Chapter 23
Chapter 23
jin hirar tasu tuntsire wa da wata irin dariyar ta rainin hankali. Wani parlour suka dad'a shiga tsayawa Jiddah tayi tare da jiyowa ta kalli Suhaima tace "Don Allah Suhaima kiyi hak'uri da abin da Zahra tayi miki bata kirki ne " Mayar da kwallar Suhaima tayi tare da kwakwalo murmishi yak'e tace "Kada ki damu Jiddah duk abin da akayi min zan d'auke kai saboda ke " Rungume ta Jiddah tayi cikin farinciki da jin abin da Suhaima tace mata "Thank U so much dear " "Jiddah ke da wane? " Da sauri Jidd ta saki Suhaima jin maganar Umman ta wani kallo Umman take yiwa Suhaima kamar irin kallon da Zahra tayi mata. Da murmishi akan fuskar Jiddah taja hannun Suhaima zuwa kusa da Umma tace "Umma ni da Suhaima ne, itace wadda nake baki labari, Suhaima wannan ce Ummana" Da sauri Suhaima ta durk'usa k'asa cikin girmama wa tace "Umma ina yini? " "Lafiya " Cewar Umma cikin halin ko inkula daga k'arshe ma cewa tayi "Jiddah kiyi sauri ki wanka yanzu mai makeup zata zo kinsan yau ne dinner wadda Hajia Faridah ta shirya na family koh" Tana gama fad'in haka ta wuce ko kallon inda Suhaima take bata sake yi ba ta wuc abinta cikin tak'aici Jiddah tabi bayan Umma da kallo kafin ta dawo hankalin ta kan Suhaima da har yanzu take durk'ushe ta kasa tashi saboda mugun sanyin da jikinta yayi na abin da ta fara cin karo dashi tun shigowar ta gidan su k'awarta Jiddah. A lokacin hankalin Suhaima ya tashi sosai ta d'auka Umman Jiddah zata kar6e ta da fara'a ba kamar Zahra ba, shi yasa tayi wa Jiddah alk'awarin kauda kai daga abin da akayi mata, amman fah Jiddah tayi mata abubuwan da zata iya jure duk wani cin kashin su akanta na tsayin kwana biyu daga lokacin da tafi gidan su babu wanda zai sake ganin ta balle har yayi mata kallon banza. "Kiyi hakur..... " Jiddah ta fad'i hakan tana d'ago Suhaima fuskar ta da tarin damuwa sosai, da sauri Suhaima ta toshe mata baki da tafin hannun ta tare da k'ak'alo murmishin dole tace "Kada ki bani hak'uri Jiddah me akayi min babu komai kada ki damu please " Girgiza kai Jiddah kawai tayi tare da rik'o hannun ta tana cewa "Mu tafi bedroom d'ina ki huta kiyi hak'uri da halin 'yan gidan mu kusan haka suke " Gaban Suhaima ya sake fad'uwa da jin abin da Jiddah ta fad'a anya zata iya zaman gidan nan kuwa... Aishat A Muh'd 🏌🏻♀ [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 A SANADIN SON KI 💝 Written by Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 34-35 Hannun ta d'auke da cup wanda coffee ne aciki ta shigo cikin bedroom d'in turus ta tsaya ganin shi a zaune ya zabga tagumi, ta rasa abin da yake damun d'an nata gaba d'aya ya canja tun ranar da ya doki Fadilah, ajiye cup d'in tayi saman center table d'in k'arasa wa inda yake tayi har zuwa lokacin Sabeer baisan da zuwan Mumyn nashi kusa dashi ba, girgiza kawai tayi tana kallon shi kafin ta sanya hannun ta d'ora shi tayi saman kafad'ar shi tace "Son tunanin me kake? Me yake damun ka ne kwananan " Girgiza kai yayi tare da cewa "Nothing Mumy " Zama tayi kusa dashi tana mai kamo hannun shi cikin nata kallon shi take cikin kulawa tace "Son baka da wanda zaka fad'a wa damuwar ka duk duniyar nan sama da ni, ka sanar dani ko zan iya baka shawara please " Cikin gajiya da maganar Mumy yace "Nace miki babu komai ki rabu da ni please " Ya k'arasa maganar da d'an tsawa kad'an. "Shikenan Son koma mene Allah ya yaye maka " Cikin zuciyar shi ya amsa da Amin. "Ga coffee kasa na lura tun breakfast baka k'ara cin wani abin ba, idan ka gama ka shirya ka kayan ka saman bed kasan yau ne dinner na sister d'in ka Jiddah kuma kowa na family zai je don haka ina buk'atar ganin ka please Son " Shiru yayi mata bai kulata ba itama bata sake bi ta kanshi ba ta wuce ta fita don idan da sabo ta saba da shariyar Sabeer wani lokacin musamman idan yana cikin damuwa bai fiye son magana ba. Mumy tana fita ya zame ya kwanta kan sofa yayi matashin kai da hannayen shi, idanun shi lumshe su yana tunanin Suhaima sosai yake mamakin yanda yarinyar ta tsaya mishi cikin zuciyar shi, shi baisan so ba amman da alama ya fad'a son wannan yarinyar, dummm gaban shi ya fad'i da ya tuna yanda 'yan uwanshi da iyayen shi suka tsani talaka balle ita a k'auye ma take, yanzu shi ya zai yi zuwan shi wajen uku k'auyen ko mai kama da ita bai gani ba ya rasa yanda zai yi. Son da yake mata bazai iya hak'ura da ita dole ne yasan yanda zai 6ullowa al'amarin, bayan bikin Jiddah dole ya koma k'auyen ya neme ta, zai nuna mata so sannan zai bawa iyayen ta kud'i sosai ya basu gida da mota da jari sosai yanda bazai samu matsala ba ta 6angaren iyayen shi idan suka ga iyayen ta masu kud'i ne, wani murmishi ya saki na kamar wanda ya samu nasara ma sai lokacin hankalin shi ya kwanta, kiran sallahr mangarib ne ya katse mishi tunani, toilet ya shiga yayi alwala ya fito kai tsaye masallaci ya wuce. Babban hall ne wanda ya k'ayatu da decorations masu kyau da k'ayatuwa wajen ya tsaru yayi kyau sosai, ga haske tamkar ba dare ba sanyi Ac ta ko'ina ban da k'amshin tsadaddun turaren jikin manyan masu kud'in da suke zaune a wajen kamar anyi 6arin turare a wajen. Manyan hamshak'an mutane ne masu kud'i sosai a wajen ansha kwalliya ta kece raini ga tsadaddun sutturu da aka sanya mutane suna zazzaune a wajen da aka tanadar musu, slow music ne ke tashi kawai a wajen duk mutane an hallara, family d'in Jiddah gasu nan ga friends na iyaye dana amarya sai na yayyanin amarya dana k'anen ta abin dai ya tsaru gwanin sha'awa kowanne da kalar ankwan su, haka 6angaren dangin ango gasu nan da nasu ankon daban suma sunyi kyau sosai. Amarya da ango ake jiran shigowar su babu dad'e wa mc ya fara sanar wa shigowar ango da amarya kowa ya nutsu ya zubawa kofar shigowa kallo don ganin shigowar amarya da ango. Cikin takun k'asaita da nutsuwa Jiddah da angon ta khaleel suka shigo hannun su sark'e da junan su, Jiddah tana sanye da wata farar gown har tana jan k'asa sai ash head da ta sanya yana da kwalliyar flowers silver ajiki pose da hill nata dukka ash ne masu kwalliyar silver ajiki tayi kyau sosai abin ta, haka angon ma Khaleel yasha shadda ash colour sun yi matukar kyau da dacewa da junan su, sai watsa musu wasu fararen furanni da red ake yi. Bayan su kuma Suhaima ce tasha light pink na gown sai head nata pink mai d'an duhu tasha makeup tayi matukar kyau tamkar ba Suhaima ba, ba wanda zai ganta ya zaci daga k'auye ta fito tama fi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104