Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 77

Chapter 77

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da sultan suke gani tinda bata gabansa babu abinda yake gabansa nata likita dayane tinda ya nadasa mai duba lafiyar Ayanah din shikenan baitaba fasa zuwa bibiyan lafiyar taba koda Yaushe a tsawon shekarun nan, ‘Ammi’ ya Ambaci sunanta cikin sanyi da kauna me girman gaske tareda nutsuwan da bayason damar da ita sbd jinta shiru. A sanyaye ta sauke bayyananniyar Numfashi jikinta gabaki daya a mace ta bude Baki tace ‘NUAB,Yene HAYATEEM,Yene LEUL idanuwana suna son ganinka, Zuciyana da ruhina duka san ganinka sukeyi kafin na…..’ Katseta yayi da tsananin nutsuwa da cewa ‘AMMI’ sbd yasan kalman mutuwa ne zata qarasa dashi, Tsigar jikinsa ne suka sake tashi a hankali Wani irin yanayin da mahaifiyarsa ce kadai ke motsa zuciyarsa na ratsashi sbd ya tabbatarda akwai abinda yake damunta ko zuciyarta dayayi girman datake buqatan ganinsa harta furta da bakinta, Dole wata damuwarce take faruwa da kila batasan tayaya zata iya gane wa ko fada masa ba kawai ta buqaci ganinsa sbd zuciya da ruhinta su sanyaya, Numfashi mara sauti ya kuma saukewa tareda dagowa idanuwansa farare tas masu Kayar da gaba da suka sauya a take suna dan rikida da ja ya bude Baki a natse yace ‘Ammi bakida lafiya ne? Girgiza masa Kai tayi a hankali da sanyi kaman yana kusa da ita Wanda sautin ya shigar masa kunne a cikin sanyi dan haka ya rufe idanuwansa ahankali ya kuma bude su yace ‘Akwai abinda yake damunki Ammi? Nan ma girgiza Kai tayi a natse batareda tinanin ba lallai ya fahimta ba, Nan ma yaji Gyada kan sbd akwai yan kunnen zinari masu dan fidda sauti kadan a kunnuwanta Wanda ya saka idan ta girgiza Kai sautin su ke shiga kunnuwansa suna narkar da zuciyarsa da babu abinda take tsananin so da kauna a duniya idan ba ita din ba ‘Ammi akwai Wanda ya saka miki damuwa’ Girgiza Kai tayi ya sauke Numfashi me sauti wannan Karan ya bude baki zaiyi magana muryanta ta Katsesa a sanyaye tace ‘Idan zaka taho kazo da Abaas,ina son ganinsa HAYATEEM’ Rufe idanuwansa yayi a Wani irin yanayin da zuciyarsa ke cizo da radadin kasa bawa macen da ita kadai ce rayuwansa abinda takeso sama da shekaru masu yawa. ‘Ammi zan taho gareki ba tareda Abaas ba amma nayi miki alkawarin indai Abaas yana raye zan kawo miki shi a gabanki, Nayi miki Alkwarin indai Abaas yana raye zan Nemo miki shi zai qarasa rayuwarsa a gabanki bazai taba barin gabanki ba har sai mutuwa ta rabaku….. Wasu hawaye ne suka gangaro idanuwanta da suka saka hankalin sakinah dake tareda ita a palo Zaune tashi sbd bata kuka Sam a yanzu sbd kuncinta da baason ya dawo dan haka a natse ta iso gurinta ta zauna gefenta ta kalli wayar hannunta ta miqa hannu tace ‘Nima zan gaisa dashi’ Miqa mata wayar Ayanah tayi cikin nutsuwa tana cewa ta yadda da NUAB zai cika mata wannan alkawarin ko Bayan ranta ne zai nema Abaas. Maganar tata har kunnuwansa ta sauka ta shigesa a hankali ya Lumshe idanuwansa yana Jin wata wuta mai Zafin gaske tana kunnuwa a zuciyarsa ta son kasancewa da mahaifiyarsa da tabbas lokaci yayi da zai dawo da ita hannunsa dan kuwa daman magana daya ce duk ranar daya saka kafa a BOYEM to bazai taba tafiya batareda mahaifiyarsa ba, Babu me buqatarta a masarautar da qasar gabaki daya hatta Wanda take zamansa baya buqatanta ya watsar da ita tin tanada kuruciya dan haka shi babu abinda yake buqata a rayuwarsa sama da ita a basa ita kawai shine cikar duk wani burinsa na rayuwa Bayan hakan baya buqatar komai a rayuwarsa. Saukar muryan Maa sakinah a kunnuwansa ya sakasa bude idanuwana jajir yana bude baki a natse da kulawa yace ‘Maa akwai abinda yake faruwa ne?? Akwai abinda ya kamata na sani ne?? Amminah na da damuwa ne? Akwai abinda yake faruwa a masarautar ne daya taba Amminah? A Jere ya jerowa Maa sakinah tambayoyin da suka saka jikinta sanyi ta sauke ajiyan zuciya mara karfi tareda bude Baki cikin nutsuwa ta manyanci tace ‘Babu komai dayake faruwa kawai dai yanayi ne na kewanka datake yi shine kadai ya saka amma ka damu babu abinda yake faruwa’ Shiru yayi itama Maa sakinan yana karantar yanayin muryanta datai sanyi sosai, Kai tsaye yace ‘Maa akwai abinda yake damunki kema? Menene yake faruwa a masarautar nan? Waye ya tabaku? Katsesa tayi da sauri tana kokarin daidaita kanta cikin sauti da dan sauri sbd Jin yanda muryansa ta fara sauyawa tana daukan Zafi da fushinsa da babu me iya kashe wutarsa tin yana yaro tace ‘Babu komai Ka yadda da hakan LEUL,kada Ka bata ranka ko kadan dukanmu muna cikin kwanciyan hankali da lafiya’ Kasa nutsar da zuciyarsa dake daukan zafi yayi ya bude Baki cikin sassauci yayi sallama da ita Kai tsaye wayar Maa tenya ya kira yana bude idanunwansa da sukai jajir Akan Agogon dayake palon dan kuwa matiqar yaji ya tabbatarda akwai damuwan dasuke ciki babu abinda zai Hana jirginsa sauka BOYEM kafin fitowan alfijir din asubar gobe. Maa tenya dake dakinta ta gama sallar nafila wayarta dake kan marble center table din dayake lafiyayyan dakinta da babu duniyar da babu a cikinsa koina na Qamshi da sanyin ac tafara ringing. Hannunta ta miqa a sanyaye ta dauki wayar tareda dauka ta Dora a kunnanta cikin sanyi tayi sallama tana miqa masa gaisuwan data zama kaman dole kasancewansa jinin BOYEM kuma asalin magajin karagar mulkin. Bai amsa gaisuwan sarautarsa ba ya miqo mata tasa gaisuwan ta zamanta uwa a garesa kafin ya Dora da cewa ‘Maa idan akwai abinda yake faruwa ki sanar dani sbd ina rasa hankalina anan sbd Amminah akwai abinda yake damunta kuma Inason saninsa koma menene’ Ajiye Numfashi me sauti sosai tayi kafin ta sake shiga sanyi da nutsuwa tace ‘Allah ya qara maka lafiyar zuciya LEUL BOYEM Amminka jikinta yana Neman dawowa sosai a kwanakin nan rikicewa kawai lafiyarta ke kokarin yi Wanda tabbas tana buqatan ganinka takeso kafin ta qarasa rasa cikakken hankalinta ta manta waye Kai………. Shiru da tsit yaji duniya gabaki daya tana masa sai yanajin muryan Maa din tamkar sautin dayake tahowa daga nesa sbd straight zuciyarsa labarin ya caka yanajin dumi na gauraye jikinsa koina musamman idanuwansa da sukai jajir. Kasa iya cewa komai yayi sai sallama da yayi mata yana kashe wayar idanuwansa na tsananta ja ya da dago ya saukewa aleey su dayake tsaye gefe yana jiran umarnin koma menene yakeson Ayi. Kallan da yayiwa aleey Wanda ke kallansa cikeda nutsuwa da girmamawa take aleey ya fahimci umarnin sa dan haka Kai tsaye cikin girmamawa da cika umarni yace ‘Aiit B’ iPad din hannunsa ya daga yafara dannawa yana fidda wayar sa itama ya saka kira yana Juyawa yabar gurin yana fara aikin da baya buqatan bata lokaci dan kuwa kome zai tsaya cak sai LEUL BOYEM ya isa fadar da tasa ce gabaki dayanta. Shi kuwa ajiye wayar hannunsa yayi tareda Dora kafarsa Ka daya a hankali yana jingina bayansa da kujeran dayake Zaune yayi folding hannuwansa duka biyu kirjinsa yana Lumshe idanuwansa ya rufe dan kuwa a yanzu komai na rayuwarsa ya tsaya cak har saiya isa yayi tozali da mahaifiyarsa wadda shekaru

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});