Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 94

Chapter 94

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta fara rauni tausayin mahaifin nata ya fara shiga cikin zuciyar ta amman tana tsoron kallonshi balle tayi mishi magana. "Haba Aliyu kada ka zama mutum mara yafiya, nasan ka da zuciya mai kyau kayi hak'uri ka yafe mishi mahaifin ka ne baka da kamar shi duk duniyar nan, Allah yana son masu yafiya idan an zalunce su, kayi duba ma da halin da yake ciki wannan kadai ma ya ishe shi " Nan Baba Adamu da Babaa Lantana suka dunga yi musu nasiha tare da nuna musu mahimmanci mahaifi agare su koda wanne laifi ya aikata a wajen ka yana nan matsayin mahaifi ba'a ta6a canja shi k'addara ce da son zuciya suka rinjaye shi ya aikata hakan, nan Sabeer ma ya fara ya fara lalla6a su akan suyi hak'uri su yafe mishi haka Aunty Aliyah ma ta sanya baki akan maganar dakyar da sud'in goshi Aliyu da Suhaima suka yafe wa mahaifin su saboda ganin girman mutanen da suka sanya baki cikin maganar. Yana kuka yana gode musu tare da sanya musu albarka Yah Aliyu dai tashi yayi kawai ya shiga d'aki baya tunanin ko makaranta zai iya zuwa yau wani abu ne yake nuk'urk'usar cikin zuciyar shi kwanciya yayi yak'i fitowa sai da yaji muryar Baba Adamu yana kira shi sannan ya fito idanun shi jawur ya samu waje ya zauna. Cikin kuka Umaru ya fara basu tak'aitaccen labarin shi bayan barin shi gidan..... "Tun da na d'auki jaka ta na tafi ban tsaya ko'ina ba sai cikin kaduna anan na tsaya cikin kasuwa ina buge buge na, na neman aiki ni ne dako da duk wani aikin k'arfi don kawai na samu kud'i na tara naji dad'in rayuwa ta,amman sai naga ko nayi aikin kud'in basa yi min albarka sai dai uban wahalar da nake sha da haka dai na samu dakyar na samu d'an rumfa ina siyar dasu kayan miya, ba laifi ina d'an ciniki akusa da inda rumfa ta take ne akwai wata mai siyar da abinci sunan ta Ladidi mai abinci 'yar duniya ce sosai awajen ta nake siyan abinci kullum, mun gaisuwar mutunci da ita gashi wani lokacin kyauta zata zuba min abinci ta aiko min shi har rumfata da haka muka d'auki tsayin lokaci ashe sona take sai daga baya take sanar min, da fari nak'i yarda ganin yanda idanun ta suke a bud'e sosai amman daga k'arshe ta shawo kaina na amince da ita, nan muka shirya yin aure nace mata banda iyaye ni maraya ne sai kawai na samu limamin unguwa ya zama wakili na ya d'aura mana aure daman agidan ta zamu zauna tun da tana da gida, farkon zaman namu munyi shi cikin kwanciyar hankali da jin dad'i amman da muka fara d'aukan shekaru komai ya canja ta fara yi min rashin mutunci kala kala na yau daban na gobe daban, gashi yanzu kasuwa taja baya d'an kayan miyar da nake siyarwa jarin ya karye mun cinye shi a abinci, daga nan fah wulak'anci take min kala kala har takai zaman gidan ya gagare ni saboda masifar ta duk wani hakk'i nawa na kanta bata sauke min na zama kamar matar ita mijin tunda ita take ciyar dani amman da sharad'in sai nayi mata aikace aikacen gidan ". Kallon shi Yah Aliyu yayi ya tuna lokacin da Umman su idan bata gama abinci ba da wuri zagi kala kala zai yi mata har da duka kuma ya dunga ball da duk abin da ya ci karo dashi agidan yana kiranta k'azama abubuwa dai kala kala babu irin wanda bai yiwa Umman su ba lallai Allah ne ya nuna mishi ishara akan zaluntar su da yayi. Ya cigaba da cewa "Haka nake yi mata aikin don kawai ta ban abinci, gashi tana tara maza agidan musamman 'yan daudu, ashe Ladidi 'yar bariki ce ta k'arshe daga baya nake jin labari har shaye shaye take agabana babu abin da na isa nayi k'arshe sai ta ware min d'aki a zaure aciki nake kwana azaba da wahala nasha shi kala kala nayi bak'i na rame sosai nayi nadama sosai gashi kullum cikin mafarkin Fatima nake da yara na, ita kuwa Ladidi bata haihuwa kwata kwata gashi na rasa me ya sanya na zauna nake bauta mata duk zafin zuciya ta kuwa gaba d'aya nayi sanyi kamar ba ni ba ni kaina nasan Ladidi ba haka ta bar ni ba don tana bin malamai sosai, da haka muka kwashe shekaru da ita ina cikin wannan wahalar, nan na fara rashin lafiya sosai dakyar nake iya tashi amman ko kud'in da zan siyi magana ban dashi, daga k'arshe dai Ladidi ta kamu da cutar HIV ban san tana da ita sai kawai........ " Wani kuka ne ya kubce mishi na tsananin bak'inciki da takaici, yayin da gaban Aliyu da Suhaima yayi mummunar fad'uwa kada Ladidi ta shafawa mahaifin su ciwon, kallon shi suke a tsorace don jin mai zai ce haka su Baba Adamu da Babaa Lantana, Aliyah da Sabeer suka tsorata suna addu'ar Allah ya sanya bata sanya mishi ba. Cikin kukan ya cigaba da cewa "Sai kawai ta yanke shawarar bazata mutu ita kadai ba sai ta goga min ciwon nata, bansan hawa ba ban san sauka ba wata rana kwatsam naga tana faman gyara gidan ta shirya lafiyayyen abinci ta kawo min amman ban iya ci ba saboda lokacin jikina babu sauk'i, na tashi zan shiga bandak'i ne naji tana magana da wata kawar ta a waya ashe abincin nan da ta kawo min duk sai da ta zuba musu jinin jikinta saboda yanzu ban da k'arfin da zan sauke mata buk'atar ta sai ta 6ullo ta wannan hanyar, ban k'arasa jin zancen ba na zube k'asa a sume don nayi matuk'ar kad'uwa da jin wannan maganar ta" Wata ajiyar zuciya Aliyu da Suhaima tare da sauran mutanen wajen suka saki jin bata yi nasara akan shi ba lallai Ladidi ta cika macuciya kuma muguwa, share hawayen fuskar shi yayi kafin ya k'arasa da cewa "Daga nan sa farkawa nayi naji ni agadon asibiti sai dai na had'u da lalurar shanyewar 6arin jiki wato paralyzed,nayi kuka nayi nadama sosai alokacin kullum cikin addu'a nake akan Allah kada ya d'auki rayuwata sai nazo na nemi yafiyar ku kullum da ku nake bacci nake tashi ina tsananin son naga na dawo wajen ku, naji ma ina jinya kafin na samu na 6arin jikina ya fara motsi da taimakon wannan liman d'in da ya d'aura ma aure da Ladidi da yake d'an shi likita ne, bayan na d'an fara magana ne na saki Ladidi saki uku wadda itama alokacin ciwon yaci k'arfin ta har ta kwanta, daga nan liman ya taimaka min da kud'in mota na taho gida na nemi afuwar ku don nasan hakk'in ku ne yake bibiyar ta dakyar na iya kawo kaina garin nan wannan shine tak'aitaccen labarina tun bayan bari na gida, ina sake neman afuwar ku 'ya'yana ". Suhaima kuka take sosai najin irin azabar da mahaifin su yasha a hannun muguwar matar nan, Cikin rad'a Sabeer yace "Baby ba kuka zaki yi ba godewa Allah zakiyi da ya tseratar da Baba daga hannun ta " Nan Aliyu ya dad'a saukowa daga fushin da yake da mahaifin

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});