Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

baiwa Bayan tana ganin yanda imebētis ke qasqantarciyar mutuwa ta rashin mahimmanci kuma sun mutu kenan a banza a wofi babu me sake tinasu sai ‘yaya idan sun haifa, Wani irin nauyi kirjinta yayi lokacinda tenya tace ta korawo ayanah tanajin gabobin jikinta na sanyi idanuwanta na cikowa da hawayen fatar ba abinda ake tinanin bane, Dakin Ayanah din ta nufa ta taddata kwance ba bacci takeyiba amma idanuwanta a rufe suke tayi shiru lafe a lallausan gadon zuciyarta a narke da damuwan data zamar mata jiki, Zuba mata ido sakinah tayi tana qure kallanta akanta zuciyarta na sake shiga matsanancin tsoro da tausayi me karfin daya saka hawayen idonta fara gangarowa ta saka hannu ahankali ta shafe hawayen tana kallan sauyi sosai dayake bayyane a jikin Ayanaah din. Ayanaah din ce ta bude idanuwanta masu haske ahankali kan sakinar sbd taji shigowanta hakama tanajin idanuwanta akanta dan haka a sanyaye ta bude ido ta saukewa sakinar batareda tace komai ba. Itama sakinar qasa tayi da kanta sbd bazata iya cigaba da kallan Ayanaah ba zata iya fasa kukan dayake cizon zuciyarta, Numfashi mara sauti ta sauke ahankali tareda bude Baki a natse da sanyi ta sanar da ita kiran tenya. Tana fada ta juya ahankali ta fice daga dakin sbd kallan da Ayanah ke mata na karaya da rayuwa koyaushe. Sai datai mintina biyu a kwancen tana kallan kofar da sakinah ta fice kafin ta tashi Zaune a hankali tareda ziro kafafunta qasa ta miqe tsaye slippers masu taushi a kafarta ta nufo kofar ta fito sanye da doguwar rigar qasar me kyau black kanta rufe da qaramin Gyale me hade da niqap din dayake da adon sarka me rawa ta zinari sbd tasan da zaa kawo masu dubata sbd zazzabinta amma bata San abinda zasuyi Bayan hakan ba kuma doka ce me karfin gaske babu namijin dazai iya ganin fuskarta tinda ta zama imebētin sultan me BOYEM gaba daya. Ko data sako Kai a palon Qamshinta ne ya fara cike palon kafin fitowanta data saka likitocin biyu dauke kansu gaba daya daga kallan hanyar datake tahowar, Tenya ce take kallanta su sakinah ma gabaki dayansu ficewa sukai kansu a qasa zuwa kitchen ayyukansu, Sakinah hankalinta gabaki daya kwata kwata yana kan abinda zai faru a palon tana tsananta adduar Allah yasa Ayanah bata dauke da jinin boyem a cikinta, Cikin nutsuwa likitocin suka nutsu suka gudanar da bincikensu Akan Ayanah wadda dukkanin tambayoyinsu ta amsa a sanyaye. Bayan dan lokaci suna bincike da bin harbawan jijiyanta suka bar bangaren dan tafiya da sample dinta da zaa auna dan tabbatarwa kafin bude baki ga fadar kowane irin sakamako ne. Ayanah bata buqatan sanin menene yake damunta sbd ba damuwanta bane ta rayu ko sabanin hakan, Tenya kuwa Miqewa tayi itama ta fice ta aika aka saka mata ido sosai a cikin sirrin dan tsaro da kiyayewa batason kowa ma yasan da duk abinda zaa fada. Jiran wuni guda tenya tayi tana jiran sakamakon Wanda ya hanata dukannin sukuni da nutsuwan zuciya hankalinta na kan koma menene, Daga qarshe tenya da kanta ta isa bangaren lafiyyyar clinic din dake cikin masarautar, Sai dare ta isa batareda barin kowa yasan da inda ta nufo din ba sbd tasan sosai akwai Idon HAILE Akan duk wani motsinta da abinda ya shafi Ayanah. Ko data iso Kai tsaye babban likitan ne da kansa ne ya zauna suna fuskantar juna ya sauke Numfashi ya koro mata bayani Kai tsaye ciki ne da Ayanaah qarami. Ajiyan zuciya da Numfashi mai karfi tenya ta sauke tareda kallan likitan Wanda ta ciro silan danyan zinari ta ajiye gabansa matsayin tukuicin zancen sa ta miqe ta juya ta fice tana Jin yanayi na farin ciki da samun nutsuwa dan Kuwa adduarta a yanzu zata sauya zuwa Allah yasa wannan Karan haihuwan LEUL BOYEM ne tazo mai albarka dazai zamo abin alharinta da uwarsa dan kuwa shine karshen baqin ciki da haukar da zata Kama HAILE dan samun namiji a gurin wata macen da ba ita ba yana nufin zarewanta. Koda tenya ta isa babu Wanda ta sanarwa da maganar cikin imebēti Ayanaah sbd fitar zancen cikin tamkar miqa rayuwar Ayanah ce ga halaka dan haka ta zabi tayi shiru ta Hana kowa sanin cikin saiya bayyana. Sakinah Jin shiru kwana daya kwana biyu harma kwanaki babu sakon labarin samun ciki ga Ayanaah ya sakata Jin dan sassaucin abinda take ji na tsoro da tashin hankali ta dan kwantar da hankalinta duk da kullum sake sauyawa Ayanah ke yi alaman mace me ciki yana sake bayyana gareta batareda itama tasan cikin ne yake dauke dashi ba. A haka satikan hutunta suka cika aka fara shirin fara zuwanta tiraka sedai wannan Karan tenya bata bada umarnin anyi mata shiri me karfi ba Wanda hakan ya tado tsoron sakinah sedai kuma indai har cikin ne da Ayanah dole Ayau zasu sani kuka kowa ma dake masarautar zai gane dan bazata qara zuwa ba, A al’adance duk macen data samu cikin sultan matiqar an tabbatar tenya ce takeda ikon sanar masa idan takai mace kwanan karshe shi kuma daga wannan ranar zai sallamota ne ta hanyar alamar rashin bata tukuicin kwanciya Wanda hakan na nufin ya gama da ita kenan shikenan kota haihu kawai matsayinta dayane ta haifar masa jininsa, To wannan alamar ce take sakawa kowa dake masarautar yake sanin mace ta samu ciki sai kuma Bayan lokaci nai dan tsayi kafin a fara shirin zabar masa wasu imebēti din, Tenya duk wani shiri na nutsuwa da qamshi me sanyi na bankwana da tirakar sultan shi tayiwa Ayanah tanajin damuwan sanin cikin da zuwa yanzu kowa zaiyi, Karfe goma sha Dayan dare suka iso tirakar tasa wadda kowannensu ya tsaya cak inda shine gurin tsayuwarsu, Silan zinari dayake da adon hoton tafin kafar jariri a jiki tenya ta bude hannun Ayanah ta saka mata batareda cewa komaiba, Wucewa ciki Ayanah tayi batareda ta bude hannunta ba bare tasan sakon menene amma dai sanin yawancin sakon masarautar da alama a silan zinari suke Aikasa dan haka a sanyaye ta isa dakin Wanda yayi sanyi sosai qamshin sa datai sati uku bata shaqa ba yayi shiga hancinta yana ratsa kanta cikin sanyi ta dan Lumshe idanuwanta t bude a natse kafin ta fara Takawa da sanyinta sautin karar sarkar kafarta dayake daban dana matansa yana tashi a kowane takunta yana shiga kunnensa da sautin yakewa dadi, Isowa tayi har inda yake Zaune sanye da Riga da wando masu dan kauri farare qal d suka sakasa komawa tamkar matashin saurayi, Kanta na qasa ta zube qasa ta miqa masa gaisuwanta da muryanta da babu hayaniya a cikinta ko kadan, Amsa gaisuwar yayi yana kasa dauke idanuwansa daga kanta dan kuwa zuwa yanzu ya gama yadda da koma menene Ayanah na basa nutsuwa da sukuni fiyeda kowa dan kuwa ko yayansa baida Wanda zaice gashinan shine yafi so ko ji a zuciya, Bayan kujeran mulkin BOYEM yanajin a yanzu ne ya sake samun abinda bazai taba iya bawa wani ko barin yafita hannunsa dan Hak……. Bai qarasa abinda yake zuciyarsa ba ta dago hannuwanta biyu sama kadan ta bude masa su sakon na bayyana kan idanuwansa kanta na qasa. Qurawa tafin hannun nata ido yayi

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});