Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 83

Chapter 83

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Dora ASIM ALMAZZ a mulkin BOYEM yanzu kuma wannan ya dawo zai rikitar musu da tinani da raayin sultan dan haka suke cikin baqin ciki me tsanani amma Bayan hakan Sam sunsan tako ina babu inda zai kamo kafar ASIM a komai dan haka sukai shiru cikin takaici da baqin ciki, ASIM ALMAZZ dayake Zaune a kujeran datake ta Mutum daya idanuwansa a dan rufe yayi shiru da zurfafa a tinani bude idanuwansa yayi ahankali ya sauke Akan mahaifiyarsa kafin ya bude Baki cikin tasa Izzar da Wani irin yanayin dayake ji a ransa na babu Wanda ya isa ya rabasa da matsayinsa dayake Kai da Wanda yakeso a duniyar nan batareda ta aikasa inda ya kamacesa ba yace ‘Mamee babu abinda zai faru ki kwantar da hankalinki kokarinki na shekaru bazai taba tafiya a banza ba zan tabbatarda da hakan, Indai ba nine magajin karagar mulkin BOYEM ba to tabbas BOYEM zata rasa magaji da sultan din da zata kira nata, Kawai dai a yanzu ku Bari wannan dan gudun hijirar daya dawo ya gama abinda ya kawosa ya tattara mistress din mahaifinsa ya qara gaba da ita zuwa yawon bin yan taaddan da akace yanayi.’ Karban zancen HAILE tayi cikin wani irin radadin zuciya da cewa ‘Banda rashin tinani irin na Ubansa da tsufan dayake cinye kwakwalwansa tayaya zaiyi tinanin ma sauya Ka daga zama mai mulkin BOYEM Akan Wanda yagamo yawon duniya da taaddanci’ Numfashi meryam kawai ta iya saukewa me zafi tana fatar koma menene kowa zeyi yayi itadai buqatarta ASIM ALMAZZ ya zamo me mulkin BOYEM ya dauke hukuncin dayake kansu ta auri koma Wanene zata samu. Aslam kuwa can qasar zuciyarta Wani irin tsoro da fargaba takeji Wanda yake hanata cewa komai dan kuwa koma yayane dawowansa su dai ba alkhairi ce a garesu ba, ASIM ma a qasan zuciyarsa wata shakka ce ke son shigarsa da matsuwa da son haduwa da NUAB ALMAZZ dan yaga menene yake dashi a yanzu sannan ya sheda cewa shi ASIM ALMAZZ yanzu ya fisa komai musamman ilimin daya samu cikakke me kyau Wanda ko hakan zai saka a basa mulkin shi a hana masa dan babu ta yanda dan taadda zaiyi mulkin BOYEM baa taba ba kuma bazaa taba farawa ba. HAILE ma kusan bazasu taba gane abinda take ji a zuciyarta ba sbd har abada indai NUAB ALMAZZ yana raye batajin akwai ‘dan da sultan zai so kamarsa duk da baya tareda NUAB din shekara da shekaru amma hakanan take Jin bai taba Dena sonsa ba kawai abinda ya sakata kwantar da hankalinta shine koda yana sonsa baya tareda shi yana tareda ‘danta ne kuma gaggawar datake yi shine a Dora ASIM kafin ranar dawowan NUAB tayi gashi yanzu ya dawo batareda burinta ya cika ba dan haka yanzu sabon yaqi ne garesu su dukansu Akan tabbatarda burinsu ya cika kota halin yaya. *****Se karfe goma da mintina ya Baro bangaren Amminsa Bayan yaci abinci tareda ita cikeda kwanciyan hankali sun samu kasancewa da juna yanda yakeso tukuna ya fito ya fice. Lafiyayyan gyaran da akaiwa bangarensa ya saka yana zuwa Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa Wanda yake da Wani palon hutawansa a ciki kafin asalin bedroom din. A jikin bangaren nasa akwai manyan bedrooms guda biyu da sukeda girma sosai da toilets a ciki anan Yaransa suka sauka aleey kuwa bedroom daya dayake cikin bangaren nasa ya sauka dan haka dukkaninsu shigewa sukai sbd lokacin hutun LEUL ne. Wanka yayi da dukkanin abinda ya saba amfani dashi sbd babu abinda yake amfani dasu da aleey bai siyo ba baa. Dogon wandon bacci na lebarto ya saka mai wani irin santsi da Laushi sbd tsadarsa sai farar rigar wandon Kwantawa yayi ransa da ruhinsa cikeda nutsuwa take baccin hutun dayake buqata ya daukesa. Gabaki daya bangaren da zagayensa tsit yayi sbd Yaransa da suka tabbatarda hutawa yakeyi babu kowace hayaniya da ake buqata. Daga shi har Yaransa Hutu sukeyi Bayan an bada cikakkiyar umarnin kada Wanda ya tinkaro bangaren. Acan fada kuwa kowa ya cika duk wani babban masarautar yana cikin fada Zaune, Hakama duk Wanda yake gari ko qasar datake kusa da BOYEM indai jinin BOYEM ne sun iso suna cikin masarautar wadda ta dauki dumi dan kuwa a cike take da masu fada a ji na mulkin BOYEM, Shi kansa sultan Bayan dogon lokaci daya dauka kafin fitowansa ya fito daga karshe Bayan kowa ya gama Halarta kenan shi kadai ake jira da LEUL din Wanda baima San mesuke yiba, Zaman fada da meeting din zafi ya fara dauka Wanda ya saka sultan yake sake jin baiyi danasanin aika dansa ba harma ya zama koma menene ya zama yanzu din dan kuwa a bayyane wata irin zazzafar qiyayya ce yake gani tako ina a idanuwa da kalaman duk Wanda yake fadar Akan sai hukunci yahau kan duk Wanda ya taka dokar Masarautar BOYEM koma wanene. Sultan da abu dayane yake cikin zuciyarsa yana Juyawa shine rashin zuwan NUAB din garesa Bayan shigowa sa masarautar da shine yake mulki da ikonta hakama shine uban daya haifesa komai Zafin kansa da ikonsa wainda a gurinsa cikin jininsa ya gajesu, Dagowa yayi ya kalli taron manyan qasar BOYEM din gabaki dayanta da idanuwansa da tsananin zallar mulki da ikon dayake jininsa yana bayyana, Umarnin suke jiran ji dan haka akai tsit Ana kallansa tareda jiran abinda zai fada kowa zuciyarsa har rawa takeyi sbd jiran umarnin da sultan din zai bada. ASIM da idanunwansa sukai jajir zuciyarsa har wani fizga takeyi ya kafe sultan din da ido yaja baza kunnuwansa jiran abinda zaa fada, Bude bakin sultan umarnin kiran LEUL BOYEM ya bada tareda tabbatarda umarni ne me karfin gaske. Dan aike Koda ya isa tin daga nesa ya zube qasa bakin kofar bangaren yana daga muryansa ya isar da sakon cikin tsananin girmamawa. Dukkanin sakonsa a kunnuwan Yaransa ya isa amma babu Wanda yakeda niyar isar da sakon sbd lokacin gurinsa bai qareba dan haka manzon sakon yana zube a qasa bai tashi ba sbd Sai an amsa masa sakon zai tashi koda kuwa zai kwana ya wuni a hakan. Shiru shiru ba dan sako Wanda ya saka fadar sake daukan zafi babu Wanda ya iya cewa komai sedai xukata sun dauki Zafi. Awa kusan biyu manzon sakon ya shafe a durqushe cikin rana kafin me BOYEM din ya tashi baccin sa Kai tsaye ya shiga toilet yayi wanka ya bata lokaci sosai kafin ya fito daure da towel fari qal daidai nan wani manzon sakon ya sake isowa sedai wannan Karan bayi biyu ne daga bangaren mahaifiyarsa aka turo Wanda hakan ya sakasa Dakatawa cak daga abinda yakeyi sbd bayin saida suka gabatar da kansu suka isar da sakon ya kuma San me ake nufi da aiko bayin mahaifiyarsa Wanda take zuciyarsa ta fidda Wani irin Numfashi me dumi ya ajiye towel din dayake hannunsa na goge Kai ya juyo ahankali cikin isa da wata irin izza ya nufo kofa ya fito. Aleey dayake palo a tsaye yana jiran fitowansa yana ganin fitowansa da towel take ya dauko sunglasses na Versace ya miqa masa hannu kadai ya saka ya karba yana nufar kofa Kai tsaye wadda tini aka wangale masa ita, Yana fitowa umbrella

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});