Chapter 92
Chapter 92
taba tashiba kwata kwata. Zaman fada a ranar gabaki daya ya tsayawa yayi cak sbd Ayau duk Wanda yake masarautar ya sheda tareda tattabarda son Ayanah bai taba fita daga zuciyar sultanba duk tsawon wannan shekarun sbd al’amarim daya bayyana garesu na halinda take ciki da halin da suke iya hango wa qarara sultan ya shiga dukda ya boye hakan tareda danne wa amma a wasu lokutan sirrin zuciya idanuwa ne suke nunawa. Halinda ya bayyana daga idanuwan sultan dayake Neman tona zuciyarsa ya lalata sanyin zuciyar dasu HAILE ke samu ga wannan ciwon lokacin daya dayake Neman kawar musu da Ayanah a cikin sauki. Duk yanda likitoci ke kokarinsu sunyi sun samu daidaita numfashinta dake samuwa da taimakon oxygen amma bata farfado ba Wanda kuma a abida suka gani ba lallai ta iya farfadowa yanzu ba bare dawowa daidai hakama abu biyune zai faru idan ta farka shine zata iya dawowa daidai harma da tinaninta da memories dinta data rasa hakama zata iya tashi kuma ba lafiya ba ta rasa Sauran hankali da memoryn daya rage mata Wanda zata manya komai hatta dan data Haifa da sultan da duk Wanda ta taba sani a rayuwarta dan haka abinda sukafi buqata a yanzu shine kada ta farka kusa kusa hakan zai bawa qwaqwalwarta daman samun ishashen hutun da batai aikin komaiba dan haka tinaninta da nutsuwarta zata fi Saurin dawowa cif cif insha Allah sabanin ta tashi da wuri hakan zai iya harbawa cikin kwakwalwan ta buga gabaki daya dan haka zasu hada da nasu taimakon dazai saka bazata farfado ba sai Bayan kaman wata daya haka indai so samu ne. Wannan bayanin ya karya tareda jijjiga duk wani kuzari da zuciyar NUAB ALMAZZ yake dashi dan kuwa Amminsa duniyarsa ce idan har zata iya tashi ta manta wanene shi da girman kaunar datake tsakanin jininsa da nata zai iya rasa kansa a wannan duniyar. Gabaki daya duniyar su aleey suma sai data jijjiga da wannan bayanin na likitoci dan haka Kai tsaye Aleey ya buqaci tattaunawa a tsakanin nasu likitocin dake qasashe daban daban dasu Dr Amed Wanda suka tattauna tattaunawa me tsayi kafin suka fahimci komai anan doctors dinsu suka tabbatar musu da bayanin su Dr Amed din haka yake a yanda suka fahimci kowane bayanin yanayinta da results nata. Wannan tabbacin da suka samu daga nasu doctors din ya saka suka shiga sabuwar zazzafan yanayi suna jiran abinda Allah zaiyi a farfado wan nata. Su sakinah da tenya duniyar tayi musu tsananin quncin da babu kowace irin walwala a rayuwarsu dan haka suka duqufa fadawa Allah sbd dawowan hankalinta da tinanin wata sabuwar masifar ce a rayuwarta da kowane irin baqin cikin data dandana zai dawo mata sabo fil. Sultan tsananin tsaro ya qarawa bangaren Ayanah din hakama shima NUAB Zafafan securities dinsa mata sun iso daga Moscow sune ciki da wajen bangaren Wanda a yanzu Bayan tenya da sakinah sai likitanta Dr Amed babu me shiga dakin datake idan ba NUAB din. Sultan bai taba zuwa dubata ba al’adar dake kansa matsayin shugaba dan haka zuciyar NUAB take sake tsananta akansa. A bangare daya kuwa Wani tsananin bincike aleey yakeyi me gigitarwa Akan Neman Abaas Wanda NUAB yayi alkawarin Nemowa kafin watan nan daya da ake saka ran tashin Amminsa ya cika dan kuwa a yadda likitocin sa suka basa tabbacin indai aka samu abinda zuciyarta tafi tsananin so ko maitarsa fiyeda komai a memory dinta na baya aka gabatar mata dashi tana farfadowa to hakan zai iya tabbatarda tsayuwar hankalinta da memories dinta. Hakan ya saka Kai tsaye ya bada umarnin duk inda Abaas yake a duniya yanason aleey ya qure lissafin kwakwalwansa Akan inda zaa fara nemansa. Wannan ya saka qwaqwalwan Aleey budewa da kyau ya nutsu ya buqaci ganawa da Wanda yasan Abaas a duniya Bayan Ammin. Kai tsaye Sakinah ce wadda zata basa bayanan dayake so dan haka a lokacinda ya zauna a palon da zai tattauna da Maa sakina dagowa yayi a natse ya kalleta da idanuwansa masu sirkin blue blue na asalin baturen Russia ya bude baki Bayan ya dauki iPad din dake hannunsa dan dauka da tattara duka bayanan da zatai masa ya dago yana nutsar da duka hankalinsa akanta yace ‘Maa’ Kallansa tayi a natse itama batareda ta bude bakiba sbd nauyin da bakin yayi mata na rayuwarsu dake dawo mata, ‘Maa,waye Abaas?? Ina Abaas yake? Bata yayi ko guduwa yayi kokuma korarsa akai? Idan bata yayi daga ina ya bata? Idan guduwa yayi daga ina ne ya gudun? Idan korarsa akai waye ya koresa,me yayi aka koresa? Meye cikakkiyar alaqar Abaas da Ammi? Shekara nawa yanzu da rabuwan Ammi da Abaas?’ Numfashi me nutsuwa ya sauke yana kallan Maa din Wadda idanuwanta sukai jajir ya sake tausasa muryansa yace ‘Maa,Maa duka wannan bayanan shine zai bani daman dawo da Abaas rayuwarku, Da wannan bayanin da zaki mun Maa nayi miki alkawarin Nemo Abaas matiqar yana raye insha Allah dan haka kowane bayaninki Maa ki sani yanada mahimmanci da rawar dazai taka a wannan aikin.’ Numfashi me Zafi da wasu hawaye masu Zafin gaske suka gangarowa Maa sakinah wadda Bayan shekaru masu tarin Yawa Ayau NUAB kila zaiji tarihin mahaifiyarsa da bai taba saniba mai daci da rashin dadin ji. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 61 A hankali cikin tsananin sanyi da mutuwar jikin radadin dayake dawo mata da quncin da harsu mutu bazasu manya dashi ba Maa sakinah tace ‘ABAAS GHAZ shine ‘da na karshe a jinin sarautar GHAZ data shafe a duniya gabaki daya yanzu, Shekaru masu yawan gaske ne da bazan tinaba suka Baro mu da asalin ANJOM GHAZ wato garin da mahaifin Abaas yake mulki, Abaas da Ayanah uwa daya uba daye suke tareda yan uwansu biyu da duka iyaye daya ne suka haifesu, AYANAH GHAZ itace babba sai ZUHRAH GHAZ sai NURAT GHAZ kafin ABAAS GHAZ…….. Ahankali tafara basa mummunan labarin rayuwarsu dayake cikeda baqin cikin da bai taba gogewa ba daga zuciyoyinsu,baqin cikin da dashi zasu mutu,baqin cikin da shine ya kawar da lafiyar kwakwalwa da gangar jikin Ayanaah,baqin cikin da shine zai zama abinda zasu mutu dashi,baqin cikin da har zuriar Bayan baya tasu Ayanah zasuyi baqin cikin jinsa har cikin jininsu,baqin cikin da a yanzu shine yake Neman raba Ayanah da rayuwarta…. Wani irin kuka takeyi mara sautin daya saka aleey daukan tissue ya miqa mata idanuwansa jajir hannuwansa na rawa zuciyarsa kaman zata fado hakama hawaye ne masu Zafin gaske suke Neman cikowa idanuwansa yanajin komai cikin zuciya da kirjinsa, Babban abinda yake sake saka jikinsa rawa shine yanda wannan mummunan tarihin zai isa kunnuwan LEUL, Yaya tarihin nan zai isa ga zuciyar datake shirye da mutuwa Akan wadda wannan mummunan tarihin yayi kaca kaca da rayuwarta? Tayaya zuciyarsa zata riski wannan tarihin kaddarar dayake dabaibaiye da rayuwar Amminsa. Numfashi Aleey ya sake saukewa yana kallan Maa yayi mata alkawarin zai Nemo Abaas a cikin qanqanin lokaci insha Allah hakama wannan tarihin LEUL ba a bakin kowa zaiji Saba insha Allah Sai a bakin Abaas da kansa. Ficewa Aleey yayi daga palon yana danna iPad dinsa sbd
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106