Chapter 35
Chapter 35
jin dumin juna ba, Bazamu taba kallan juna ba, Bazamu taba dawowa Ayanah da Zuhrah GHAZ ba shikenan mun rabu har abada sai kuma ranar da Allah ya bamu yanci Kinsan da hakan? Wannan shine doka da qaidar kuma taka hakan a bakin rayuwarka kenan,bazan iyaba Zuhrah.’ #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 23 FREE CLASS ALERT 07068433198 Kinason business dinki ya zama tamkar kamfani me zaman kansa, Kina da kaya ko sabis Amman tallanki baya Jan hankali? Mutane suna ganin tallanki Amman basa saye? Lokaci yayi da Zaki koyi yadda ake vedio advert mai daukar hankali da kawo kwastomomi🥳🎉 Shiga wannan FREE CLASS ki koyi yadda ake hada vedio da zai juya masu kallo zuwa kwastomomi🎉 ********** Sakinah data yadda da indai zasu rayu gwara su hakura din matiqar sunsan suna guri daya yafi a san sunada alaqa tin anan gurin a kashesu a banza kokuma a rabasu duniya daban daban gwara su tsaya guri daya koda babu abinda zai sake hadasu har abada dan haka hannuwansu ta Kama da hannuwanta biyu ta rabasu da karfi Zuhrah na Wani irin kuka Mara sauti zuciyarta na mutuwa a matakin karshe na shikenan. Ayanaah ma wani irin kuka takeyi mata sautin tana kasa dauke idanuwanta daga Zuhrah wadda itama ita take kalla sakinah ma hawayen takeyi tana sunkuyar da kanta qasa. Layi na zuwa kansu sunansu AYANAAH GHAZ da ZUHRAH GHAZ Ana tambayan alaqarsu Ayanah ta dago jajayen idanuwanta da suka rine gabaki daya ta zubawa Zuhrah wadda ta goge fuskanta tas ta bude baki tace ‘BABU ALAQAR JINI sunan ne iri daya’ Tana fadar haka take aka buga stamp a sunayensu tareda wata irin stamp ta daban wadda take bada tabbacin ko a toilet daya tsautsayi ya hadasu a kashe dayansu abar daya sbd kawar da zargi hakama duk ranar da dayansu ya kalli daya shima hukuncin daya ne. Miqa musu Id cards nasu akai tareda jansu zuwa ciki Wanda kowannensu babu abinda yake aiki a gangar jikinsu Bayan kafafunsu dake jansu kaman marasa lakka a jiki. Hawaye ne masu tsananin zafi suka gangarowa Ayanah tanajin kusan komai nata na Dena aiki tanason dagowa tayiwa Zuhrah kallan karshe amma damar ta qare hakama itama Zuhrah Ayanah takeson kallan ba damar ta qare sedai hawaye suka sauko mata ta rufe idanuwanta tana bin inda ake tafiya dasu hanya daban da wadda aka tura Ayanah da sakina. Duk Taku daya da Ayanah ke yi jin takeyi tana rabuwa da ruhinta sbd a yanzu kam takai matakin karshe na rasa komai nata batada Sauran hasken da idanuwanta zasu gani ko miskala zarratan, Rawa kafafunta keyi zuciyarta na kasa wa sbd bazata iya rabuwa da Zuhrah ba koda hakan zai rabata da rayuwanta ta yadda dan haka ta dakata ahankali daga tafiyan datake, Dagowa tayi ahankali zata juya ta kalli Zuhrah koda hakan zaiyi sanadin rayuwanta, Da sauri sakinah dake bayanta ta riqeta cikin nutsuwan da bazata bari a gane su ba ta hanata Juyawa sbd bazata iya barinta Juyawa ta rasa rayuwanta kokari da sadaukarwar Zuhrah ya tashi a banza, Wasu hawayen ne masu tsananin zafi suka cigaba da gangarowa Zuhrah wadda itama bata juyoba tana Jin ciwo da radadin halinda Ayanaah take a jikinta, Sakinah ce ta iya waiwayowa a hankali ta zubawa Bayan Zuhrah dake tafiya jikinta na bayyanarda gap take da samun bugawan zuciya, Tausayinta ne ya rufe zuciyar sakinar sbd ita zata rayu bateda duk Wanda rayuwarta ta taba sani ba dan gwara Ayanaah din ita tana tareda ita, Koma menene tasan wannan ma wata sabuwar jarabawar ce Allah zaici gaba da jarabtarsu da ita, Ahankali ahankali aka gama rabasu zuwa bangarori da dama Wanda sai da aka kuma daukansu cikin wasu motocin aka isa dasu can ciki inda duniyar boyem take, Tsari da yanayin gini da aljannar duniyar dake cikin Masarautar boyem ya wuce tinanin duk wani labarin daular duniya da ake bada labari da tarihin Masarautu, Tamkar suna tafiya baa cikin duniyar ba haka suke jin kansu sbd koina da ake giftawa dasu madubai ne suke ganin kansu a ciki suna daukan idanuwansu dan haka tsoro duka ya cika su suka sake saukar da kawunansu a qasa suna kama jikinsu dake rawa sbd tsoro suna tattaro nutsuwarsu sbd itace gaba a komai na aikinsu. Kai tsaye sabon bangaren bayin dake cikin masarautar aka kaisu aka basu daki shima kamar wancan da suka Baro daular bayi sedai wannan Mutum uku uku ne a daki. Duniyar da aka jefata daban data Zuhrah sbd tsakanin bangare da bangare akwai yar tazara da kuma tsaro sosai dan haka ita kai tsaye ita bangaren imebētiś aka kaita Wanda yake duniya ce guda mai zaman kanta wadda take dauke da part part sun kai hamsin duka na imebētiś ne maana mistresses na sarki, Duk macen da sarki ya kwana da ita indai ta samu ciki anan zaa bata flat dinta mai shegen kyau da wata irin daula a cikinsa tareda bayi sama da goma wainda sun zama nata zatai rainon cikinta anan ta haihu anan ta reni jini boyem cikin jin dadi da daular da hankali ma bazai daukaba kuma anan zataci gaba da rayuwanta da bayinta cikin jin dadi da yanci har sai jinin BOYEM data haifa ya girma ya kai shekaru goma sha biyar shikenan zaa ware masa nasa muhallin daya zarce tinani acan cikin asalin ginin da sultan yake a zuba masa bayin ya koma can sedai Yazo gaida mahaifiyarsa kokuma ita taje gurinsa. Duk macen da sarki ya kwana da ita kuma bata samu ciki ba bangarensu daban bautar suke komawa sedai Ana sauya musu guri a cire su cikin asalin bayi, To Ayanah a cikin bayin dake kulawa da sabuwar imebētin sultan aka kaita itada sakina ita kuma Zuhrah a can asalin bangaren uwargidan sultan aka kaita dan haka sukaiwa juna Nisan da babu ranar cike gurbin. Tinda suka iso dakinsu Neman somewa Ayanaah keyi sbd halinda tashiga na rabuwa da Zuhrah daqyar sakina ke kokarin bata taimakon daya hanata somewan sedai har tsakar dare tana fama da ita kafin Allah ya kawo mata dangana ta sakawa kanta karfin halin hakura. Washe gari tinda asubar fari suka shirya cikin uniform dinsu tsaf suka fito zuwa aikinsu, Kai tsaye bangaren sabuwar imebetin suka isa su shida ne dan haka suna isa suka bude suka shiga kai tsaye kowannensu ya fara hidimarta tin kafin ma ta tashi. Ayanah aikin gyara toilet tayi tareda wanke Kayan wankin da ime din tayi amfani dasu ta wanke su sosai da hannuwanta batareda ta saka washing machine ba duk da an koya musu komai da yanda zasuyi amfani da koman a gurin karatunsu, Tana gamawa sake gyara toilet tayi ta hada mata ruwan wanka masu dumi sosai da Kayan qamshi masu dadi na wanka Wanda duka shima an koya musu dan kusan babu abinda baa koyar musu ba komai kankantarsa, Tana gamawa ta koma bakin toilet din ta tsaya kanta a qasa tana jiran farkawanta, Tsayuwan mintina talatin tayi kafin ta fito daga cikin makeken lafiyayyan gadonta mai rumfar dataji ado da dukiya. Tana qarasowa ko amsa gaisuwan da Ayanah din tai mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106