Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 105

Chapter 105

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rai da rayuwarta tareda bata kariya da dukkanin kauna da kulawan tareda tattalin data rasa tin tasowanta, Insha Allah indai kulawa da nuna kauna da soyayya me tsanani sune suke kawo haske a rayuwar datake cikin duhun kadaici to tabbas zata cikewa Bahar duhun rayuwarta da haske koda kuwa zasu qare a cikin wannan sirrin su mutu matiqar hakan na nufin kariya da samun tsaronta. Numfashi ta sauke ahankali me sanyi da mutuwar jiki tana tina rayuwarsu ta baya da yanda suka Baro ANJOM GHAZ da kuruciyarsu dukkaninsu amma ayau gasu sun manyanta wasu sun rasu sun bar duniya wasu kuma basa tareda su ita kuma gatanan ayau da ‘yar Abaas a hannunta batareda dukansu sunsan hakan kaddara ta tanadar musu ba. Wasu hawaye ne suka ciko idanuwanta tana kallan tata rayuwar da babu komai a cikinta face kaunar jinin GHAZ da bauta musu har qarshen tata rayuwar da batasan Yaushe ne ba amma koma Yaushe ne tana fatar Allah ya dauki rayuwarta itama a cikin aminci da kauna. Shafa fuskar BAHAR data rufe jajayen idanuwanta a hankali tayi tanajin kaunar Bahar din na sake ratsata sbd rayuwarsu a wannan matakin da suke kai yanzu iri daya ce, kaddararsu iri daya ce, Basuda uwa basuda uba basuda Wanda kai tsaye zasu kira nasu Bayan Ayanah dake kwance basu San yaya tata kaddarar zata kasance ba sai NUAB Wanda ayau idan ya rasa Amminsa kila shikenan yabar BOYEM da duk Wanda yake cikinta har abada su kuwa kila duniyar zasu bi sbd rashin Ayanah a BOYEM zamansu a BOYEM din ya qare sbd ita sakinah ba baiwa bace a yanzu hakama Bahar din duk da a yanzu basuda zabin daya wuce a shiga da ita masarautar a matsayin baiwa tinda babu Wanda yasan ita wace ce hakama babu damar fadar ita din waye Wanda sakinah batada zabin daya wuce ta tafi da ita a baiwa matiqar tanason kasancewa da ita batareda Ayanah tasan komai Akanta ba bare mutuwar Abaas. Tausayin Bahar din ya sake cike zuciyarta sbd batasan tayaya zata fara fuskantar rayuwar da zasu tarar din a BOYEM ba musamman da suke ba kowa ba basuda kowane karfin kansu, Hannun Bahar din na hagu dayake ajiye Akan kafafunta ta zubawa ido Akan lambar 99 dake zane a hannunta Baro Baro tayi baqi sosai Akan farin hannunta daya keda fari sosai sbd zamanta bata Baro komai na mahaifiyarta ba, Wasu hawaye masu tsananin zafi ne suka gangaro daga idanuwan sakinah dake Haba kukanta zuwa sbd da wuta aka rubuta lambar 99 din wadda take lambar Abaas ta Shedan zama cikakken bawa da kusrawa sukai musu, Lambar mahaifinta Abaas ce a jikinta zeti da inda akai masa tasa shima a gefen hannu daga sama gurin gwiwan hannun, Rufe baki da hannunta daya sakinah tayi tana kukanta bayyana sbd Bahar dake shiru a jikinta, Nata hannun ta kalla inda tata lambar take Baro Baro a jiki 96, Zuhrah ce 97 sai Nurat 98 tukuna Abaas dinne 99 Ayanaah 100 Wanda haka akai musu su a Jere babu Wanda a cikinsu haryanzu wannan lambar bata jikinsa Wanda da ita zasu mutu, NUAAB tin da ya tashi yaga mahaifiyarsa da wannan lambar a jikinta da hannunsa ya zanawa Kansa lambar a jikinsa da wuta sbd itace lambar dazai tabbatarwa Abaas shi din ‘dan Ayanah ne dan haka da lambar mahaifiyarsa ya tashi a jikinsa bata taba dauka Abaas shima yayiwa tasa yar lambar sa ba sbd koda baya raye da lambar sa zasu yadda da Bahar ‘yarsa ce. Kuka sosai Maa sakinah din tafasa tana kasa riqe kanta sbd har abada sunyi rashin da bazasu taba manta radadin sa ba, Sunyi rashin da shine mafi ciwon rashin da sukai a baya Bayan nan. BAHAR dake kwance shiru zuciyarta bata iya komai Bayan bugawa ahankali sbd komai ya tsaya mata cak tana jin sautin kukan Maa sakinah yana shiga kunnuwanta a hankali yana ratsata sbd tasan kukan rashin Abaa dinta ne akeyi. Bude idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga cikinsu a sanyaye tana sake Numfashi me sanyi Mara sauti batareda ta motsa daga kwancen datake a jikin matar da bata taba saniba a zahiri Sai a tarihi amma ayanzu da ita kadai zatai rayuwa. Tafiyar kusan wuni guda sukai kafin jirginsu ya sauka a qasar BOYEM suka fito tareda securities din NUAB din duka da aka hado su dasu shikuma daga shi sai aleey suka koma. Motocin alfarmar GHAZ ne suka daukesu daga airport zuwa Masarautar BOYEM me tarin abubuwa da tarihi dama Wani tarihin da zaa kafa. Ko a cikin mota hannun BAHAR din yana cikin na Maa ta riqe cikin nata tana bata dumin dazai Haba gangar jikinta qarasa rasa kanta. Duk duniya da Aljannar duniyar dake tin daga babbar gate din farko ta masarautar bai shiga idanuwan Bahar ba bare zuciyarta sbd komai na rayuwarta a yanzu rufe yake gap babu kowane irin Sauran shaawa ko burgewa a rayuwa da zai shigeta dan haka idanuwanta a kafe suke kawai a waje tana kallan wajen amma kwata kwata tinaninta baya jikinta ko daya tayi nisa a tinanin rayuwar datai a baya da mahaifinta Wanda a yanzu yana kwance cikin qasa, Tafiya sukai suka sake wuce gate na biyu har zuwa gate na uku suka shige akai parking motocin bakin hanyar da zata kaisu bangaren cikin gida kai tsaye aka bude musu motocin dukansu su biyun a lokaci daya. Maa ce ta fara fitowa a natse cikin sanyin jiki ta sauke ajiyan zuciya da Numfashi kafin ta zagayo ta miqa hannu cikin motar ta Kama hannun BAHAR wadda bata motsaba tinda aka bude mata motar ta janyota a hankali cikin kulawa ta fito motar, batareda ta saki hannunta ba ta jata a natse zuwa ciki suna tafiya babu me karfin jiki. Duk Taku daya da Bahar ke yi Wani siririn sautin sarkar kafarta ta mahaifiyarta data gada ne yake tashi tareda Wani irin sakar da nutsuwa da saka son juyowa ga duk Wanda sautin ya shiga kunnensa dan hakane duk tayi Taku daya bayin dake jere a hanyar sai sun sauke kansu qasa cikeda girmamawa ga Maa sakinah wadda kowa yasan matsayinta na shaqiqiyar Wishmah kuma jakadiyar bangaren wishmah ta biyu. Kai tsaye hanyar bangarensu Maa ta nufa da BAHAR wadda har lokacin duk inda Maa ta jata saka kafa kawai takeyi ba Wani kuzari a jikinta. Isowarsu gap da hanyar data raba bangaren Queen HAILE da bangaren Wishmah Ayanah a daidai wannan lokacin Li’uli ASIM ALMAZZ ya fito bangaren mahaifiyarsa cikin shigar sky blue cashmere mai fitinanniyar tsada qamshinsa yana sauya niimar gurin take dukkanin bayin dake hanyar suka sauke kansu qasa suna tsayawa cak inda suke har saiya wuce. Maa sakinah dake gap da shigewa da Bahar bata juyowa tayi a natse dan basa girmamawa itama a natse Banda Bahar da batasan me takeyiba daga kafarta tayi tana cigaba da Takawa ba karfi a gangar jikinta ko kadan. Sautin takunta ne da sarkar kafarta ke fiddawa a natse a gurin daya dauki tsit tamkar babu rai ko daya a gurin sbd bada girmamawa garesa ya sakasa tsayawa da takunsa cak yana dakatawa. Sake ratsa kunnuwansa sautin yayi Wanda ya sakasa juyowa da Wani irin nutsuwa da mamaki yabi inda sautin

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});