Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ******** ************* Matsota Abaa yayi tayi saurin sake yin baya da karfi tana fasa kuka me karfin gaske numfashinta na sarkewa. Abaas da Zuhrah da Nurat kuwa gabaki daya riqe Abaan sukai kowannesu jikinsa na rawa suna tsananin rokonsa akan ya biyo su su tafi karya sauya hakan. Zafafan hawayensa ne masu tsananin zafi suka Riga akan fuskan Abaas dake jikinsa ya sauke Kansa yana banbaresu daga jikinsa yace suyi sauri subar gurin shi zai rufe hanyar kafin kusrawa su qaraso sunyi nisa zai biyo su daga baya. Girgiza kai dukkaninsu suka hau Ayanah kuma tsananta kukanta yayi tana Jin kirjinta na wani irin radadi me tsananin gaske. Harbin mashi suka fara Ji tako ina ba tsammani take suka fara gudu dukkaninsu wasu kuma kibiyar na samun su dan haka suka shiga firgici me firgitarwa suna Neman rarrabewa amma Abaa ya kasa barin hakan ya taresu ta baya suna gudu me tsanani batareda sunsan inda suke jefa kafafunsu ba. Biyosu kusrawa sama da arbain sukai suna harbosu da kibiya tako ina suna wani irin ihu dake girgiza duk wani me sauraro. Duhun dajin suke bi suna gudu sosai Wanda kusan da yawan wainda suke tareda su suna Jin yanda suke mutuwa amma babu daman tsayawa wa hakama Abaa cikin tsananin tashin hankali ya hanasu juyawa su waiwaiya baya yace suyita gudu karsu tsaya. Cikin gudu da tsananin ciwon dayakeji a kirjinsa na tsananta yace ‘Ayanah duk tsanani kada ku tsaye kuyita gudu harsai kun tsira’ Sanyi jikinta yayi zata juyo cikin karfin hali da daga murya yace karki juyo Kuyita gudu Ayanah. Muryansa da bataji daidai ba ya sakata juyowa da sauri idanuwanta suka akan kibiyar data bullo gefen kirjinsa ta bayansa da aka harbo Tsayawa zatai Ya fizgeta da karfi yana turata yace ‘Ku tafi karku tsaya, Ku tafi Ayanah, Ki tafi dasu karki Bari kowa ya juyo bare tsayawa’ Kasa wa tayi ta juyo tareda riqe hannunsa suna gudu tare yana turata daga jikinsa zuwa gaba yana cewa ta tafi ta kula da yan uwanta ta tabbatarda sun tsira sun kubuta sun Gina rayuwa me kyau. Fara gazawa yayi dan haka turata da karfin gaske tana kokarin dawowa ya dago idanuwansa jajir yace ‘Ban Aminta ki tsaya ba bare dawowa gareni ki tafi Allah zai zama gatanku insha Allah, Burina burin Ammanku shine ku tsira dan haka Ayanah ku tafi ku cika mana wannan burin ku rayu, Duk rintsi ku hada kai karku rabu da juna’ Sake turata yayi sa karfi tana qara riqosa amma ina jini sosai yake fita a kirjinsa harma da bakin sa take kafafunsa suka kasa daukansa ya durqushe a gurin ta kira sunansa da karfi tana kokarin durqusawa Kaman daga sama taji bayanta an riqeta. Cikin tsananin azaba ya dago idanuwansa ya kalli Asamah wadda bata hayyacinta sbd kukan baqin ciki da danasanin datake ciki tareda fatan tayi mummunan mutuwan data jawa rayukan dake ANJOM. Daqyar ya bude baki jini na fita sosai yana kallan Asamah yace ‘Ki tseratar dasu, Karki bari kowannesu ya tsaya bare dawowa ANJOM ‘ Janta Asamah tayi tana Hana su Zuhrah dawowa suka fara ihu ganin halinda Abaansu ya shiga ransa na kokarin barin kirjinsa sbd wani irin jinin dake fita bakinsa. Kaman daga sama sai ganin Mutum biyu sukai akansa ba Imani a tare suka soka wuqa biyu a wuyansa idanuwansa na kan yayansa dake Ihun gaske suna Neman zarewa sbd mummunan tashin hankalin sheda mutuwan mahaifinsu akan idonsu. Asamah cigaba da turasu tayi suka kutsa dajin suna tsananta gudu hannun Ayanah yana cikin na Abaas hakama Nurat da zuhrah suma hannuwansu na riqe dana juna. Biyo su akai wannan Karan an Dena harbin da alama da rai ake sonsu. Kuka sosai sukeyi suna tsananta gudunsu Banda Ayanah datake Jin zuciyarta na kokarin nema bugawa hakama idanuwanta basa ganin komai jefa kafa kawai takeyi. Dukkaninsu sun kasa yadda a awannin da basu wuce uku ba sun rasa iyayensu duka cikin dare daya a Masifa da mummunan kaddara daya, Neman sarewa sukeyi amma Sam Asamah ta kasa Bari saima hanya data sauya musu sbd an kusa kamosu dan haka cikin wani irin qazantaccen rami ta turasu suka shige suka boye tareda sakina wadda take riqe da Zuhrah a yanzu. Suna shigewa Asamah ce ta saka hannuwanta ta toshe bakin Nurat da Abaas ita kuma sakina ta rufe na Zuhrah sbd yanda suke kuka suna wata irin jijjiga. Ayanah ta kasa komai ta koma tamkar marasa hankali da kwakwalwa kwata kwata dan haka batace komai bare kukan Wanda ya kasa fitowa tsabar muni da girman tashin hankalin datake ciki. Suna Ji kusrawan na wucewa da gudu da karfi suna ihu me ban tsoro amma basu motsa ba har saida suka Ji sun gama wuce kafin Asamah ta zare hannunta a Bakinsu Sai a lokacin Nurat ta fasa wani irin kukan daya saka Idon sakina fara zubar hawaye Asamah kuwa kukan itama ta fasa me tsananin ciwo tana rungume Zuhrah dake jijjiga kaman me wani ciwo. Rintse idanuwa Ayanah tayi tareda sunkuyar da kai tana fasa kuka mai tsima zuciya da girgiza kowa. Babu Wanda yace komai a cikinsu dukkaninsu kuka ne sukeyi mara dadin Ji bame rarrashin wani sbd kaddarar tayi musu nauyin da zuciyarsu take kasa dauka, Ayanah hannu ta Dora Akan kirjinta tana duka kukanta na sake tsananta sbd kirjinta ya toshe Jin takeyi kaman ta mutu tabi iyayenta. Har asuba tayi gari ya fara haske suna cikin ramin idanuwansu sunyi wani irin kumbura da ja babu me iya dogon motsi sbd mutuwa da jikinsu yayi rayuwan gabaki daya ta fice musu arai sbd basu San ta ina zasu fara rayuwa babu daya daga cikin iyayensu ba, Basu San koinaba,basu taba fita ANJOM ba tinda aka haifesu, Basu saba da kowa ba Bayan junansu fa iyayensu, Basu taba jagorantar lamarin su ba da kansu komai iyayesu ne ke tafiyar musu dashi, Abinci ma basu taba Cinsa batareda iyayensu ba, Ayau dare daya sun tsinci kansu a mummunan kaddarar da basuma San ina zasu ba, Gurin wa zasu? Tayaya zasu fara rayuwa? Yaya rayuwa zatai dasu bare Wanda zai tsaya ga lamarinsu dan haka Ayanah kukanta ke karuwa sbd batasan ta ina zata fara zamowa uwa da iyayenta suke fada Akan kannanta kawai dai abu daya ta sani a yanzu zata iya rasa rayuwarta akan wani abu ya samesu sbd sune rayuwanta. Sakina ce takeda dan Sauran kuzari a jikinta sbd itama

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});