Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,180 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sun san Allah ne mai azurta bawan shi a lokacin da yaso, ba wayon su ko dabarar su ne yasa suke da kud'i ba a yanzu idan Allah yayi sai ya kwace kud'in. Da sauri ta sanya hannu ta goge hawayen fuskar ta tare da jiyowa jin an dafa kafad'ar ta, Suhaima ta gani tana murmishi itama murmishin yak'e tayi kafin tace "I'm so sorry Suhaima akan abin da Umma tayi miki" "Haba Jiddah ni fah babu abin da akayi min " Ta k'arasa fad'i tana cire sark'ar jikin Jiddah bayan ta gama cirewa ne ta d'auko mata wanda su zata sanya ta d'auko wannan ta sanya. "Wow kin had'u tawan ni yanzu ki had'a ni da driver na tafi " "Okay dear " D'auko phones nata tayi ta kirawo driver magana tayi na tsayin 2 minute's sannan ta mik'a wa Suhaima wayar tace "Yana waje yana jiran ki driven " "Okay thank U " Daga haka ta d'auki bag nata suka fito tare ta kofar baya Jiddah ta nuna wa Suhaima ta fita don batason wani ya sake 6atawa Suhaima rai, bayan Suhaima ta fita driven shi ya hango ta yayi mata magana aikuwa nan ta shiga mota yaja suka bar gidan. Tun da Suhaima ta fito daga part d'in su Jiddah tazo ta wuce ta shiga mota yana kallon ta, wani mirmishin mugunta ya saki duk gajiyar da yayi dakyar yake d'aga k'afa gudowar shi daga wajen reception ko gamawa ba'a yi ba ya taho don duk ya gaji da hayaniya ganin Suhaima ne yasa duk yaji gajiyar ta wartsake cikin sauri ya shiga mota ya bisu a baya... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: A SANADIN SON KI Written by Aishat A Muh'd ♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM Dedicated to my Sadeey saNaz PAGE 40-41 Tafiya suke Suhaima sai wara ido tana kalle kalle sosai taji garin na Kano ya birgeta daman Yaya Aliyu yana bata labarin yanda yanayin garin yake kodayaushe cikin sha'awar zuwa take sai gashi a dalilin Jiddah tazo ta, karatun Qur'an ne yake tashi a motar k'ira'ar Shureim cikin suratul Ma'idah sosai karatun yake ratsa cikin zuciyar Suhaima har wani lumshe ido take tana bin karatun a hankali cikin k'asa k'asa da muryar ta. Agaban wani k'ayataccen mall driver yayi parking tare da cewa "mun iso ranki ya dad'e" D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa "Okay bari na shiga na fito " "A fito lafiya " Bud'e k'ofar motar tayi ta fito cikin takun nutsuwa take tafiyar duk da kuwa yanda gaban ta yake fad'uwa don bata ta6a zuwa irin wannan wajen ba, kawai d'auriya tayi kada ta ba da kanta amman zuciyar ta fal tsoro kamar ace kyat ta zura da gudu, har ta k'arasa wajen k'ofar shiga ta shiga ciki. A hankali Sabeer yayi parking kusa da motar da ta kawo Suhaima, fitowa Sabeer yayi sannan ya k'arasa wajen motar tun kafin ya k'araso drive ya ganshi don haka da sauri ya fito daga motar yana cewa "Yalla6ai barka da rana" Sabeer bai tsaya bawa driven amsa ba yace "Salisu me kake anan? " "Yalla6ai na kawo k'awar Jiddah nan zata yi shopping " "Okay zaka iya tafiya gida " D'an shiru Salisu yayi kafin yace "Yalla6ai Jiddah tace na jirata ta gama na mayar da ita gida don bak'uwace anan " D'an shan mur Sabeer yayi kafin yace "Oh baza kayi abin da na saka ba? " Cikin d'an tsoro da biyayya Salisu yace "Ayi min afuwa Yalla6ai yanzu zan tafi " Yana gama fad'in haka ya shiga mota yaja ya bar wajen zuciyar shi cike da d'an tsoro yanzu idan ya koma gida me zai cewa Jiddah idan ta tambaye shi ina k'awar ta, gashi bazai iya musu da Sabeer ba don kada ya rasa aikin shi don dashi ya dogara. Salisu driver na tafiya Sabeer ya saki wani murmishi dani kaina bansan ma'anar shi ba kafin ya shiga cikin mall d'in cikin takun shi na k'asaita, zuciyar shi cike da tunanin yanda yarinyar da ko sunan ta baisani ba zai tunkare ta da magana mafi daraja a wajen shi wanda babu 'ya macen da ta6a furtawa. Bayan Suhaima ta gama duk siyayyan gift's d'in da zata bawa Jiddah ne ta nufi wajen biyan kud'i, ga mamakin ta akace an biya mata cikin mamaki take kallon matar da ta fad'a mata da gani yare ce don hausan ta baya fitowa sosai. "Wane ya biya min anya nice?" Suhaima ta tambayi matar, d'an murmishi tayi tare da cewa "Yes kene aka biyawa ba ke da mijin ka bane? " Ad'an tsorace Suhaima tace " A'a ba mijina ba ne ko zanyi iya sanin wanda ya biya min?" Da mamakin abin da Suhaima ta fad'i tace mata "Yawwa ga Yalla6an can wanda ya biya miki " Matar ta nuna wajen da d'an yatsanta, bin d'an yatsan matar Suhaima tayi kallo zuwa inda take nuna mata wani irin buguwa zuciyar Suhaima tayi sakamakon had'a ido da Sabeer da tayi yana wani kasheta da murmishi zaune yake kan kujera yana kallon ta suna had'a ido ya d'aga mata gira tare da yi mata wink, wayyo Allah nah yanzu wannan mutumin duk inda nayi sai ya biyo ni yanzu ya zanyi na guje mishi?, fad'in haka cikin zuciyar ta. A sace ta k'ara kallon matar inda Sabeer yake sai taga ya tashi tsaye yana gyara rigar dake jikin shi, da sauri ta fara tafiya zuwa hanyar da zai kaita ta fita sauri kawai take tana fatan ta ganta a cikin mota ta shiga ciki ta zauna sun bar wajen. Tana fitowa ta k'arasa inda suka yi parking amman wayam bata ga motar ba nan ta sake dudduba wa ko ba wurin ba ne taga dai still anan suka yi parking, toh ina motar da driven? Zuciyar Suhaima ta ambata. "Ni nace ya tafi " Fad'in Sabeer kenan wanda ke tsaye a bayan ta tamkar yasan abin da zuciyar ta take sak'amata, bata kula shi ba ta fara tafiya a wajen don bata da abin cewa tun da driven su ne d'auko shi suka yi yana musu aiki su biyashi dole yaji maganar shi tun da ita ba komai bace. Ganin tana tafiya yasa Sabeer bin bayan ta yasha gabanta yana cewa "Hey beauty kizo nayi dropping naki zuwa gida " Ja Suhaima tayi ta tsaya tare da d'an kallon shi gaban ta na fad'uwa ta daure tace "Bana so zan kai kaina inda nake buk'ata " Tana gama fad'i haka ta kauce tare da zagaye shi zata wuce da sauri ya rik'o hannun ta, tsayawa Suhaima tayi tare da jiyowa ta kalli tsintsiyar hannun ta inda ya rik'e mata wani bak'inciki ne ya kamata ganin namijin da ba mijin ta ba muharraminta ba ya rik'e mata hannu a cikin bayyanar jama'a, ko jiya ma da ya rik'e mata hannu ba cikin nutsuwar ta take ba. Wasu hawaye ne suka hau zubo mata a idanun ta kallon shi tayi tare da cewa "Ka cika ni " Muryar ta can k'asan mak'oshi ta furta hakan, ganin babu wasa a fuskar ta ya sanya shi cikata tana ganin haka yasa Suhaima juyawa zata cigaba da tafiya, cikin wata irin murya Sabeer yace

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});