Chapter 8
Chapter 8
tanadar muku ta barin gari ku bi karku tsaya sai kun fita ruwa gabaki daya kun fada nahiyar yom acan zaku samu rayuwan kwanciyan hankali idan har kuka fadawa sarkin garin ku GHAZ ne. Shiru sukai dukkaninsu Banda Ayanah da Amma da suka riqe hannunsa suna girgiza kai, Nurat da Zuhrah tareda Abaas kuwa cikin tsananin tashin hankali da wani irin firgici suka ce ‘Abaa ina zaka? Karka fita dan Allah kazo mu tafi din bama sai mun jira ba dan Allah Abaa’ Girgiza kai yayi yana kallansu da jajayen idanuwansa da suke rine da tsananin ‘daci da baqin ciki yace ‘Ni shugaba ne ta yaya zan tafi nabar mutane na batareda nasan meya ke faruwa a garin ba…….. Katsesa Amma tayi cikin wani irin mugun tashin hankali muryanta na rawa zufa na tsiyayo mata da cewa ‘Koma menene ba alkhairi bane sbd Ihu da kukan da garin gabaki daya ya dauka ya tabbatarda hakan, Masifa ce da balai a garin yau karka tafi dan Allah ka tsaya’ Zare hannunsa yayi cikin nata idanuwansa na sake kada wa jajir. Cafke hannunsa Ayanah tayi tana fadawa jikinsa ta qanqamesa wasu hawayen tashin hankali me tsanani suna kufce mata a rikice tace ‘Abaa dan Allah karka tafi mu tafi mubar garin tare bazamu iya tafiya koina babu kai ba’ Nurat ma qanqamesa tayi Zuhrah ta fada jikin Amma tana qanqameta Abaas ma Abaan ya riqe yana wani irin rawar jikin tashin hankali da tsoro take ya fasa kukan daya saka Abaan kallansa yanajin tsananin tausayinsa. Banbare Ayanah da Nurat yake a jikinsa suna qanqamesa Ayanah tayi fashewa da wani irin kukan da bata taba sakewaba a rayuwarta tana ambatar sunan Abaan. Fincikesu yayi da qarfi yana hana zuciyarsa karyewa ya turasu jikin Amma ya fice da sauri yana janyo marufin dakin. Rawa da kuka sukeyi sosai Wanda gabaki daya gurin yayi tsit sai sautin kukansu dake tashi ahankali cikin mummunan tsoro,fargaba da tashin hankali. Masifa,balai da kaddara ne suka saukarwa garin ANJOM a cikin Daren dayake na farko a tarihinsu da wannan masifar ta fadowa garin, Wuta ce take ci tako ina zagaye da garin Wanda saida kusrawa suka gama cinnawa zagayen garin wuta sosai koina ya Kama sannan suka shigo cikin silalowa suka sakawa koina wuta a cikin garin kafin suka afkawa garin da wata irin mummunan kisan da take jini yafara fesuwa koina na mutane. Ihun da kukan Neman agaji da ceto mutane suka fara Wanda ya saka gabaki daya garin daukan hayaniyan Data saka kowa fitowa Ana gudun Neman ceto sedai yawa da karfin da kusrawan ke dashi ya saka munin lamarin yayi yawan da komai ya lalace. Kukan kananun yara dana mata da dabbobi ma dake gudun cetan rayuwansu ne yake gauraye gari da dajin ANJOM dayake amsa wa cikin sauti mara dadi da karya zuciya tareda tsananin tausayi. Wuta kuwa haka take cin wasu mutane harma da dabbobi sbd gobara sosai garin ya dauka kowane gida sakawa wuta sukeyi sbd kada ma mutane su samu gurin boye dan haka komai ya zama tashin hankali mara misali lokaci daya. GHAZ da fadawansa da askarawansa koda suka fito dan bada ceto ga jamaar gari lamarin ya gama munanar da babu abinda zasu iya sbd Angama cinye garin ANJOM da wuta da jinin mutane dan haka take suka fara cetan wainda zasu iya cikin azabar wuta da tashin hankalin munin gawawwakin mutane da suke tsallakewa da takawa. #MAMUH #ROYALTY #SLAVERY #BEST LOVE HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070 6 *_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ******** ********** Wani irin zufane yake jiqa Dukkaninsu zuciyoyinsu kaman zasu fado sbd munin tashin hankalin dasuke ciki, Cikin duhun hasken wutar daya kusa cinyewa Ammah ta dago Idanuwanta da sukai jajir da hawaye masu karya zuciya ta kalli Ayanah kafin ta maida kallanta kan Sauran ‘yayan daya bayan tana hana hawayenta saukowa fuskanta sbd zuciyoyinsu duka a karya suke batason qarasa karyasu gabaki daya. Juya kanta tayi ta kalli kofar dakin zuciyarta na kasa jurewa ta juyo ta sake kallan Ayanah wadda tayi saurin riqeta cikin mummunan tashin hankali ta bude baki da wata irin murya mara karfi cikin yarensu tace ‘Aāyi Amma, ātadirigi Amma, dan Allah Amma karkiyi hakan, āyi Amma.’ Hawayen da Amman ke riqewa ne suka gangaro cikin tsananin karyewan zuciya ta kalli Ayanah din tace ‘Ayanah dole zan dubosa sbd da hakan zamu tsira gabaki dayanmu’ Wani irin rikitaccen kukan tashin hankali me tsanani Ayanah ta sake tana rintse idanuwanta tareda sake qanqame hannun Amman tana girgiza akai ko magana ta kasa, Nurat datake qame tin Bayan biyar Abaansu riqe hannun Amman daya tayi Tana girgiza kai itama hawaye masu tsananin zafi na gangarowa daga idanuwanta. Abaas dake rungume dashi da Zuhrah saurin fadawa jikin Amman yayi ya rungumeta shima dukkanin jikinsa na rawa yace ‘Amma babu inda zaki tafi’ A rufe murya na rawa Zuhrah tace ‘Abaa ya tafi zai dawo Amma mu jirasa dan Allah karki tafi, Idan kin tafi zan biki mu dubosa tare’ Turesu tayi daga jikinta tana kasa kallan kowannesu tace ‘Ku jira zan dawo, Ayanah ki kula dasu karki Bari kowa ya biyo koda ban gansa ba zan dawo’ Sake riqeta Ayanah tayi Tana girgiza kai hannunta na rawa sosai muryanta na sake mutuwa kukanta na bayyana tace ‘Amma bazan iya ba dan Allah karki fita, Amma bazan iya ba, Āyi Amma dan Allah’ Zare hannu Amman tayi tace ‘Ayanah zaki iya yanzu fa zan dawo, Nima idan na dade ku tafi kawai zamu taho daga baya ni dashi mu sameku acan Kawai ki tabbatarda kin kula dasu sbd kece uwa a cikinsu kinji?’ Kasa cewa komai Ayanah din tayi kukanta na qaruwa tana girgiza kai jikinta na rawa sosai, Su Zuhrah ma kuka sukeyi sosai suna qanqame Amman hankalinsu a tsananin tashe tsoronsu na sake bayyana. Sake daukan Ihun tashin hankali da tsananin tsoro garin ke dauka hakama wuta tako ina Wanda ya saka Amman kasa riqe kanta sbd tana buqatan janyo GHAZ subar garin dan kuwa ba lallai su tsira ba hakan kawai ya hakura su tafi kawai dan tseratar da ahalinsu. Tsoronta cirewa yayi tana Jin tsananin buqatan dawowansa su bar garin ta qwace daga riqon da yayanta sukai mata ta fice tareda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106