Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 41

Chapter 41

A Sanadin Sonki Book 1 Complete Hausa Novel – A Story of Love, Sacrifice and Destiny 1,194 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

waje d'aya. Hannun shi ya sanya ya d'auke gashin da ya rufe mata face nata ya zuba mata ido musamman pink lips nata wanda ta d'an danne na k'asan kad'an da hak'orinta na k'asa ji yake kamar yayi ta kissing d'in su sai dai ba yanzu ba da sauran lokaci amman duk lokacin da ya mallake su sai ta gane kurenta sai ya ladaftar dasu ta tsiwar da suke mishi. "Baby open your eyes please " A hankali ta bud'e idanunta gabanta na cigaba da fad'uwa ta zube idanunta saman fuskar Sabeer wanda batasan lokacin da suka d'auki mintuna 2 tana kallon cikin idanun shi wanda daga k'arshe kasa jure kallonsu tayi sai kawai ta sunkuyar da kanta k'asa jikinta yayi sanyi wani irin abu ne yake fisgarta game da Sabeer amman tana kok'arin yaki ce shi don batason yayi mata tasiri akanta. "Baby mene aibuna da baki sona why Suhaima? " Shiru tayi babu amsa hannun shi ya sanya ya d'ago face nata cikin muryar shi da ta soma rawa tamkar wanda zai fashe da kuka yace "Saboda me baki sona ni d'an iska ne ko kuma ban cancanta a so ni ba? " Girgiza kanta tayi don bakinta yayi mata nauyi ta kasa magana. "Toh kina sona? " Nan ma ta girgiza kai, wani abu ne ya tokare wuyan Sabeer wanda ya sanya wasu hawaye fita daga idon shi. A hankali ya saki fuskarta jikin shi yayi sanyi sosai goge hawayen face nashi yayi tare da sakin murmishin yak'e yace "Ni kuma ina son ki kuma insha Allah zai kin zama tawa, ina son ki Baby " Yana gama fad'in haka ya juya ya tafi har yana cin tuntu6e da abu sauran kad'an ya fad'i saboda gaba d'aya ba'a hayyacin yake ba. Hankali Suhaima ya tashi da sauri ta ce "Sabeer kayi hankali kada kaji ciwo" D'an jiyowa yayi ya kalleta kafin ya juya ya bar gidan gaba d'aya zuciyar shi sam babu dad'i. Jikinta a sanyaye ta shige d'aki ta kwanta rub da ciki a saman bed wasu hawaye ne suka fara zuba a idanunta me yasa bata ta6a jin tausayin Sabeer irin na yau, me yasa ta fara jin wani yanayi game da Sabeer wanda bata ta6a jin irin shi ba, anya kuwa zuciyar ta bata fara son Sabeer ba kuwa?...... Aishat A Muh'd ✍🏻 [2/24, 9:00 PM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻: *A SANADIN SON KI* Written by Aishat A Muh'd Dedicated to my Sadeey SaNaz PAGE 57-58 Ta dad'e kwance a hakan don batasan iyakacin lokacin da ta d'auka ba jin dawowar su Yaya Aliyu taji daga hospital, nan ta tashi da sauri tana zira kaya tana mai mamakin dad'ewar da tayi don ma ta gama dukka ayyukanta, wani siket ta sanya pink colour mai turuwa sai T-shirt in black colour mai k'aramin hannu tana da tattara daga gaban rigar sai ta gyara gashin kanta tayi rolling da pink d'in veil kalar siket d'in batayi wani make-up ba daga powder da ta sanya sai lips gloss mai kamshin apple tayi kyau sosai duk da batayi kwalliya ba. Nan ta fito tsakar gidan babu kowa d'akin Aliyah ta wuce sai ta tarar da Babaa Lantana da Aliyu sai Sabeer a palour babyn na hannun Sabeer yana faman kallon shi addu'a yake cikin zuciyar shi Allah ya nuna mishi auren shi da Suhaima ta haifa mishi kyakkyawan babyn yanda yake shi d'aya yana rok'an Allah yasa ya haifi yara da yawa don bazai sassautawa Suhaima ba duk shekara yake son tana haifa mishi baby shi zaina yin zaman rainon su. Yana cikin wannan tunanin yaji sassanyar kamshin turaren ta sai da ya lumshe ido kafin ya bud'e su ya sauke su saman beautiful face d'in Suhaima sai akayi dace ita ma ta d'ago idanunta ta kalleshi nan suka fara kallon junan su, dakyar Suhaima ta iya controlling d'in kanta ta janye idanunta ta wuce ta samu ta zauna kusa da Aunty Aliyah, shima Sabeer d'auke idon nashi yayi yana wani shan kamshi ji yake tamkar ya lasheta don tayi mishi kyau. Duk wannan kallon da suke yiwa junan su Aliyah da Aliyu suna kallon su suna kyautata zaton Suhaima an fad'a tarkon Sabeer, wayar shi ya d'auko ya d'auki babyn pic's yana d'an yin hira da Babaa Lantana wadda yake zaune kusa da ita, sun jima a zaune a haka Suhaima tana son d'aukan babyn don bata ganshi ba gashi Sabeer yak'i ajiye shi gajiya tayi don haka cikin muryar shagwa6a tace "Wai ni Aunty Aliya baza'a ban na d'auki babyn ba ni fah tun da aka haife shi ban d'auke shi ba sosai " Rik'e ha6a Aliyah tayi tare da cewa "Ni zan hana ki d'auka ne ai gashi hannun mutumin na ki sai kije ki kar6a " D'an jim tayi kamar bazata je ba sai kuma ta kasa jurewa don haka sai ta mik'e a nutse ta nufi inda Sabeer yake zaune, kamar an tsikare shi ya mik'e tsaye da sauri ya mik'awa Babaa Lantana babyn tare da cewa "Nayi mantuwa Babaa rik'e minshi ina zuwa " Yana mik'a mata ya fice da sauri har yana mance wayar shi, baki sake Suhaima take bin shi da kallo tabbas akwai wani abin d'an ta6e bakinta tayi ko maye ruwanta ma, kar6ar babyn tayi ta rungume shi a jikinta k'aunar shi na ratsa cikin zuciyar ta. Wayar Sabeer ce take k'ara kira na biyu kenan da ake yi mishi gashi tun da ya fita bai dawo ba. "Suhaima ajiye babyn ki kai mishi wayar tunda bai dawo ba " Cewar Yaya Aliyu, Babaa Lantana ta mik'awa babyn ta mik'e tare da d'aukar phone d'in nashi ta fita daga parlorn, kallon phone d'in take sosai tayi mata kyau da gani mai tsada ce sosai bana kad'an ba. Bata ganshi a tsakar gida ba don haka tayi sallama d'akin shi sau uku ba'a amsa ba, sai kawai ta tura kanta cikin d'akin wayam bata ga Sabeer, abin ya d'aure mata kai ina ya shiga ne. Fitowa tayi ta duba don ta duba kofar gida tana lek'awa ta hango abin da ya kusan sumar da ita saboda tsanannin tashin hankali, tuni jikinta ya hau rawa zuciyar ta na bugawa da k'arfi nan da nan idanun ta suka rikid'a daga farare sol zuwa ja, ba komai ta hango ba sai Sabeer da yake zaune saman wani d'an reshen bishiya da ya karye ya fad'o k'asa sai ake zama a kanshi sai wata budurwa wadda bata gane fuskarta ba tasha uwar d'amara a kugunta a tsaye gaban Sabeer suna dariya hankalin su kwance ita kuma tana wani jan mayafi tana rufe fuskarta tamkar mai jin kunya. Shi kuma yana mata magana, tuni Suhaima taji wani mugun kishi ya tokareta wanda batasan tana da irin kishin nan ba, batasan lokacin da ta k'arasa inda suke ba ta tsaya ranta a mugun 6ace. Tun tahowar ta Sabeer ya hango ta yana kallonta ta gefen idon shi ganin yanda fuskarta ta koma yasa shi narke murya yana dad'a jan budurwar da hira wadda kasance k'anwa ce ga Ashiru. Ganin ta d'auki tsayin seconds a tsaye babu wanda ya kulata yasa taja wani mugun tsaki tamkar zata tsinke harshenta, da sauri suka jiyo suka kalleta. "Laaa

Table of Contents

Chapters

104 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});