Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,181 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na tsane shi kamar yanda yace baya son mu ya tsane m........ " Kafin ta k'arasa fad'in maganar taji an zabga mata wani wawan mari wanda yasa ta hantsila k'asa, ledar garin kwakin ta baje a k'asa ta tarwatse cikin dandaryar k'asar tsakar gidan. Ashe basu ankara da shigowar baban nasu ba gidan, yaji abin da Suhaima ta fad'a shine yayi mata wannan marin da ko babba aka yiwa sai haka, cikin rashin imani ya kama Suhaima ya hau dukan ta kamar Allah ya aiko shi, Umma tana d'aki idar da sallahr mangarib d'in da tayi kenan tana sauri ta fito don ta jawa Suhaima kunne ta daina wad'annan maganganun, don lokacin da dawowar uban su gida yayi, sai kawai taji saukar dukan da yake yiwa Suhaima runtse idon ta tayi da k'arfi hawaye na fita a cikin su tana mai addu'ar Allah yasa kada yayi mata bugun da zai illata ta. Yana dukan ta cikin fushi yana cewa "shegiya tsinanniya daman ni ai ba son ku nake ba, da zaki ce baza ki min addu'a ba sai uwar ki da Yayan ki, na tsane ku bazan ta6a kaunar ku 'yan iska matsiyata " Cikin kuka Aliyu yace "Don Allah Baba kayi hak'uri ka dai na dukan ta, ka ga Suhaima yarinya ce k'arama ba zata jure dukan nan ba " Sakin Suhaima yayi yana haki kamar wanda yake jibgar k'atu, harara ya dalla wa Aliyu tare da cewa "Don uwar ka ni zaka fad'a wa gaskiya koh ?" Kafin Aliyu ya ankara tuni Baban ya kawo mishi duka nan ya had'a su ya dunga duka kamar Allah ya aiko shi, sai da yayi musu lilis tukunna ya ce " yanzu na fara dukan ku 'yan iska, Allah yasa ku mutu na huta da ganin ku" Da sauri Umma ta runtse idon ta tana rushe wa da kuka jin mummunan kalaman da uban su yake yiwa 'ya'yan ta wanda ba yau ta saba jin su a bakin shi ba. Yana gama fad'in haka ya fice daga gidan yana fad'a kamar wani ta6a66e, Umma tana jin yana fita ta fito waje da sauri zuwa wurin 'ya'yan nata da suke kwance magashiyan a k'asa suna kukan azabar dukan da aka yi musu. Nan Umma ta rasa me zata yi musu kawai sai ta had'a ruwa mai d'umi ta fara yiwa Suhaima wanka, daman ta d'ora ruwan tun kafin mangarib, sai da ta gama yi mata wanka ta gasa mata jikin ta, tukunna ta kai ta d'aki ta kwantar da ita, sannan ta dawo wajen Aliyu ta kai shi band'aki tare da ruwan wanka tace "kayi hak'uri Aliyu na, maza kayi wanka ka gasa jikin ka " Gid'a mata kai kawai ya iya yi, sannan ta fito ta tattara garin kwakin da ya zube ta tsince shi tukunna ta jik'a musu. Dawo wa d'akin tayi ta tashi Suhaima sanya mata kaya tayi sannan ta zuba mata garin a kofi ta mik'a mata, ai kuwa da sauri ta kar6a ta hau shan shi babu k'akk'auta wa. Ido Umma ta tsura mata tana kallon kumbararriyar fuskar ta ta zuciyar ta fal tausayin su, tana nan zaune Aliyu ya shigo d'akin dakyar ya iya yin sallah sannan ya zauna, mik'a mishi nashi garin Umma tayi girgiza kanshi yayi yana cewa "Umma ki sha kawai na k'oshi " Girgiza kanta ita ma tayi idanun ta fal hawaye tace "A'a Aliyu ka kar6a kasha idan kana son ganin kwanciyar hankali na " Bashi da yanda zai yi ya kar6a ya fara sha a nutse, ita ma Umma ta d'auki ragowar tana sha, bankad'a labulen d'akin aka yi tare da shigowa ba sallama, babu wanda ya d'ago kan shi ya kalli kofar saboda sun san wane mai shigo wa d'akin a haka. Ko kallon su bai yi ba ya shige k'uryar d'akin ya zauna saman gadon tare da bud'e kunshin tsire da gurasar da ya siyo ya hau cin abin shi hankali kwance, tuni d'akin ya d'umame da k'amshin naman da gurasar suka hau had'iyar yawu dukanin su har da Umma. Abin ka da mai ciki akwai kwad'ayi gashi ba ci ake ba nan ta shiga had'iyar yawu akai akai haka ma Suhaima, kallon Aliyu yake yi zuciyar shi tana zafi na tsanar halayyan mahaifin nashi, tashi tsaye yayi tare da cewa "Umma zan kwanta sai da safe " Don idan bai fita daga d'akin nan ba zai iya had'iyar zuciya ya mutu saboda tsabar bak'in ciki, kallon shi Umma tayi tare da cewa "Allah ya tashe mu lafia " "Amin " Yace tare da fice wa a fusace. "shege mai zuciyar tsiya da bak'in hali " Babu wanda ya tanka mishi har Suhaima bacci ya d'auke ta tana had'iyar yawu na son cin naman, kwantar da ita tayi tare da lullu6e ta da zani saboda lokacin hunturu ne. Tashi tayi tare da nufar gefen gadon k'arfen nata ta kwanta a can k'arshe tana mai tunanin makomar rayuwar su a gaba, ga cikin ta da yake k'ugin yunwa da haka bacci ya fara d'aukan ta, can cikin baccin nata taji mijin nata na lalubar ta alamar akwai abin da yake nema a wajen ta, wasu hawaye ne masu zafi suka dunga fita a idanun ta, duk dare ta saba da wannan halin mijin nata gashi ba abinci kirki yake basu ba, shi yasa kullum take tashi jiki ba kwari a gala6aice, tana kuka shi kuma yana sha'anin gaban shi har zuwa lokacin da ya rabu da ita ya juya mata baya, ba dad'e wa ta fara jin saukar minsharin shi, dakyar ta iya mik'e wa ta fito zuwa band'aki tayi wanka don bata iya bacci a haka, tana fito wa ta ga Aliyu zaune a tsakiyar gidan ga tsananin sanyin da ake zabga wa cikin mamaki tace "Aliyu lafiya? " D'ago kanshi yayi tare da cewa "Umma na kasa bacci ne, zuciya ta rad'ad'i take min " Ya k'arasa fad'a hawaye na fita a idon shi, cikin tausayin shi tace "kayi hak'uri Aliyu komai tsanani yana tare da sauk'i, bana son kana sa damuwa a ran ka wani ciwon ya kama min kai, kasan kai ne mai taimakon mu, yanzu tashi kayi alwala kayi sallah tare da addu'a, ka mik'a wa Allah buk'atun ka " Tana nan tsaye yayi alwala sannan ya shige d'akin shi, tukunna ta juya ta shige d'akin ta kwanta, jikin ta babu k'arfi da ita ma nafilar zata yi ta fad'a wa Allah matsalar ta, amman duk da haka sai da ta janyo carbi ta fara istigifari tare da salatin Annabi (SAW), da haka bacci mai k'arfi ya d'auke ta........... *** **** *** *ASALIN LABARIN SU* Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: 💝 *A SANADIN SON KI*💝 *written by* Aishat A Muh'd ♻ £xclusive Writers Forum *Dedicated to My Sadeey (SaNaz)* *PAGE 3-4* Umaru direba miji ne a wurin Fatima, auren so da kauna suka yi don sai da suka d'an jima suna soyayya kafin su yi aure. Bayan sun yi aure ne suna zaman su lafia cike da so da kulawar junan su, don ma bai fiye zama a gida ba tun da direba ne shi suna tafiye tafiye zuwa garuruwa daban daban, amman hakan bai hana shi kula

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});