Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 66

Chapter 66

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,182 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

maka? " "Komai ma Baby zanci tunda ke zaki dafa min" Tana kok'arin kunna gas ne suka ji an danna door bell, kallon ta yayi sannan ya yamutsa fuska yana cewa "Yanzu haka Jiddah ce zata zo ta dame mu muna cikin hutawar mu ko lokacin da tayi nata auren wane ya tak'ura mata da zata dame mu" Dariya ta kusan kubcewa Suhaima amman sai ta danne don taga fuskarshi d'auke da damuwa, amman gaskiya har cikin zuciyar ta taji dad'i zuwan Jiddah har idan itace d'in. "Har kasan Jiddah ce ta zo? " "Of course don nasan itace zata yi zuwan wannan wurin " Tunawa da Suhaima tayi ko lokacin da zasu fito a d'aki da 11 na safe yayi shine zuwan wuri, Sabeer yasan ba mai zuwa cikin family d'in shi sai Jiddah shi yasa ya kawo ta cikin ranshi itace. Fita yayi tare da bud'e door d'in aikuwa tunanin shi ya zama gaskiya Jiddah ce da sauran friends na Suhaima wad'anda anjima kad'an zasu koma gidan su, shine suka zo yiwa Suhaima sallama. Wata harara da Sabeer ya watsawa Jiddah sai da dariya taso kubce mata amman ta danne ta tare da turo baki tace "Wai... wai kai Yah Sabeer indai muka had'u sai kayi ta harara ta ni me nayi maka? " Share Jiddah yayi yana amsa gaisuwar friends d'in Suhaima da suke mishi yana gama amsa wa ya basu hanya zasu wuce, aikuwa ya sanya hannun shi ya rankwashi kan Jiddah har sai da ta saki k'ara ta rik'e kanta nata wanda sauran kad'an ta zubar da basket d'in hannun ta. Jin k'arar Jiddah ya sanya Suhaima fitowa daga kitchen duk saurin da taso yi amman ta kasa sai a hankali ta taho, Jiddah na hango ta da sauri ta k'arasa wurinta had'e da rungume ta. "Lafiya naji kina k'ara? " Tana turo baki tare da kau da kanta daga kallon Sabeer tace "Ba mijin ki bane ya rankwashe ni akaina ba, duk abin da nayi mishi bai gani ba" Had'a ido tayi da Sabeer taga yana shafa bayan kanshi, d'an murmishi tayi tare da girgiza kai kawai wannan abu tsakanin su ne ita me zata iya yi akai, hannun Jiddah Sabeer ya kamo yana cewa "Sorry sweet sister ke kika ban haushi ina cikin hutawa zaki zo ki katse min hutu, yanzu me kika kawo mana? " Duk a hankali yake mata maganar, yayin da Suhaima ta k'arasar da friends nata cikin parlour suka zauna. "Yaya breakfast na had'awa Besty na da kai, ko an kawo muku daga gida? " Girgiza kanshi yayi cikin takaici ya furzar da numfashi, hannun shi ta kamo cikin jin tausayin shi tace "Yaya kayi hak'uri komai zai wuce insha Allah " "Nagode 'yar uwata " Dinning table suka k'arasa zama yayi sannan Jiddah ta fara jera kayan breakfast d'in kan table sai da ta gama sannan ta shiga kitchen ta d'auko su plate, cups, spoons and sauran abubuwan buk'ata na kayan tea, sai da tayi serving Sabeer tea ne sai pepper chicken and chip's da egg's, sannan ta had'awa Suhaima ta kallo inda take zaune acikin parlour ta d'an d'aga murya tace "Babyn Yah Sabeer kizo kiyi breakfast " Murmishi Suhaima tayi kan ta tashi ta taho zama tayi ta d'an fara shan tea d'in, da yake su Jiddah sunyi breakfast a gida sai kawai ta d'auko musu ruwa da drinks ta zauna a parlour cikin k'awayen Suhaima suna hira tare da kallo. Ganin yanda take cin abincin ne yasa shi cewa "Baby lafiya kuwa? " "Me yafaru? " Ta fad'a tana kai cup na tea bakin ta. "Bakya cin abincin sosai " Kamar zata yi kuka tace "Ni bana jin dad'in baki na ne " Tausayin ta ne ya kamashi cikin kulawa ya rik'o hannun ta sannan yace "Sannu Baby amman ki daure kici abincin zaki ji dad'in jikin ki" Fork d'in ya kar6a daga hannun ta bata yake abaki a hankali take kar6a har tace mishi ta koshi sannan ya rabu da ita, tashi suka yi daga dinning table d'in parlour ta dawo yayin da shi kuma ya shige upstairs. Cikin 30 minute's ya fito ya canja kaya zuwa wani black boyel takalmi ma black da watch d'in shi but bai sanya hula ba sai ya gyara gashin kanshi, sosai yayi kyau Suhaima ma binshi da kallo tayi kan ta d'auke kanta kuma tana yiwa Allah godiya da ya bata Sabeer a matsayin miji. Saukar numfashin shi taji kan face nata, d'ago eyes nata tayi suka had'a ido kafin ta janye nata, d'an murmishi yayi yana daf da k'arasa cire wannan kunyar. "Baby zan tafi gida wajen su Daddy mu gaisa " "Okay, ka gaida su Allah ya dawo da kai lafiya " Sai da ya lumshe idon shi yaji dad'in abin da ta fad'a, kafin yace "Amin Baby nah " Yayi kissing nata a kumatu sannan ya fita. Hira suka yi sosai har zuwa lokacin da 'yan uwa Suhaima suka zo, gara suka kawo kamar yanda al'adance ake yiwa amarya sai su dublan, alkaki da su cincin, wani abin dad'in a wajen Suhaima har da Baba Lantana da Aunty Aliyah aka zo. Don Aunty Aliyah kasa jurewa tayi sai da ta biyo su aikuwa Suhaima rungume ta tayi k'am tana kuka, dakyar dai aka rarrashe ta tayi shiru sannan Suhaima ta canja kayanta zuwa wani lace milk and touch pink ajikin shi sai mayafi pink da shoes nan Jiddah ta fesa mata perfumes masu sauk'in kamshi suka tafi gidan su Sabeer don damk'a amanar Suhaima a hannun su. Sakin baki da hanci suka yi suna kallon had'uwar gidan, inda Allah ya taimake su basu da yawa suka zo su 5 ne sai Suhaima, Jiddah da friends nata. Jiddah ce tayi musu jagora har zuwa part d'in Alhj Dr Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa suka tarar a parlour tana zaune ta wani hamshak'e kan kujera eyes nata d'auke da medical glass tana kallon tashar Arewa 24 suna yin film na india mai translation in hausa. Sai Dr Faridah da take gefen ta suna d'an ta6a hira jifa jifa a tsakanin su, a wani kyamace suka amsa sallamar tasu ko wajen zama ba'a basu, sai da Jiddah tayi magana cikin bak'inciki tace "Babaa Lantana Aunty Aliyah ku zauna " Nan suka zauna jikin su a sanyaye da irin tar6ar da aka yi musu, Jiddah fita tayi ta kirawo Umman ta da sauran matan gidan duk suka taho part d'in Hajjah Hauwaa sannan taje kitchen d'in Hajjah Hauwaa ta d'ebo musu soft drinks and snack's sai ruwa ta ajiye musu. Suna yamutsa fuska suka amsa gaisuwar su, sannan Babaa Lantana ta damk'a musu amanar Suhaima babu dai wanda yace komai saboda takaici Jiddah barin parlourn tayi, tana kyamar halin family d'in su. Ko drink's d'in da Jiddah ta kawo basu sha ba suka taso suka fito gaba d'aya gwiwoyi a sanyaye, sosai Jiddah ta basu hak'uri a hanyar dawowar su ta gidan Suhaima. Abinci ma sai takeaway Sabeer ya sanya akayi musu saboda lokaci ya k'ure zasu tafi, bayan sun gama ci suka yiwa Suhaima nasiha sosai Aunty Aliyah ta d'ora da bata shawarwari masu kyau. Suna yin sallahr la'asar suka ci abinci suka tafi, driver Sabeer ya

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});