Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wannan ukubarba bazai taba magana aji sautinsa ba na namiji dan haka daga lokacinda ya aka saiya jinsa zuwa na mace ya koma kurman da baya magana sedai nuni. Wasu irin hawaye masu Zafin radadi a ido da zuci ne suka gangaro masa na tsananin azabar dake ratsashi gashi shi ya kasa somewan. Bulala aka daga me kaurin gaske ta fatar dabba aka zabga masa yayi daurin rintse ido numfashinsa na sarkewa akace ya tashi. Da rarrafe ya koma gefen wainda akaiwa Shedan numfashinsa har lokacin na kokarin yankewa hakama yanason fasa kukan azabar dake ratsashi amma fitan sautin kukansa zai bayyana sautin muryansa datake da dan kauri ta maza dan haka haka yaci gaba da danne azabar yana hadiyewa jikinsa na wata irin muguwan rawa. Zuhrah ma dake Ihun gigitacciyar azaba har lokacin bulala me Zafin datakai azabar wutar aka sakar mata wadda ta sakata sakin qara me rikitarwa Tana rarrafawa gurin Abaas nenam dauki. Ruwa aka watasawa su Ayanah da Sauran bayin da suka some Ana dukansu da Bulala a haukace suke rarrafawa gefe suka fadawa kan yan uwansu. Sakinah ma bata some ba amma tashiga kidima da fitar hayyaci azaba, Nurat duk rashin hankalinta kuka takeyi sosai na azaba Tana nunawa Ayanah hannunta dake tsananin radadi. Hawaye Ayanah ke fitarwa Tana rungumesu cikin azaba da wahala me tsanani suna dauriya da karban wannan sabuwar masifar da suka samu kansu kuma a ciki. Ana gama kirgasu aka fara raba musu Abinci suna karba Ana wucewa dasu dayan dakin da Sauran bayin duka suka ciki sama da daruruwa masu shegen yawa. A yunwace suna jin azaba suka hau cin abincinsu Bayan sun Nemi guri sun rakube a cikin dakin, Ana gama shigo da kowa aka rufe kofofin dakin dake sama take dakin yayi duhu nan take kuma aka fara ihu da kuruwa tareda hayaniyar kokuwan masu karfi da marasa karfi gurin qwacen abinci. Cikin tsananin sabon tsoro su Ayanah suka qanqame juna suna hadewa guri daya take sakinah ta tura Abincinta duka a baki tana hadiyewa tace suka Suyi hakan. Tura abincin sukai gabaki daya a baki suna hadewa cikin azaba da wahala yana yankar maqoshi amma haka suka Hadiye. Kafin kace me gurin anji wa sama da Mutum Hamsin rauni wasu ma a qonuwarsu aka raunatasu. Su kansu Ayanah sunsha duka da shuri na mutane kafin dakin yayi tsit Angama kokawar. Wani Daren ne ya tsala sosai koina yayi tsit duk da basa gane dare bare rana sbd duhun inda suke dan amma shirun ya tabbatar da Daren yayi. Babu Wanda ya samu bacci a cikinsu shiru sukai zuru a jikin juna har lokacin suna maqale, Zafin zazzabi me karfi ne ya fara saukarwa Nurat har tana dan fizga Hakan yasa Ayanah rungumeta a jikinta Tana Shafa bayanta Ahankali, Itama zazzabin take fama dashi sosai amma bata kwantaba sedai jikinta da yayi Wani irin zafi sosai. Zuhrah ma zazzabin ne ya sakata zame wa ahankali ta kwanta da jingina, Abaas ma karfinsa lamarin yaci ya bangare a gurin idanuwansa na rufewa jikinsa na rawar zazzabin. Sakinah duk abinda suke Ji tana jinsa amma haka ta daure ta taya Ayanah kulawa dasu duk da babu abinda zasu iya ko suke musu Bayan Shafa bayansu dan basu sassauci koma yayane. Gari na wayewa tinda Sauran duhu aka bude kofa aka diba Mutum hamsin aka fice dasu zuwa aiki. Dayan dakin suka wanke me tsananin girma tareda aikin tsafta ce duka Sauran koina dake jirgin, Suna aikin suna Shan Wani irin dukan azaba a haka suka gama aka dawo dasu kafin aka fara jeho musu abincin safe Bayan rana ta dade da yi kenan. Haka suka wuni cikin duhu da azaba har wani Daren kafin aka sake basu abinci Wanda kullum so biyu ko daya ake basu abinci. Fitsari da kashinsu kuwa anan suke yinsa a cikinsu cikin wata qatuwar durum wadda aka ajiye a karshen dakin cikinsu sai da safe ake sakasu kwasarshi suna zubarwa a iska dan haka a cikin mugun wari da qarni da Zarni suke kwana suna wuni. *******ahankali ahankali su Ayanah suka fara fuskanta da yadda da wannan rayuwar fa itace yanzu zasu yi har karshen rayuwarsu dan haka duk muninta haka zasu karbi kaddarar rungumarta su koyi yinta, Hakan ne ya saka suka fara sabawa Bayan sunyi ciwon,sunyi ciwon amma gangar jiki tafara sabawa da duka da wahala, Hakama hanci da hanjin cikinsu sun fara sabawa da wari tareda manta akwai kamshi a rayuwa, Idanuwansu da zuciyoyinsu sun saba da duhu da qunci sbd a cikinsa suke rayuwa dip Baka ganin ko dan uwanka dayake kusa dakai Shiyasa su Ayanah basu taba yadda sun matsa ko inci dayaba daga junansu, Ko lalurar zagayawa Fitsari ko abinda ya fisa ya kamasu tare suke zuwa da sarka a qafafunsu su jira Wanda zeyi su gama su dawo tare, Sunayin hakan ne na zuwa gabaki daya dan bawa Abaas kariya daga tsautsayin wani ya gansa. Rayuwar bauta sun Riga sun samu kansu a cikinta dan haka yanzu basuda Sauran Buri Bayan Allah yabar su tare suyita bautar a tare da junansu. Ahankali yunwa ta fara barin jikinsu duk da ci daya ko biyu suke samu a rana amma sbd suna samu din dai dakuma Zaune da suke guri daya ba rana sai suka fara rage mummunar kamar aljanu da suke cikinta amma ita datti da wahala a jikinsu har lokacin qaruwa ma takeyi ba raguwaba. Duk wannan rayuwar da suke Abaas ya zama Kurman da gaske bai taba magana ba koda tsautsayi komai wuya kuma baya fidda sauti haka yake hadiyewa musamman idan Ana dukansu bai taba fidda sauti ba ko su yan uwan nasa yanzu da hannu yake musu magana duk da magana ba basu cika yiba sbd baqin ciki da qunci rayuwa daya gama cike zukata da bakinsu babu abin fada sedai ido. Tafiyar Sati hudu sukai a cikin ruwan kafin jirginsu ya sauka a wata babbar qasar da zasu tsaya su siyar da wasu qalilan daga bayinsu dan siyan Kayan abinci su zuba a jirginsu tukuna su wuce dan haka zasu yada zango anan na kwanaki kafin su wuce. #MAMUH #SLAVERY #ROYALTY #BOYEM #AYANAH #YANAH #BEST LOVE #BEST STORY HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 09033181070 13 *JEWELRY JUNCTION* 08039440312 Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma, Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne?? To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan, Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana, ✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌 ✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌 ✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});