Chapter 61
Chapter 61
k'asa suka nufi motar da ango yake, suma friends nata biyar sun sha gayun su cikin wani material pink da blue sun yi kyau kam ba laifi, Jiddah ma ta shirya cikin wata gown ta material pink colour tayi kyau itama hannun ta yana rik'e dana mijinta Khaleel shima yayi kyau cikin wata lallausar shadda fara. Tun da suka taho Sabeer ya saki baki da hanci yana kallon Babyn shi yanda ta koma tamkar ba ita ba, duk da yasan Babyn shi mai kyau ce ko batayi kwalliya but wannan kyan da tayi na daban ne har baisan lokacin da ta shigo motar ba sai jin daddad'an k'amshin turaren ta cikin hancin sh. Wata ajiyar zuciya ya sauke mai d'an k'arfi baisan lokacin da ya rik'o hannun ta ba d'aya ya d'ago fuskarta da d'ayan hannun yana mata wani irin kallo da eyes nashi wanda suke a wani lumshe lumshe, bakin shi yakai saman goshin ta yayi kissing d'in shi sannan ya cika fuskar ta yana cewa "Masha Allah " Abin da ya fad'a kenan a lokacin da suka bar harabar gidan Jiddah but still hannun shi yana cikin nata yana wani irin murza su a hankali, ita kuma Suhaima kunya ce ta kama ta sosai ganin abin da Sabeer yayi mata wanda bai ta6a kwatanta yi mata sai yanzu kuma tasan kwalliyar tace ta burgeshi sosai. Sabeer bakin shi yayi mishi nauyi ya kasa magana saboda wani irin abu da yake ji yana ratsa shi a cikin kowanne lungu da sako na jikin shi, da haka suka k'arasa wajen da za'a gabatar da dinner d'in kallon ta yake tamkar yau ya fara ganin ta. A d'an sace Suhaima ta kalle shi yasha wata shadda milk colour mai d'an duhu milk d'in sai aikin jikin rigar brown zare akayi amfani dashi har da babbar riga karo na farko kenan da Suhaima taga Sabeer cikin shigar manyan kaya sai taga yayi mata kyau ya k'ara mata wani girma da kwarjini a idanun ta har da hula milk and brown ne kai Sabeer ya had'u kawai ta ko'ina gaskiya Suhaima tayi dacen miji haka shima yayi dacen mata sun dace da junan su sosai. Motar su tana k'arasa wa wajen tayi parking but basu fito ba suna zaune aciki, sai da Jiddah suka k'araso sannan suka fito hannun su na sark'e waje d'aya suna gaba Jiddah da Khaleel, Musaddiq da Mufidah a bayan su sai kuma friends na Suhaima su biyar d'in nan a bayan su. Wajen yasha decoration na peach, red, pink and white ko'ina sai kyalkyali yake ga mutane duk an zazzau suna zaman jiran shigowar ango da amarya wani slow music ke tashi na wakar india ta Piya O Re Piya Tere....., itace ke tashi a wurin suna shigowa kallo ya dawo kansu sai fesa musu wani spray mai kyalkyali ga wasu furanni farare da ja da ake watsa musu a jikin su har suka k'arasa inda zasu zauna wata kujera ce d'aya mai d'an fad'i da zasu zauna daga bayan su kuwa wani k'aton frame ne yasha decoration an rubuta anyi zanen heart sai aka rubuta S-S ajiki wato Suhaima and Sabeer. Bayan an zazzauna ne kuma Jiddah ta bud'e taron wajen da addu'a sannan ta bayar da tak'aitaccen tarihin amarya da harshen turanci bayan ta gama Musaddiq ma ya tashi cikin tafiyar kasaita Mufidahn shi mak'ale dashi yaje shima ya bayar da tak'aitaccen tarihin ango Sabeer sannan kuma akan nemi ango da amarya su fito su d'an taka rawa. Suna tsaye wajen da aka tanada don yin rawa hannun Sabeer d'aya zagaye da kugun Suhaima d'ayan hannun kuma yana rik'e da d'ayan hannun ta ita kuma hannun ta yana zube saman kafad'un shi da haka suke d'an jujjuyawa don babu wanda ya iya wata rawa acikin su, sun birge mutane sosai yana mata magana kasa k'asa saitin kunnen ta bayyana mata irin tarin son da yake mata yake yi. Jiddah ce da Khaleel suka fara zuwa wajen suka fara yi musu lik'i nan Musaddiq da Mufidah suka taso suma daga nan sauran mutane suka fara yi musu lik'i, can na hango My Biebie dee, my Sadeey, Ummu Safwan, Zahra da sauran fan's suna faman lik'a musu 'yan five five a kunyace suke yi saboda babu mai lik'a k'asa da five hundred sai su lol 😂. Nan daidai aka cigaba da gudanar da dinner har zuwa lokacin da za'a yanka cake, Sabeer na rik'e da Babyn shi suka k'arasa wajen cake d'in wanda ya kasance hawa 5 ne yasha decoration sosai na white da peach, Suhaima ta rik'e knife na yanka wa Sabeer ya d'ora hannun shi saman nata nan suka yanka sannan Suhaima ta gutsuro cake d'in sai da ta d'an russuna k'asa sannan ta sanya mishi abaki a d'an kunyace tayi hakan tana yin murmishi. Shima Sabeer murmishin yake kafin ya sanya hannun shi ya d'ago ta tsaye tukunna ya d'an rungume ta a jikin shi ya bata cake d'in da d'an juice a cup daga k'arshe ya bita da kissing a cheek d'in ta sai d'an ihun birgewa mutane ke yi suna yi musu tafi daga haka suka koma wajen zaman su. Sannan aka fara ciye ciyen abubuwan ci da sha wanda aka shirya su na alfarma, Sabeer ne ya kallo Babyn shi cikin wani salon kallo yace "Baby nah i luv U, i really luv U bazan iya rayuwa babu ke ba ina fatan addu'ar Allah ya bar min ke har iyakar tsayin rayuwa ta " D'an murmishi Suhaima tayi kawai, hannun ta ya rik'o wanda ke rik'e da cup da juice aciki ya kai bakin shi ya d'an kur6a kad'an kafin yace "Baby baki ce komai ba fah, yanzu gobe kamar haka na zama ke kin zama ni babu zancen jin kunya kuma, kodan ma kunyar bin ta zanyi duk inda take na cire ta ko ba haka ba amarya ta? " Kamar k'asa ta tsage Suhaima ta shige haka take ji lallai Sabeer ya fitsare da yawa, yanzu ma yana mata haka balle gobe an d'aura musu aure sai kuma abin da yafi haka nan taji gaban ta ya fad'i, yana kokarin sake magana Musaddiq ya k'araso yana cewa "Ango kazo ayi pic's don dare nayi my wife ta gajiya zamu tafi gida" Tashi suka yi nan aka fara d'aukan picture's sosai da mutane, nan na d'an kutsa na samu aka d'auke mu pic's da ango da amarya sannan na samu wani table na zauna a gajiye nake lik'is, d'an waigawar da zanyi ba sai na hango su My Sadeey, My Biebie dee, Zahra, Ummu Safwan ana faman kiciniya da cinyoyin kaji bakunan su yayi dumu dumu da maik'o amman basu san da hakan ba, wani huci na saki mai zafi ganin zasu sanya ni jin kunya idan aka tambaye ni wadannan wane ya gayyace su idan aka nuna ni dole naji kunya kuwa don haka harara na dalla musu sannan na d'auke kai na lol🤣😂, gaskiya naji dad'i sosai ganin yanda fan's na ASANANDIN SON KI sunyi k'arar zuwa wannan bikin na Sabeer da Suhaima mun sha hira dasu sosai gashi har da ankon su na daban suka yi daga k'arshe muka yi sallama dasu don ni bayan amarya zan bi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104