Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fitar sa ba, Tsananin tsoronsu haduwa da Kusra da suke cikinsa dan haka suke Jin kaman suyita zama bakin ruwan har ransu yabar jikinsu. Zuhrah da har jikinta ya fara rawa sbd tsananin tsoro da tashin hankali tareda tina azababbiyar tafiyar kallan Ayanah tayi da idanuwanta da sukai ja sosai ta bude baki cikin tsananin tsoro da sallamawa tace ‘Ayanah wannan itace karshen kaddararmu, Mu karbeta kada mu koma dajin nan, Mu fada ruwan nan rayuwarmu tazo Karshe mu huta dan Allah, Bazan iya ba Ayanah, Mutuwar tafi mana biyu Hutu da sauki dan Allah Ayanah mu fada ruwan nan mu tafi mubar duniyar nan wlh bazamu iya ba, Koina bazamu kai ba zamu rasa kanmu dan haka dan Allah mu yankewa kanmu wahala….. Abaas na Jin hakan yaji zuciyarsa na Aminta da yadda da hakan dan haka Ayanah yake kalla idanuwansa cikeda hawayen rauni da ‘qunci yana Jiran jin tace ta amince da hakan, Kallansu Ayanah tayi tana jin zuciyarta na yadda da hakan itama sbd tabbas din bazasu iyaba dan haka gwara su mutu anan tin kafin azabar da ukubar tayi yawan da babu iyaka. Ganin yanayin Ayanah din na itama tana ganin hakan shine zai fi musu yasa Zuhrah Jin dan dadi dan har zuciyarsu gabaki daya sun zabi mutuwar sbd itace hutun karshe da zasu samu a wannan duniyar dan haka miqewa tayi tana Juyawa ta kalli ruwan tana Lumshe idanuwanta zuciyarta cikeda samun nutsuwa ta juya gurin Nurat dake Zaune quri babu alaman tasan komai dayake gudana a rayuwanta yanzu ta durqusa gabanta ta kamo fuskanta da tafukan hannuwanta biyu takai bakinta ta sumbaci gefen fuskanta da gashinta kafin ta hade goshinsu tana cewa ‘Nurat inda su Abaa da Amma suka tafi zamu tafi zamu bar nan bazamu iyaba,ke kin rasa hankalinki bazaki taba gane azabar da zamu shiga ba amma kuma zaki kasance cikin hadari dan haka mu tafi…. Kama hannun Nurat tayi ta miqar da ita ta kalli Abaas ta miqa masa hannu shima ya Kama ya miqe tsaye, Ayanah suka tsaya akanta suna kallan da jiranta, Abaas da Zuhrah din tare suka miqa hannu ta kallesu tana miqa hannunta ta Kama nasu zata miqe Sakinah tayi saurin riqeta tana girgiza mata kai tace ‘Idan kun zabi mutuwa Akan rayuwa zan biku Nima na zabi mutuwar sedai idan kukai hakan sadaukarwar iyayenku dan kawai ku rayu ta zama ta banza, Sadaukarwar Asamah ta zama ta banza itama, Ayanah ki tina su Abaa basu da burin daya wuce ku rayu kota yayane, Ku tsira kota yaya ne, Duka duniyar kowa dake gwagwarmaya yana yi dan cika burin magadansa da magabatansa amma ko kwanaki masu yawa baa yiba zaku kashe kanku sbd kasa rungumar jarabawa., Idan har jinin iyayenku ne jinin GHAZ yake yawo a jinin jijiyoyin jikinku to tabbas zakuyi kowace irin gwagwarmaya ku jure ku rayu dan tabbatarda burin iyayenku ya cika kun tsira sun rayu kun samu rayuwa da zaku tina baya ya zama tarihi, Wannan shine ya kamata ya zama sabon Alkwarin jini da duk wani jinin GHAZ zai taso a cikinsa na duk zuriar GHAZ da zasu zo a gaba wato juriya ga dukkanin tsananin rayuwa kowane iri ne ka tsira ka rayu, Karku manta kune jinin GHAZ na karshe Wanda kuna barin duniya dukkaninku to shikenan jinin GHAZ Yazo Yazo karshe kun shafe a duniya sedai a tarihi idan an ambaceku dan haka Kuyi hakuri Kuyi juriya Kuyi gwagwarmaya kuci gaba da jagorantar GHAZ ku yada zuriar da zata ci gaba da jan sunan GHAZ a duniya.’ Kuka Zuhrah keyi sosai da maganganun da suka shige su amma ita har lokacin tana jin tafi son mutuwar sbd bazata iya rayuwar da dabbobi ma sunfi su yanci da gata da rufin asiri tareda kwanciyan hankaliba, Kallan Ayanah dake kuka sosai kaman ranta zai fita cikeda da gajiwa take kukan idanuwanta sunyi kumburanda kaman zasu fado su tsiyaye. Maida kallanta kan Abaas tayi Wanda shima kukan yakeyi sosai hannuwansa na kakkarwa, Nurat ta juyo itama ta kalla wadda ta koma abar tausayi yanzu sbd bata iya cewa komai zuru tayi da idanuwanta dake bayyanarda tsananin qunci da Neman Hutu na barin duniyar sedai batada tinani na kanta yanzu sai yanda akai da ita. Itama Zuhrah jin tayi kaman kanta da zuciyarta bazasu dauka ba dan haka ta fara ja da baya tana hawaye. Miqewa Ayanah tayi batareda tasan tanada Sauran karfinba tayi kan Zuhrah din da sauri sedai Juyawa zuhran tayi tana nufar ruwan da gudu zata fada, Abaas ne shima yayi kanta da gudu hakama sakinah Ayanah Sakinah kuwa Nurat ta riqe sbd kada itama ta juye ta bisu ta fada ruwan. Har Zuhrah ta fada ruwan Abaas ya Riga Ayanah isa gareta ya riqota tana fizge wa tana kuka me karfi tana rokonsu su tafi. Rungumeta Abaas tayi sosai jikinsa yana bude baki cikin karfin Halin dake zuciyarsa data fara bushewa yace ‘Zuhrah zamu jure,zamu jajirce,zamu tsira,zamu rayu insha Allah zaku ma mu sake amsa sunanmu GHAZ wata ran…. Girgiza kai takeyi tana cewa ‘Aa Aa Abaas bazamu sake amsa sunanmu ba har abada gwara mu tafi dan Allah’ Girgiza mata kai yakeyi shima yana sake daurewa kukan dayake zuwar masa Ayanah ma rungumesu tayi dukansu tana maimaita abinda Abaas ya fada Akan sun rungumi hukuncin ubangiji duk tsananin tsanani zasu jure zasu jajirce zasu rayu a cikin kowane Hali dadi ko wuya. Kuka Zuhrah keyi sosai tana girgiza kai a hakan haka har suka fito ruwan suna samun guri suka zauna suna yin shiru tsawon lokaci kafin suka kalli juna suka sake daukanwa kansu alkwarin jurewa da rungumar kaddara tareda kasancewa da juna sbd duk masifa da munin rayuwan da zasu fuskanta idan suna tare da juna zasu jure dan rabu wa da junansu shine mafi muni da girman kaddarar da suke tinanin zai samesu Wanda gwara musu mutuwa Akan hakan. Fitowa rana ya saka suka miqe suna sake cika cikinsu da ruwan sosai suka bar gurin Bayan sun jiqa kayansu sosai da ruwa har suna tsiyaya ta yanda zasu yi tafiya me tsayi basu azabtu da tsananin Zafin rana da kishirwa ba. Komawa sukai cikin dajin suna kallan hanyar gabas suka miqa suna riqe hannun juna Nurat kuma tana hannun Abaas ya riqe hannunta gam cikin nasa. Wuni sukai suna tafiya har rana ta fadi duhu yayi suka nema guri suka zauna babu me iya numfashin arziki sbd wahalar yunwa da kishirwa. Dukkaninsu sunyi galabaitar da baa magana dan haka tinda suka zube a gurin babu Wanda ya sake motsi kaman matacci har gari ya kuma wayewa yayi haske. Numfashinsu fara Neman gagararsu yakeyi amma a hakan suka tashi suka sake bin hanya suna kasa ko riqe juna wannan Karan, Wuni suka sake yi suna yawo a dajin batareda ma sun San inda suke jefa kafafunsu ba gashi kaman dajin dayake da wani sirri dan baka iya gane gurin fita.. Kwanaki suka dauka suna ragaita a mummunan dajin Wanda zuwa lokacin tini suka fara cin ganyen duk icen da suka samu Wanda yafara maidasu kaman wasu dabbobi, Kamanninsu sun sauya daga mutane zuwa wasu kalar, Fatar su ta koma kaman busashiyar dabinon daya fito cikin qasar sahara, Bakinsu ya bushe ya far fashe jinin dayake fitarwa shi

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});