Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 67

Chapter 67

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ita a daidai lokacinda zaa fara tana dauke da NUAB a hannunta. A bisa dolen al’adah sai matansa sun fito sune zasu tarbesa su rakota a tare har inda yake dan haka koda akai sanarwar isowanta kofar fadar tareda bayinta da securities din dake tsare da NUAB da jakadiyarta take HAILE ta Hadiye wani kakkarfan busashen yawun daya saka hannunta rawa tana yagar fatar Dayan hannun nata da karfi yana yagewa, Cikin sauri da basarwa Aslam dake kusa da ita ta Dora hannunta Akan hannun mahaifiyar tata tareda dan kallanta a natse tana girgiza mata Kai kada kowa ya gani. MARAKI ma dagowa tayi zuciyarta na daukan Wani irin nauyin zazzafan kishi mai tsananin ciwo da dumama jini ta zubawa AYANAH GHAZ idanuwanta tana kallan Wani irin fitinannen sirrin kyau daya saka kusan koina tsit sbd duk da tana rufe amma gyalan yayi shara shara din da babu abinda basa gani na halittar da Allah ya qera a gurin, Akan sultan MARAKI da HAILE suka sauke kallansu a lokaci daya zuciyoyinsu na shiga wani nannauyan kishin da babu wadda batajin kaman ta Hadiye zuciya a lokacin ta mace. Wani irin kallo ya dago fararen idanuwansa masu kyau da girgiza dan Adam ya saukewa AYANAH GHAZ daga lokacinda ta sako kafa a cikin fadar batareda ya kyafta ba dan kuwa duniya biyu ne aka hade masa guri guda a gabansa ita da NUAB datake rungume dashi suna tinkaro sa. Yan jarida da televisionsa da duk wani dan media suna gefe daya da aka ware musu sbd tsari da Kyan fadar daga can suke daukan hotinan da flashers kawai ake gani tana haskowa babu kakkautawa. Haile da maraki ne suka iso gefenta kowacensu da adonta mai kyau da tsari tareda daukan ido itama suka fara tako wa tareda da ita dukansu idanuwansu Akan sultan ta cikin nasu rufar Ayanah kuwa kanta a qasa shi kuwa nasa idanuwan Akan ‘dansa dake hannun Ayanah kawai yake kalla taqaita kallansa daga gareta hana kishinsu Kai illa ga zukatansu. Isowan AYANAH GHAZ gabansa suka zauna inda aka tanada dan zamanta da nasu take aka fara gabatar da kosher din Wanda yake tamkar daurin aurensu ne zaayi. Dukiyar kosher datake tamkar sadaki aka gabatar daga jinin BOYEM na manyan cousins din sultan dake qasashe daban daban suna rayuwar mulki da daula tareda hutawa a qasashen turai daban daban dayake dik jinin BOYEM indai suna raye ko a ina kake Ka Halarta dan haka masarautar take shaqe da masu duniya a hannunsu. Irin dukiyar da aka bayar ya saka masarautar jijjiga take aka karba dukiya aka bawa jakadiyarta sbd itace gatanta wadda kadai take da ita aka fara adduar kosher din tsawon lokaci kafin aka rufe da Amin Wanda Amonsa sbd yawa ya ringa amsawa har wajen Masarauta. YUNAR KAREEM ALMAZZ BOYEM Shine babban dan wan mahaifin YASAR Wanda yake Zaune a qasar Kuwait da matarsa daya da Yaya uku sai yaya hudu daga imebētinsa daya dan haka shine ya isar da cika Burikan wishmah guda uku Wanda Kai tsaye budar bakinta idanuwanta a kafe kan NUAB dayake kan kafafunta muryanta na tsananta sanyi da karfin Hali tace Abu na farko datake so shine a yanta bayi dari a cikin bayin dake kurkukun masarautar, Sai Abu na biyu shine tanason a ‘yanta mata baiwarta daya tak sakinah, Na ukun shiru tayi zuciyarta na yin Wani irin rauni da sanyi ta dago idanuwanta da sukai ja ta saukesu Akan sultan tace tanason ko tana raye ko baya raye idan NUAB ya girma kada a tirsasata hawa mulkin Masarautar BOYEM matiqar baida raayi idan ba shine yayi raayi ya hau dan raayin Saba. Tsit kowa yayi koina ya dauki Wani irin shiru mamaki na kashe kowa musamman sultan da HAILE da Wani irin sanyi a Karan farko ya dan ratsa zuciyarta ta kafe Ayanah din da ido tana mata kallan mahaukaciyar data rasa tinaninta dan kuwa batada labarin cewa tinda ta fada wannan burin saiya cika koda zata mutu Akan sauya hakan, Tayaya zata ce idan danta baida raayi kada a basa mulki? Ta kuwa san menene samun mulkin Masarautar BOYEM? Sultan kuwa kafeta yayi da idanuwansa Wani irin daci mai karfi yana Sosa zuciyarsa dan kuwa tamkar Kai tsaye ta kallesa ta yaga burinsa daya kullata koda zai mutu ne ta yaga a gaban idonsa, A matsayin datake dashi harta isa samun wannan tinanin? Menene nufinta na fara lalata burinsa Akan dansa tin yanzu? Tabbas tayiwa burinsa na shekara da shekaru tabon da har abada bazai goge ba musamman idan abinda ta fada din ya tabbata. Manyan fada dik da shock din da suka shiga take aka sanar babu burinta da baama gama cika wa dan haka take aka bada umarnin a saki bayi dari biyu ma da suke kurkukun, Sakinah ma take aka yantata tareda kyauta me tarin yawan data saka Ayanaah din rufe idanuwanta ahankali hawaye masu dumi na gangaro mata sbd samarwa sakinah yancin da sukam bazasu samu ba har abada. Har tsakar dare sosai Ana hidimar sai kusan gap da asuba aka gama kowa ya watse zuwa masaukinsa. Washe gari da sassafe aka saki bayin da akace a saki, Koda aka fara fitowa dasu tenya na bakin kurkukun dan cika sabon aikin daya hau kanta na hadawa mai girma YUNAR BOYEM sabuwar imebeti a matsayin tukuicin dukiyar kosher daya bayar ta wishmah daga mai girma sultan YASAR, Tin farko tasan daman zaa bada tukuicin imebeti ga duk Wanda ya bada dukiyar kosher din wishmah a matsayin tukuici Shiyasa ta fadawa Ayanaah sadaukar da zatai na rabuwa da Zuhrah har abada sbd ita zata bayar dan hakanne zaisa itama ta samu rayuwar da har zata haifa nata yayan amma sun yafe juna kenan har abada sbd daga ranar da aka gane jininsu daya duka su biyun zasu rayuwarsu matiqar ba yayansu sunyi girman da zasu sassauta musu hukuncin hakan ba kuma a yanzu Ayanah ta yadda da hakan matiqar zasu rayu Zuhrah ta Gina tata rayuwar harma zuriar kanta, Hakanne ya saka tenya take tsaye a lokacinda aka fito da Zuhrah wadda ta fita kamanninta gabaki daya Kai tsaye gurin duba lafiyarta tasaka aka wuce mata da ita dan shiri da gyaran gaggawa zaa fara yi mata na tsawon wata daya cif kafin a Kai masa ita ya wuce da ita qasar kuwait. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 44 A daidai lokacinda Zuhrah ta sako kafarta wajen kurkukun fata shafe Sheka daya da watanni a ciki a daidai wannan lokacin Ayanah ghaz datake tsaye zuciyarta na Wani irin harbawa da Wani irin zallan kewar datake ratsa ruhi da zuciyarta kafafunta na dan rawa tanaji a jikinta Zuhrah na cikin halinda itama take tsananin son ganint su shaqar da rahamar ganinsu. Sakinah dake tsaye gefen Ayanah din itama zuciyarta cike take da yanayi na sanyi da mutuwar jiki tareda tsananin so da kaunar ganin Zuhrah wadda shikenan wannan Karan sun rasa juna kenan da gaske har abada. Tenya ma dake tsaye wajen kofar kurkukun zubawa Zuhrah idanuwanta tayi babu kyaftawa tana Jin tsananin tausayin Ayanah da zata iya rasa ranta idan taga Zuhrah a halinda

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});