Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wata duniyar yana gararin da zai iya rasa rayuwarsa koma ya rasa din? Ayanah kin manta komai ne kin zubar da komai? Sakinah data fito wanka ne ta iso gurin Zuhrah din da sauri tana riqe hannunta cikin tausasawa tace ‘Kar kice haka Zuhrah’ Fizge hannu Zuhrah tayi tana Miqewa tsaye idanuwanta na gangaro da hawaye tace iso gaban Ayanah din wadda bata iya juyowa ba ta kalleta cikin wani irin radadin zuciya tace ‘Maye a cikin wannan sabuwar rayuwar daya mantar dake yan uwanki da halinda muka shiga? Daman damuwarki Akan yan uwanki na dan lokaci ne? Daman akwai jin dadin da zai taho miki ki manta dan uwanki dake can duniya cikin garari da qunci?…. Riqota da karfi sakina tayi tana cewa ‘Ya isa haka Zuhrah,kinfi kowa sanin Ayanah ba haka take ba karki Bari Batan tinani yakaiki ga aikin dana sani’ Sake fizge wa tayi tana kallan Ayanah wadda ta dago ta zubawa Zuhrah idanuwanta da sukai wani irin jajir tsananin qunci da radadi me ciwon gaske yana cikesu amma bazata iya cewa komaiba Bayan kallan zuhran dake fada mata maganganu masu ciwo da radadin gaske. Zuhran ma cikin tsananin jin ciwo da radadin ganin idanuwan Ayanah din taci gaba da fada mata maganganun da itama suke sosa zuciyarta tace ‘Ayanah su Amma sai sunyi Allah wadai dake da zasu dawo duniya su ga yanda kika zabi jin dadin duniya kika manta amanar da suka bar miki a lokaci dan qanqani, Abaas zaiyi baqin cikin zabar sonki fiyeda Sauran yan uwansu idan yaga yanda kika zabi wata rayuwar akan tinaninsa, Ayanah inama ace Nurat ce aka bar mana dan ita bazata taba manta yan uwanta ba koda bata cikin hankalinta…..’ Wasu irin hawaye ne masu tsananin dumi suka gangaro daga cikin idanuwan Ayanah a karo na farko Bayan tsawon lokaci mai nisa, Silalewa qasa take kokarin yi sakina tayi saurin riqeta tana fasa kukan kalaman Zuhrah itama sbd tsananin tausayin Ayanah wadda har lokacin ta kasa furta komai sbd rabata da ranta ne kawai kalaman Zuhrah basuyi ba amma sun gama ratsa zuciyarta sun yayyankata, Kalaman sun qarasa karya duk wani kuzarin daya rage mata na rayuwa, Kalaman sun yanka mata sabon Raunin da shima har abada bazai warke ba……. Wasu irin hawayene ke gudu sosai a fuskanta ta kasa iya tsayuwa duk riqon da sakina tayi mata silalewa qasa tayi tana Dora tafin hannuwanta biyu a fuskanta ta rufe wani irin kuka mai qaramin sautin daya saka Zuhrah yin tsit yana zuwar mata jikinta na wata irin rawa sosai wadda ta saka sakina zubewa qasa tana rungumeta da sauri, Zuhrah ma sautin kukan ya ringa sosa zuciyarta ta durqushe itama a gurin tana fasa kuka sosai zuciyarta na dana sanin saka Ayanah kuka irin haka. Shiru dakin ya dauka babu sautin dayake tashi saina kukansu mara sauti sosai amma babu dadin Ji ko kadan. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 22 *JEWELRY JUNCTION* 08039440312 Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma, Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne?? To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan, Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana, ✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌 ✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌 ✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌 ✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍 🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah. WhatsApp 08039440312 Tiktok :@sokoto jewelry seller Instagram: jewelryjunction23 ********* Sun jima a wannan yanayin kafin Ayanah ta taqaita kukanta data jima bata samu yi ba sai yau ta miqe tareda sake komawa toilet. Acan ma wani irin sabon kuka ta durqushe tana yi Wanda dukkaninsu suna jiyota daga bandakin sai data jima tayi ta gama ta wanke fuskanta da ruwa ta fito ta goge fuskanta ta shirya cikin uniform dinta tana jin kirjinta da zuciyarta na Wani irin ciwo amma batada abin yi musu kawai qarasa shirinta tayi ta koma gefe ta zauna tareda kallan Zuhrah dake kuka har lokacin ta taso ta rankwafo kawai ta sumbaci tsakiyar kanta da gefen fuskanta ta bude baki da tsananin sanyin murya ta bude baki tace ‘Ya isa haka ki wanke Fuska ki shirya mu fice’ Ajiyan zuciya Zuhrah ta sake tareda dagowa ta kalli Ayanah din zata bude baki tayi magana Ayanah ta girgiza mata kai tana cewa ‘Ba komai ya wuce kije ki shirya din’ Miqewa Zuhrah tayi ta fada toilet duk ta zama kalar tausayi. Tana fitowa sakinah ma ta shiga suka gama shiryawa tsaf suka fito su ukun suka wuce zuwa hall din karatun. Wannan sabanin da suka samu ya sake ruguza Ayanah ta qarasa rasa walwala da kuzarinta sbd damuwan datai mata yawan gaske a cikin rai dan haka ta sake zama tamkar qanqara sbd sanyi da rashin magana sosai, Komai Zuhrah takeso shi kawai take mata bata iya hayaniya ko magana koyaushe indai suna daki Zuhrah na jikinta kwance zata rungumeta tana mata addua da shafata dan bata nutsuwa sbd tsoro da firgici na Neman taba kwakwalwan Zuhrah din tsoro mai tsanani kawai take samun kanta sbd ganin kaman suna shiga palace din sun rasa kansu kenan har abada kila ma harda junansu, Tsananin tsoron rabuwa da Ayanah take ji fiyeda komai ma daya faru a baya, Idan har zata rasa Ayanah so take Allah ya dauki ranta ta mutu, Koba komai mutuwar ma take tsananin so sbd rashin nutsuwan datake ji a zuciyarta. Ana gobe ne ranar tafiyarsu zuwa cikin palace a zaune suka kwana rungume da juna Sai a Daren Ayanah ta bude baki tayi doguwar magana da Zuhrah din tareda tinatar da ita babu abinda zasu iya yi a duniya yanzu su samu damar haduwa da Abaas wata rana irin su jajirce su rayu har zuwa lokacinda Allah zai sake kawo musu wani sauyin rayuwar, Babu abinda zasu sakawa kowane dan GHAZ dashi Bayan su rayu su kai labari dan haka matiqar tanason Allah ya kawo mata ranar haduwa da Abaas ko jin labarinsa to tabbas zata jajirce ta rayu zuwa lokacinda Allah zai dauki ranta. Zuhrah da Sai a lokacin ta fahimci karfin halin da Ayanah takeyi jin tayi jikinta ya sake mutuwa dan kuwa kaman ita bazata iya ba takeji amma ko bazata iya ba zatai kokarin bawa Ayanah karfin gwiwan rayuwa sbd itace kadai a raye wadda take saka zuciyar Ayanah bugawa daidai, Ita dai kam bazata iyaba

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});