Chapter 68
Chapter 68
take ciki daidai wannan lokacin. Barin sukai da zuhran wadda bata iya Miqewa qyam tsaye sbd yunwa da wahala hakama fatarta tayi duhu gabaki daya ga gashinta duk ya zama abin tsoro da qyama, Suna barin gurin tenya ta aika baiwa ta isarwa da wishmah sakon Zuhrah ta fito kurkukun da babu komawa insha Allah har karshen rayuwarta. Sakon yana isowa wishmah Lumshe idanuwanta tayi ahankali tareda silalewa qasa tana bin bango ta zube qasa tana bude idanuwanta Akan sakinah data riqeta tanason magana ta kasa sai kawai ta sake rufe idanunwata tana dora hannunta daya Akan kirjinta dake mata radadin azabar da har abada bazai dena ba sai ranar da ranta yabar jikinta dan kuwa baqin ciki ne da quncin da baida magani. Sakinah da samun yancinta bai saka taji zata iya barin Ayanaah ba har abada itama sanyaye jikinta yake hakama ta shirya zama baiwar Ayanah har qarshenta ko da yanci ko babu yanci zata bauta mata ta kuma bauta ma ‘danta har girmansa. ******acan tenya kuwa Kai tsaye bangaren gyara ta isa da Zuhrah ta fara bada umarni aka wanke Zuhrah tas aka ringa cire datti harma da wasu qananun qwari a jikinta tsawon kusan wuni guda, Taso a yanke gashinta amma sbd imebeti zaa turata tana buqatan dogon gashin dan haka sai aka barshi shima ya ringa Shan wanki kan wanki, Ana gamawa gyaran kafafunta da hannuwanta akai na farce tukuna aka kirawo likitoci suka duba lafiyarta, Magani dasu multivitamins aka bata sai kuma tenya data bada umarnin aka hado mata mai na gargaji dayake goge tabo a qanqanin lokaci dan goge tabon raunikan data yiwa kanta duk da sun warke sun fara bace wa da disashewa saura dakan Wanda shine kila bazai fita ba sai sun hada masa da magani. Har dare sosai tenya bata huta ba tana kan lamarin Zuhrah da babu wani lokacin batawa matiqar tanason jefata a matsayin imebēti tana buqatar tsayuwan gaske a gurin gyaranta. Ayanah kuwa a nata bangaren tinda Zuhrah ta fito sai taji jikinta yayi sanyi ta sake raunana da komai, Ta bawa sakinah dukiya me yawa Akan ta tafi ta samu yanci tayi rayuwarta amma sakinah Sam bazata iya barinta ta kafe zata zauna da ita har karshen rayuwa, Batada Sauran walwalan daya rage mata kokuma shaawar rayuwa dan haka bata takura sakinah dinba dan kuwa daman ita kadai ce a yanzu ta rage mata a asalin rayuwarta hakama tana buqatan Wanda zai tsaya mata ya tayata bawa danta kariya duk da ta zabar masa yancin zabar abinda yakeso da kansa ba tirsasawa tin yanzu Akan mulkin datake tsoron kada a illata mata shi akai, Hakaman tayi hakan ne dan basa kariya daga masifu da hadarin da zai fara fuskanta ta ko ina tin yana jinjirinsa so yanzu zaa bar mata shi yayi rayuwa a cikin aminci tinda an riga an cika mata wannan alkawarin sai kuma idan ya girma idan yanada raayi hakan zai zama barazana ga Maqiyansa da masu so. A bangaren sultan YASAR kuwa Ayanah ghaz tayi masa babbar sukar data rage mata matsayi a zuciyarta dan kuwa duk irin soyayyar da jinin BOYEM zaiwa mace baya taba sauya abinda yake yawo a jininsa dan ako Yaushe harkar mulkinsu da iko tareda abinda suke Buri yana gaban kowace irin soyayya da kauna, Duka shekarun daya Debo na tsananin burin samun ‘da namiji sbd hakan ne, Sbd tabbatarda magaji Akan karagarsa bama batareda ko yanada raayi ba ko bayada raayi amma a Karan farko na tarihin masarautar ta zabawa ‘danta kaddararsa tin yana zanin haihuwansa, Yanada wani magajin Bayan NUAB da zai iya gadon karagar amma abinda tayi masa ya sakasa Jin ko zata rasa ranta sai ‘dansa da yayi raayi ya mulki BOYEM koda hakan na nufin fizge ta daga matsayinta sedai amma zuciyarsa na kasa barin sa ga aikata hakan dan kuwa kaman yanda jinin BOYEM da bazai taba barin burinsa ba yake a jininsa haka soyayyarta take a jininsa dan haka idan bazai iya cireta a zuciya da jininsa ba to zai iya cireta daga dukkanin qudurinta da bazai taba cika ba. Haile a yanzu ne ta samu damar sassautawa zuciyarta ta fara Neman lafiyarta da gaske dan kuwa a yanzu ta samu tabbacin tanada dama me karfi ta qwatowa ASIM matsayinsa da aka bawa ‘dan mistress, Bazata taba hutawa ba ko samun bugawan zuciya daidai har abada idan ba ganin ASIM BOYEM tayi ba Akan kujeran mulkin BOYEM, Batada Buri ko kudirin daya wuce saka ASIM a zuciyar sultan YASAR fiyeda dan mistress dinsa, Zata tabbatar ta dawo da matsayi da ikonta a hannunta na juya rayuwar kowace macen datake imebētinsa, Zata ninka tsoronta da zafinta akansu ta yanda bazasu taba iya kallan Ayanah da ‘danta da darajar data wuce mistress ce da dan mistress dan kuwa a yanzu ne zata tada asalin rashin imaninta Akan abinda takeson ‘yayanta su mallaka, Ko rai nawa zata kashe batada shakka zata kashesu tamkar dabbobi sbd saita tabbatarda Ayanah ko kallan inda take babu me yi bare bata girman matsayin datake dashi. ****Burika ne suka cike zukatan dukkanin masu jinin sarautar BOYEM Wanda hakan ya fara bayyanarda wasu manyan Zafafan hadari da rayuwa zata fara fuskanta dan kuwa a qanqanin lokaci kadan bayin Ayanah uku suka rasu batareda ansan menene yake ajalinsu ba amma kuma masu bincike sun tabbatarda koma menene kaman poison ne, Wannan lamarin shine ya fara daga hankalin tenya da sakinah harma da sauran imebētis kowa ya shiga mummunan tsoro da firgici, Ayanah bata shiga damuwan komaiba sbd rayuwarta data gama mutuwa ayanzu kwata kwata bata San komaiba Bayan qunci da baqin ciki se kadaici dasuke cin lafiya da hankalinta ahankali ahankali batareda sanin kowa ba, NUAB ne kadai Wanda take Zaunawa ta rungume tana kallansa batareda kyafta wan ido ba tanajin akansa ne kadai take rayuwa yanzu, A duk lokacinda take kafesa da ido tayita kallansa rabin jikinta Abaas ne kadai take ganin fuskarsa Akan tasa yana yawo kewa da tsananin sonsa na tsananta ciwon dayake cin zuciya da ruhinta dan hakanne a yanzu Abaas kadaine zuciya da rayuwarta take nema. Tenya na cikin matsanancin tashin hankali da rashin nutsuwa mai yawan gaske da duk ta firgice itama sosai sbd hankalinta daya rabu biyu Akan kulawa da Zuhrah datai wa Ayanaah alkawarin saita tabbatarda ta miqa rayuwarta inda zata rayu cikin aminci kafin ta huta da kuma hadarin datake ganin yana kusanto Ayanah da ‘danta dan kuwa komai ya rikice ga dukkanin imebētis din dake masarautar sun koma tamkar yan amanar HAILE duk abinda ta sakasu shi sukeyi sun bayyanar da tsanarsu me karfi Akan Ayanah da ‘danta, A bangare daya ma kaf ‘yayan da suke na sultan tsana me karfi sukewa NUAB da Kai tsaye suke ambata da ‘dan mistress kaman yanda HAILE da kanta take kiransa, Duk wannan abin Ayanah batasan anayi ba sbd bata cikin cikakken hankalinta na tinanin kowa Bayan na danta da kwanakin dake qaratowa na rabuwa da yar uwarta da bata saka a ido ba kuma shikenan bazasu saka juna a idonta. Tenya sake dage wa tayi Akan aikinta Wanda a yanzu Zuhrah ta sauya sosai tamkar ba ita ba tayi Wani irin Kyan gani da haske sosai duk da haskenta bai dawoba amma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106