuciyar shi tana zafi. "Sabeer mene haka kashe su zaka yi ne akan wannan matsiyaciyar yarinyar ne " Bata gama rufe bakin ta ba taji saukan mari akan face d'in ta da mamaki ta d'ago kanta ta d'auka Sabeer ne ya mare ta sai taga ashe Daddy ne. Zaro ido tayi cikin tsorata tace "Yaya! " Sake kwad'a mata mari yayi tare da cewa "Rufe min baki mara kunya banza mara kunyar wofi " Cikin 6acin rai Daddy yake fad'in haka ashe Jiddah ce ta kirawo shi tana kuka tana yi mishi bayanin abin da yake faruwa shine ya taho. Dakyar aka kwaci Zahra da Khairat a hannun Sabeer aka fita dasu daga d'akin duk ya farfasa musu jikin su ko kuka sun kasa saboda azaba, zubewa yayi kan carpet tare da rik'e kanshi da hannun shi yana sakin wani ajiyar zuciya. Babu dad'ewa gaba d'aya kusan family suka had'u a gidan Jiddah har da Dr Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa wadda take kuka wiwi Sabeer zai kashe mata 'yan jikoki akan wannan shegiyar yarinyar amman ta kasa yiwa Sabeer fad'a saboda son da take mishi sai hucin da take saki. Dr Faridah ma ranta a 6ace sosai da kanta tayi treatment d'in su Zahra da Khairat a inda suka ji ciwo dole ta d'auki mataki akan wannan shegiyar, Aunty Fadilah kuwa tayi tsit da ita sai raba ido take saboda ba k'aramin tsoron Daddy take ba. Suhaima bayan ta canja kaya ne tana kwance wani zazzafan zazza6i ne ya rufe ta kuka take sosai yau taga karshen wulak'anci dole ta rabu da Sabeer duk da kuwa son da take mishi bazata jure wulak'anci da zagan mata da mahaifiya da suke wadda take kwance a kabari. Dakyar Daddy ya rik'o hannun Sabeer suka fito zuwa parlour kallo d'aya Dr d'an fillo yayi mishi yaji duk haushin dukan da yayiwa su Zahra ya kau hankalin shi ya tashi sosai ganin yanda d'an lelen shi ya koma dole yayi wa su Aunty Fadilah tatas don kawai Sabeer yaji sassauci ya nuna musu abin da suka yi basu kyauta ba daga karshe kuma yayi musu iyaka da matar Sabeer. Daga karshe tafiya suka yi gaba d'ayan su, Mumy kuwa aranta haka tace kowa ya gama nashi rashin mutuncin akan wannan yarinyar yanzu lokacin ta yayi dole tayi nasarar raba Sabeer da Suhaima rabuwa ta har abadaaa......... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/9, 9:15 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ* *PAGE 87-88* Shiga cikin bedroom d'in da take a kwance yayi hawa kan bed d'in yayi yana kok'arin had'a ta da jikin shi duk da jikinta ba kwari sai da tayi kok'arin matsawa da sauri, cikin marairaicewa Sabeer yace "Baby please kada ki hora ni akan abin da akayi miki, bazan jure hakan ba " Kamar zai yi kuka yake maganar, cikin muryar ta wadda ta dushashe tace "Mu hakura da junan mu Sabeer 'yan uwanka basa sona sun tsaneni" "Nooo! Baby ki daina fad'in haka bazan iya rabuwa dake ba, ni ina sonki kuma ni zan zauna dake basu ba " Duk yanda yaso yanda yaso ya had'a ta da jikin shi don ya rarrashe ta tak'i yarda, gashi kukan ta yana ta6a mishi zuciya, bata ankara ba taji Sabeer yana fitar da hawaye. Kallon shi ta tsaya yi kawai ana cikin haka Jiddah ta shigo da sauri ya goge hawayen shi don bayason ta gani, cikin sanyin murya yace "Jiddah ki tayani rarrashin Baby tace bazata koma gidana ba" Cikin jin tausayin su ta zauna tana kama hannun Suhaima tace "Haba Suhaima mene hakan idan kika yi hakan ai abin da suke so kenan, taya zaki zalunci kanku bayan kuna son junan su kice zaku rabu, kiyi hak'uri don Allah kada ki rabu da Yah Sabeer yana son ki " Rarrashin ta sosai Jiddah take dakyar ta ciyo kanta ta amince, rungume ta Sabeer yayi don jin dad'in abin da ta fad'a. Har an

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});