Chapter 24
Chapter 24
'yan birnin kyau a wajen don ba k'aramin haskawa tayi ba tamkar itace ma amaryar ba Jiddah, don kallo dawowa yayi kanta abin da yasa duk ta dibirbice ta rasa inda zata yi saboda idanun mutanen da suke kanta sai murmishin yak'e take. Da haka ta samu waje ta zauna bayan ango da amarya sun wuce wajen zaman su, nan aka fara gabatar da dinner cikin nutsuwa da wayewa, gaba d'aya Suhaima a tak'ure take saboda bata saba zuwa irin wad'annan wuraren ba, har zuwa lokacin da amarya da ango suka fito domin taka rawa nan 'yan uwa da abokanan arzik'i suka fito domin yi musu lik'i. Dr Faridah ce ta fito filin wajen nan mutane suka bata hanya ta wuce zuwa inda su Jiddah suke tsaye ita da angonta suna taka rawa a nutse, bag d'in hannun ta ta bud'e ta fito da bandir d'in 1k ta fara watsa musu tamkar bata san zafin kud'i ba sai da ta gaji tukunna ta bar wajen. D'ago kan Suhaima yayi dai dai da barin Dr Faridah wajen aikuwa suka had'a ido wani irin bugawa zuciyar Suhaima tayi da k'arfin gaske haka ma a 6angaren Dr Faridah d same abin da Suhaima taji haka taji itama, amman sai ta kawar da kanta daga barin kallon ta cikin zuciyar tana tunanin irin wannan kyan na yarinyar da bata ta6a ganin ta ba sai yau, gashi ta d'an birgeta kad'an da taga duk da kyan da take dashi but bata da rawar kai irin na 'yammatan da suka waye sosai kafin kuma watsar da tunanin ganin Suhaima ta cigaba da sha'anin gaban ta. Har zuwa lokacin da aka buk'aci amarya da ango su yanka wedding cake nasu, nan 'yan uwan amarya da ango 'yan kad'an suka rakasu wurin cake d'in babu 6ata lokaci suka yanka Khaleel ya bawa Jiddah a baki itama ta yanko tare da d'an tsugunna wa kad'an ta bashi nan aka hau tafi. Suhaima ba k'aramin birgeta suka yi ba sai sakin murmishi take ita kad'ai, zuwa yanzu ta d'an saki jikin ta da zaman wajen, amman sam duk da haka har yanzu bata ji sha'awar ta auri irin d'aya daga cikin wad'annan masu kud'in ba, tana kallon yanda su Zahra da sauran sisters d'in Jiddah suke wurgo mata harara tsanarta k'arara akan fuskar su, d'aga kafad'ar ta tayi alamar ko a jikin ta, tana fatan jibi iyanzu tana k'auyen su cikin gidan su, sai su harari wata ba ita ba. Ana gaf da tashi a wurin Sabeer ya shigo cikin hall yana sanye cikin wata light blue sky na shadda tsadaddiya har da hula akanshi, d'inkin shi irin wanda matasan yanzu suke yin shi ba k'aramin kyau yayi ba, a daidai lokacin kuma Suhaima ta taso zata fita daga hall d'in don amsa kiran wayar da Yaya Aliyu yake yiwa Jiddah. Karo suka yi da junan su inda Suhaima ta bige kanta da kafad'ar shi, dafe goshin tayi tare da yamutsa fuska tace "Washh Allah na " D'ago kan da zata yi ta bashi hak'uri suka had'a ido da junan su, kallon second 3 Suhaima tayi mishi ta gane ko wane tuni jikin ta ya fara rawa tsoro ya kamata kada ya d'auki fansar abin da tayi mishi a wajen da batasa kowa ba sai Jiddah, shima Sabeer kallon ta yake cikin mamakin me ya kawo ta nan kuma don ko acikin mafarki ya ganta sai ya gane ta wane ya kawo ta wajen bikin k'anwar shi? Ta dalilin wata zo nan? wad'annan tambayoyin ya yiwa kanshi a lokacin d'aya. Ganin ya zuba ido yana kallon ta yasa ta saurin fita daga hall d'in, cikin zafin nama ya bita yana cewa "Hey tsaya mana kece wan...." Kafin ya k'arasa maganar tashi yaga wayam babu kowa a wajen, ta gudu kenan abin da zuciyar shi ta fad'a ba guduwa tayi ba 6oya tayi, ina ta 6uya kuma?. Daga d'an nesa kad'an na hango Suhaima tana lek'en shi jikin ta na 6ari zuciyar ta na bugawa da k'arfi, ganin yana dube dube a wurin ya sake fad'ar mata da gaba, bata k'ara rud'ewa ba sai da taga ya nufo inda take. Yana daf da k'arasa wa inda take ne yaji an rik'o hannun shi da sauri ya juya ga ashe Mumy ce da tarin kannen shi, wayyo Allah ya furta cikin zuciyar shi don yasan yanzu yaran nan zasu sa mishi ciwon kai da hayaniyar su "Yah Sabeer kazo mu d'auki pic's please " Cewar wata sistern shi zai yi magana kenan Mumy tayi musu magana da ido, dariya suka yi don su fahimci me take nufi, aikuwa hannun shi suka kama zuwa cikin hall d'in bashi da yanda zaiyi ya bisu yana tafiya yana dube dube har sai da suka wuce ciki sam ranshi babu dad'i ba haka yaso ba yaso ta tsaya su yi magana ta fahimta amman dole ya binciko wanda yayi inviting d'in ta zuwa wajen nan. Fitowa Suhaima tayi daga inda ta 6uya tana sauke ajiyar zuciya har da gumi ta had'a duk tayi wani iri kallo d'aya mutum zai mata yasan a firgice take, zama tayi a gefen wasu flower's tana sauke numfashi.... Aishat A Muh'd 🤸🏻♀ [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 36-37 Suhaima ta d'auki wajen 5 minutes kafin ta d'an nutsu ajiyar zuciya ta sake saukewa a karo na ba adadi tace "Alhmdllh Allah nagode ma da wannan mutumin bai kamani ba da yau nasan zai ya rama abin da nayi mishi" Suhaima ta furta hakan a sarari, wayar hannun ta ne ya cigaba da ringing dole ta dai daita nutsuwar ta tayi picking ganin sunan Yaya Aliyu ne akai. Bayan sun gaisa ta tambaye shi jikin Aunty Aliyah daga nan shima ya tambaye ta yanayin zaman nata don tun da ya tafi hankalin shi yak'i kwanciya sam ga jikin Aliyah sai a hankali, boye mishi gaskiya Suhaima tayi tace tana nan lafiya yanzu ma suna wajen party dinner d'in Jiddah, daga k'arshe yayi mata nasiha sosai tukunna suka yi sallama ta ajiye phone d'in saman k'afarta tare da rafka tagumi tana tunanin yanda za'a yi ta koma cikin hall d'in bayan taga Sabeer ya shiga ciki, nan take zuciyarta ta bata shawarar zaman ta anan waje har a tashi nan take ta aminta da shawarar zuciyar ta sake gyara zama tayi tana jiyo sautin kid'an da yake tashi a wajen partyn. Sai wurin 11 na dare aka tashi lokacin Suhaima har ta fara gajiya da zaman jiran Jiddah ta fara gyangyad'i a wurin, sam Suhaima batasan har an tashi ba gyangyad'in ta kawai take sabida ta gaji gashi bata saba kaiwa wannan lokacin ba batayi bacci ba gashi ba'a saitin k'ofar shiga hall d'in take ba balle a taji fitowar mutane. Sai da aka watse a wurin bai fi mutane d'ai d'aiku ba Suhaima ta farka daga gyangyad'in da take tamkar wadda aka tasa haka ta bud'e ido firgigit, ganin yanda duhu yayi sosai yasa Suhaima rarumo wayar Jiddah dake saman k'afarta ta duba time, wani zabura tayi ta mik'e tsaye cikin tashin hankali ganin har k'arfe 11:30 tayi na dare, ai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104