Chapter 78
Chapter 78
yayi kyau Allah ya taimaka ya bada sa'a " "Amin Amin " Daga haka suka fito daga d'akin zuwa d'akin Aliyah tarar da Suhaima tana kuka ne ya sanya su tsayawa suna rarrashin ta dakyar tayi shiru sannan suka rakota d'akin ta nan ma sun jima sannan suka yi mata sai da safe suka tafi. Cikin wannan daren ya zamewa Suhaima wani irin dare na bak'inciki musamman idan ta tuna jiya kamar yanzu suna tare da Sabeer suna nunawa junan su zazzafar soyayya, tayi kuka Suhaima awannan daren har sai da taji kamar kanta da idanun ta zasu zazzago da ciwon da zafin da suke mata. ************ Cikin nutsuwa yake motsawa tare da kok'arin bud'e eyes nashi dakyar ya samu ya bud'e su saboda hasken da yake dallare mishi ido, kallon d'akin yake cikin mamakin me ya kawo shi, duk ya rame bakin shi ya bushe kallo d'aya zaka yi mishi kasan cewa bashi da cikakkiyar lafiya. "Alhamdullilah Son ka farka? " Cewar Mumy da shigowar ta room d'in kenan, cikin farinciki ta k'arasa inda yake ta zauna tare da rik'o hannun shi tana goge hawayen idonta da d'ayan hannun, don sosai lalurar Sabeer ta firgitata sosai don yau kwanan shi 3 a kwance sai drip kawai da ake sanya mishi tunda yayi doguwar suman nan. Bai kulata ba duk yanda taso da yayi magana kawai sai ya kwanta tare da juya mata baya, runtse eyes nashi yayi yana tunano musabbabin abin da ya sanya shi cikin wannan halin, tar komai ya dawo mishi cikin brain nashi a hankali wasu hawaye masu zafi suka fara sauko mishi idan ya tuna yanda Suhaima ta cuce shi bai ta6a zaton Suhaima zata aikata hakan ba agare shi. Tashi ya yunkura yayi dakyar sai dai ko taku biyu bai yi ba sai yayi luuu kamar zai fad'i da sauri Mumy ta taro shi ya fad'o jikinta a kid'ime tace "Son ya zaka tashi cikin wannan yanayin kasan jikin ka babu kwari? " Cikin fusata yake cewa "Mumy ki barni na kai Suhaima k'ara akan abin da tayi min bazan kyale ta ba sai na d'auki fansa akanta na yanda take zubar min da yara na " Wani dad'i ne ya kwaranya cikin heart d'in Mumy amman sai ta marairaice tare da cewa "Haba Son ka kyale mata Allah sai ya saka maka yanzu samun lafiyar ka shine kwanciyar hankali na " Nan Sabeer ya birkice mata sai yaje ya sanya an kama Suhaima sai sumbatu yake daga kasan ba'a ciki hankalin shi yake ba, gani haka ya sanya Mumy yi mishi allurar bacci babu dad'e wa bacci yayi awon gaba dashi ta gyara mishi kwanciyar zuciyar ta fal farinciki.... ******** Cikin tsananin 6acin rai Yaj Aliyu yake cewa "Ki fita daga gidan nan Jiddah bana son ganin ki daga ke har 'yan uwan ki macuta " Cikin rikicewar kuka Jiddah take rik'e k'ofar shiga gidan saboda kok'arin rufeta da Yah Aliyu yake yi "Yaya Aliyu don Allah kayi hak'uri ba laifi na bane inason ku wallahi baza'a ta6a had'a baki dani a cuce ku ba ka tsaya nayi maka bayani" "Tun kafin naji miki ciwo Jiddah ki fita daga gidan nan nace zan iya illata ki idan baki tafi ba " "Allah Yaya Aliyu sai dai ka kashe ni bazan tafi ba, Suhaima Aunty Aliyah kuce mishi ya tsaya ya saurare ni Suhaima ki fad'a mishi babu hannuna wajen aikata miki haka " Jiddah ta fad'i tana kallon su Suhaima da Aunty Aliyah da suke gefe suna kuka ganin yanda Yah Aliyu yake korar Jiddah. Wani irin k'ara Jiddah ta saki da k'arfi saboda yanda Yah Aliyu ya rufe k'ofar da k'arfi har yana mutstsukewa da hannun ta, a rikice Suhaima ta k'arasa wajen tare da bud'e k'ofar Jiddah ta zame hannun ta har sunyi ja sosai tana kok'arin k'arasa wa wajen Jiddah Yah Aliyu ya damk'ota tare da rufe k'ofar gidan 6am har da sanya sakata, Suhaima naji kukan Jiddah tana bubbuga k'ofar sai dai bata da ikon bud'e wa wani kuka ta fashe dashi tare da shiga d'akinta da gudu........... Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻 [4/13, 12:39 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆* Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ ♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм* *PAGE 97-98* Jiddah ta dad'e tana kuka anan sosai Babaa Lantana ce da Baba Adamu suke rarrashin ta don Yah Aliyu yak'i tsayawa ya saurare shi ranshi a 6aci yake sosai da abin da akayi wa k'anwar shi. "Babaa Lantana Baba Adamu ku taimaka min ku fahimtar da Yaya Aliyu wallahi ba had'in hannuna cikin abin da akayi wa Suhaima ni kaina yanzu binciken da nake yi kenan don gane gaskiya amman bai kamata Yaya Aliyu yayi min haka ba? " Ta k'arasa maganar tana goge hawaye. "Yanzu dai yanda Aliyu ya d'auki zafin nan ki bari har zuwa lokacin da ya huce don yanzu bazai tsaya sauraren komai ba ranshi ba k'aramin 6ace yake ba " Cewar Baba Adamu kenan. "Kiyi hak'uri Jiddah ki koma gida duk lokacin da ya huci zan sanya Aliyah ta kirawo ki awaya sai kizo " Gid'a kanta Jiddah ta iyayi kawai daga nan ta shiga mota driver ya jata, wani tsanar familyn su ya d'arsu cikin zuciyar ta yanzu da ba don sun aikata haka ba da tuni Suhaima tana tare da masoyin ta Yah Sabeer, dole zanyi iya yi na do ganin an kama wanda ya aikata haka bazan iya jure rashin Suhaima kusa da ni ba ina sonta, lallai Yah Sabeer ba k'aramin ganganci yayi ba na korar Suhaima don koda zata dawo gidan shi sai yasha wahala ba k'arama. Tun daga lokacin abubuwa suka fara canjawa don Sabeer sai da yayi wajen sati biyu a hospital kan a sallame shi, yayi wani irin ramewa sosai ko abinci baya iya ci sosai sai an matsa mishi ga wata k'asumba da ya tara yak'i yarda yaje aski agyara mishi ita sannan Mumy ma tayi kok'arin cire mishi ita da kanta amman yak'i yarda, gaba d'aya Sabeer ya canja ya koma wani iri kamar bashi ba yana zuwa aiki office amman daya dawo fah idan ya k'unshe kanshi a d'aki baya sake fitowa sai dai idan sallah zai tafi masallaci. Ya fara zama mafad'aci abu kad'an zai fara fad'a baya shiga harkar family d'in shi kamar da, har wani lokacin ita kanta Mumy tsoron kulashi take tana mai mamakin me ya canja mata d'anta lokaci d'aya haka, idan ya sake da wani suna hira har da murmishin shi to Daddy ne kawai don ko Dr Ahmad d'an fillo baya sake musu kamar da, sosai abin yake damun su a ransu Jiddah ma baya kulata sosai kamar da sai gaisuwa ce kadai ke tsakanin su idan ma har sun had'u, ita kanta Jiddah duk yanda take da son Sabeer tana jin haushin shi. Duk yanda yaso da ya fitar da Suhaima daga zuciyar ya kasa ji yake kamar ma k'ara mishi sonta yake, baya iya bacci kullum sai yaga pic's d'in ta, yayi kukan sosai wani lokacin ji yake daman zai iya cire zuciyar shi ya fito da ita ya goge son Suhaima aciki ko ya huta da abin da yake ji cikin zuciyar shi. Ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104