Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da zai kalleta bata fizgi hankalinsa ba dan haka yake killace dukkanin wata al’aurarsu sam baya barin ko yatsar hannuwansu wani na waje na gani sbd a sujjarsa gabaki daya adduar ‘yayansa ne. Ahankali jikinsa na mutuwa ya daga hannunsa ya miqa akan Zuhrah ya fara tattare gashinta cikin kulawa ya daure mata yana janye mayafinta me ado dayake gefenta ajiye ya rufe gashin nata. #MAMUH #GHAZ #KUSRAH #BOYEM #ROYALTY #BEST LOVE HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070 5 Dago Kai Zuhrah tayi ta kalli Abaa din tana Dora hannunta akanta ta taba mayafin daya rufe kanta dashi tana zubawa mahaifinta ido ta bude baki zatai magana ya Dora hannunsa daya akan bakinta ya girgiza mata Kai ya bude baki yace ‘Kanki ya kasance koda Yaushe a rufe Zuhrah ghaz’ Gyada kanta tayi batareda ta dauke idanuwanta daga Kansa ba sbd ganin wani irin kallan tsananin kaunar dayake mata. Tsakiyar kanta ya sumbata yace ‘Albarkar Allah ta tabbata a rayuwanki Zuhrah koda yan uwanki duka’ ‘Amin Abaa’ ta fada tana matsowa sosai jikinsa ta zauna. Nurat ya maida idanuwansa ya kalla wadda take jikinta yayi sanyi sbd itace tafi kowa saurin kamuwa da yanayin da duk ya sauya, Ta fisu saurin hawaye da zama emotional sbd tanada qawazuci sosai na iyayensu dan haka hannunsa ya miqa mata ta taso daga gefen Abaas ta dawo gefensa ta kallesa idanuwanta na raurau haka kawai. Wani murmushi me sanyi da kyau ya dake yana Shafa fuskanta ya girgiza mata Kai yace ‘Jarumar ‘yata Nurat bata barin jikinta yayi sanyi a kowane yanayi’ Murmushi ta sake tana Kama hannunsa qamqam tace ‘Abaa ina fatan na kasance hakan daka fada koba yanzu ba’ ‘Insha Allah Nurat zaki zama jajirtacciya dakakkiya bazaki taba gazawaba insha Allah’ Maganarsa ta saka Ammansu kallansa tana dan murmushi batareda tace komaiba. Qarasa fitar da wunin sukai cikin tsananin kaunar dasuke Jin tafi ta koyaushe musamman da mahaifinsu yaketa yabonsu yana kasa dauke kallansa akansu cikeda kauna hakama Amma Jin takeyi tana sake kaunar mijinta sbd yanda ya tarbiyantar da ita da yayansu. Da daddare Bayan sunyi sallah ishai Abinci da Kayan marmari aka kawo aka Jere musu tareda fitilun wutar ishen flower masu sanyin kamshi da aka kewaye gurin dasu suna basu haske tareda kamshi. Dagowa GHAZ yayi ya kalli sakina baiwar Ayanah dake gefensa ya bude baki yace ‘Ina Asamah gabaki daya yau ban ganta ba’ Sunkuyar da Kai sakina tayi cikin girmamawa ta bude baki tace ‘Tin jiya bata fito ba babu Wanda ya ganta a yau sbd damuwan abinda ya faru da GHAZ Abaas’ Kallan Amma GHAZ yayi yana Neman qarin bayanin hakan Kallansa tayi itama cikin kwantar masa da hankali tace ‘Tashiga damuwa sosai ne har dare jiya tana gurina tana kukan Neman Gafara da Afuwan abinda ya faru dan hakanne yau Kowa ya kyaleta ta dawo daidai’ Shiru yayi sbd bayason nuna damuwa ko fada a cikin iyalansa dan haka baice komaiba sbd duk tsawon shekarun nan bai taba dauke saka Idonsa da saka taka tsantsan sosai akan Asamah ba dan haka tin jiyan da jinin Abaas ya fita yake Jin rashin nutsuwa amma baya iya nunawa sbd yanzu suna cikin wani hali ne na kusrawa dake Neman kawo musu hari kowane lokaci suka samu damar hakan. Abinci suka ci suna fira da nishadinsu har suka gama nanma suka ci gaba da firarsu har dare sosai kafin Abaa da Kansa ya raka kowacensu dakinta da Kansa kafin ya dawo ya tafi da Amma dakinsu itama tukuna ya fito ya dawo dakin Abaas sosai kafin ya fito ya shige shima. Tsakiyar dare sosai Nurat dake kwance taba bacci cikin kwanciyan hankali da nutsuwa ta farka da karfi cikin mummunan faduwan gaba sbd mummunan mafarkin datai. Bude idanuwanta tayi ahankali tana sauke ajiyan zuciya a sanyaye kafin ta tashi Zaune tana Jin rashin nutsuwa, Shiru tayi tana Dora hannunta kan kirjinta dake bugawa sosai cikin rashin Jin dadi, Koma wa tayi ahankali tana kokarin kwanciya taji motsi me karfi daga waje dan haka gabanta ya sake faduwa ta zuro kafafunta qasa da sauri tana saukowa gadon tareda daukan mayafi tana Daurawa akanta ta nufo kofa tana bude kofar ta fito Kai tsaye batareda tsoron duhun Daren ba. Takawa tayi Kai tsaye ta nufi dakin Ayanah sedai kafin ta isa dakin wani irin jan haske taga yana gauraye saman garin na alamar wuta. Saman ta ringa kalla tana nufar dakin sai kuma hayaniyar tashin qara daga nesa Wanda ya sakata qarasawa dakin da sauri tanajin tsoro na shigarta. Tura dakin tayi ta shiga da sauri ta qarasa gadon Ayanah ta haye gadon tana shigewa jikinta ta qanqameta. Cikin bacci Ayanah taji Nurat cikin jikinta wadda tasan itace Kai tsaye sbd itace Kai tsaye take zuwa lokuta da dama cikin dare gurinta idan ta kasa bacci. Numfashi da ajiyan zuciya Ayanah ta sauke tana Shafa kan Nurat din sedai kafin ta bude baki tayi magana aka sake turo dakin cikin wani irin sauri da karfi. A tare suka miqe Zaune cikin faduwan gaba da mamaki, ‘Abaa’ Ayanah ta Ambaci sunan mahaifinsu dake shigowa da qaramin hasken wuta a hannunsa. Nurat ma cikin fargaba tace ‘Abaa’ Qarasowa yayi da sauri batareda ya amsa su ba Amma na gefensa da hasken itama jikinta na tsananin rawan mummunan tashin hankalin da basu taba samun kansu a ciki ba tsawon tarihin GHAZ. Riga me tsananin kauri ya janyo a cikin Kayan Ayanah ya miqa mata cikin kokarin hana mummunan tashin hankalinsa fita sbd kada su firgita yace ‘Saka wannan Ayanah’ Karba tayi hannuwanta na dan rawa tana sakawa akan kayanta tace ‘Abaa meya faru ne?’ Bai amsata ba ya janyo wata rigar ya saka a hannun Nurat dake sake shiga rikici idanuwanta na raurau Amma ce ta taimakawa Nurat din gurin saka rigar Abaa ya Kama hannunsu su biyun ya nufo kofa dasu wannan Karan Amma ce riqe da hasken gaba daya. Dakin Zuhrah suka isa wadda take bacci sosai hankali kwance Cak Abaa ya tadata Zaune Wanda ya sakata bude ido tana sake lumshewa zata zame ta sake komawa kwance ya miqar da ita gabaki daya yana cewa ‘Ayanah samo mata Riga me nauyi sbd sanyi’ Da sauri Ayanah ta nufi Kayan Zuhrah din ta dauko Riga da sauri ta kawo tana miqa masa Da Kansa ya sakawa Zuhrah din yana Kama hannunta itama suka fito. Dakin Abaas suke kokarin nufa wani irin kuka da Ihun mutane mara dadin saurare ya sake tsananta yana gauraye garin tareda qaruwar hasken wutar dake cin garin sosai. Sai a lokacin bacci gabaki daya ya sake su Ayanah suka shiga tsoro da faduwan gaba me tsanani suna kasa ma tambayan meya ke faruwa. Abaas ma baccin yake Ayanah ce tayi saurin isa gurinsa ta tadashi da sauri dukkanin jikinta na rawa. Fitowa sukai Abaa yaja su zuwa kofar baya ta fita gidan ya tura su wani daki tareda dukkanin bayin gidan mata ya kalli Amma batareda yace komaiba ya qanqame hannunta ya kalli Ayanah itama yace ‘Ku kula karku fito saina dawo Idan kuma kunji shiru ban dawoba ku fita ta baya akwai hanyar dana

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});