Chapter 22
Chapter 22
amma ba dama sbd alkawarin dayake kansu dan haka cizon harshensa yafara yana jijjiga Ayanah da karfin gaske. Ayanah da karfi itama ta kwala kiran Nurat din wadda kaman daga sama suka Ji saukan muryanta a tsakiyar kunnuwansu Ta kwalla qara me karfi tareda kiran sunan AMMA saida kunnuwansu suka amsa Amo zuwa kirjinsu musamman Ayanah datasan ita Nurat din take kira da Ammah. Saman dakin suka kalla da wani irin mafi girman firgici sbd jin baa cikin dakin take ba dakin dake samansu ne na shugaba khams… #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070 15 *JEWELRY JUNCTION* 08039440312 Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma, Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne?? To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan, Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana, ✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌 ✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌 ✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌 ✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍 🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah. WhatsApp 08039440312 Tiktok :@sokoto jewelry seller Instagram: jewelryjunction23 ************ Miqewa tsaye dukkaninsu sukai kafafunsu na kasa daukansu sosai sbd zaman dayake cinye lafiyar kafafun, Jijjiga da fizga jikin Ayanah yakeyi bama rawa ba ta bude Baki da karfin gaske Tana kwala kiran Nurat wadda take Ihun itama sosai. Abaas harshensa yake cizo yana wani irin gurnanin kiran Yar uwarsa a zuciya jini na fitowa bakinsa sbd mummunan tashin hankali da yanda yake cizan harshensa. Zuhrah Neman zarewa takeyi itama kaman Nurat Tana qwala kiran Nurat qafafunta na kasa daukanta. Sakinah ma kuka takeyi sosai zuciyarta na bugawa kaman zata fado, Miqewa tsaye Ayanah tayi cikin tsananin duhun tana kokarin taka mutane ta isa kofar ta kife sbd sarkar kafarta amma bata tsaya komaiba jikinta na tsananta rawa ta sake miqewa kwala kiran Nurat da karfin daye amsa dakin dukansa har sama inda Nurat din take Tana sake faduwa taba sake tashi tana taka mutane hankalinta gabaki daya ya gushe daga jikinta Ihun kiran Nurat takeyi Tana jin kaman mutuwa zatai a lokacin, Ihun Nurat dinne yafara ratsosu itama cikin tsantsar azaba tana kiran Ayanah da sunan Ammah muryanta ba dadin sauraro. Isowa setin kofa Ayanah tayi tafara bugawa da hannuwanta tana wani matsanancin kukan da ihu, Yanda take bugawa hannuwanta duga biyun da karfi batareda damuwa da yankewan da hannun keyi ba ga qusa dake jikin gurin Tana fasa hannuwanta jini na fita jin kawai takeyi tamkar ranta ne zai fita idan rayuwan Nurat dinta ta lalace. Kukan datake yi Sam bata hayyacinta sbd da a gabansu ne ake kokarin hakan da yau duka zasu bar duniya sbd bazasu tsaya kallo ba zasu qwaceta koda hakan na nufin rabasu da ransu. Jini sosai taje fiddawa a hannuwanta amma ta kasa denawa sbd bata ma Jin Zafin komai kukanta na qaruwa sosai har maqoshinta na kasa fidda sauti. Abaas da Zuhrah harma da sakina da suma kowa ke cikin mummunan Hali suka rarrafo basa gani zuwa inda sautin muryan Ayanah din yake fita Zuhrah ce tayi saurin riqeta Tana rungumeta sbd jinin dataji hannuwanta nayi data lalabo ta tareda fasa sabon kuka itama jikinta na fizga, Abaas ma Kansa yake bugawa a kofar yana wani irin kuka zuciyarsa na yagewa tako ina da radadi me yawa ga bakinsa bazai budu ba dai harshensa yake taunawa yana jini yana cigaba da buga Kansa a kofar, A daidai lokacin da Nurat ta qwalla wata mummunan qara wadda take tabbatarda azaba ce ta keta ta da akai da wasu irin surutai da khams ke sakewa a cikin kunnuwansu suna ratsa zuciya da kwakwalwansu take kowannensu ya silale qasa suna yin tsit sedai sakinah ce ta saki wani irin kuka a lokacin Tana riqe hannuwansu su duka ukun a cikin nata duka biyu sbd yanda suke jijjiga batareda sun iya sake kowane irin yunquri ba alaman zuciyarsu bugawa zatai ko ta dauke wuta, A cikin kunnuwansu sautin duk abinda khams keyi yake sauka tareda kukan Nurat dake fita har tayi tsit babu kowane irin sautinta sai nasa Wanda duk abinda yayi da ita kunnuwansu sunji musu Wanda kuma sauti ne da zai zauna a kunnuwansu da zuciyoyinsu har abada har ranar da jinsu zai dauke Bayan rai ya fita a jikinsu, Zuhrah juyewa kanta yake yi itama sbd dukan da zuciyarta ta samu mummunan dayake Neman buga zuciyarta. Sakinah rungumesu tayi da hannuwanta Tana qanqamesu kukanta na tsananta sbd yanda dakin yayi tsit kowane bawan dake jirgin ranar duk da halin da suke ciki kukansu Ayanah din ya sanyaya jikinsu tareda hawayen tausayin qaddadarsu su duka da basusan ya zata qare ba. Ayanah zubewa tayi jikin sakinah gabaki daya jikinta na saki idanuwanta na kasa Juyawa ta koma kamar wadda aka zarewa komai aka Barta da rai kawai. Jin hakan sakinah ta sake rungumeta jikinta kukanta na tsananta Tana Jin inama a ranar da suka so kashe kansu ta barsu sun mutu sun bar duniyar da sun huta da ganin wannan balain da daace iyayensu na raye mutuwa zasu yi idan suka Ji wannan mummunan ranar. Tsit babu Wanda ya iya ko dogon motsi a dakin kwata kwata kaman yanda babu Wanda ya sake Jin ko kukan su Ayanah ne dukansu sun mutu a inda suke babu abinda ke motsi a jikinsu Bayan zuciya dake bugawa. Gap da asuba aka bude dakin Wanda ya saka su Ayanah daga Kai ahankali suna kallo aka turo Nurat wadda Kayan jikinta gabaki daya suke a yage harma kusan Rabin jikinta duka a bayyane. Abaas ne ya Tara hannuwansu biyu ya tareda ta fado jikinsa ya rungume ahankali yana rufe jikinsa ta inda jikinta yake bayyane yana sake rungumeta tsamtsam. Wasu hawaye ne masu dumi suka gangaro daga idanuwanta Wanda ya sauka tafin hannuwan Zuhrah data motsa zata tabata, Saukar hawayen nata ta saka Zuhrah kallan fuskanta cikin duhun bakinta na budewa da tsananin sanyi tace ‘Nurat,Yene(my/tawa) Nurat,Yene fikir(love/masoyiya) Nurat Rabin Raina.’ Wasu sabbin hawayen ne suka gangarowa Nurat din Tana son Dora hannunta Akan na zuhrah din ta kasa dan haka ta rufe idanuwanta bakinta daqyar ya iya budewa tace ‘Ammah’ Kalmar yanka zuciyar Ayanah da dukkaninsu tayi Ayanah ta rufe idanuwa hawaye masu tsananin zafi suka gangaro mata ta motsa hannuwanta dake rawa ta Kai fuskar Nurat din taji wani abu yana gangarowa ta hancinta Wanda ta tabbatarda jini ne yake fitowa ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106