Chapter 39
Chapter 39
Basu wani rintsa ba da damuwa me nauyi da sanyin jiki suka gama komai suka fito zuwa aikinsu. A kaidar zabar imebēti daki daki ake bi dan haka Layi bai iso bangaren imebēti faree ba Sai dare Wanda tenya ce da kanta tareda bayinta kusan su goma biye da ita cikin nutsuwa da taqama da wani irin kwarjininta ta iso take dukansu suka zube qasa hadda faree wadda itama kanta yake qasa sbd ten’ya kwarjininta nada nasaba da matsayin datake riqe dashi na ita kadai ce takeda power ta zabawa sultan macen dazai kwanta da ita,ita kadai ce takeda power ta zabar wadda zata iya daukan cikin sultan ta haifar masa ‘yaya kuma itama tanaji a jikinta insha Allah a cikin zabinta ne zaa samu macen da zata kafa tarihin haifar LEUL na wannan zamanin dan hakanne ma wannan Karan mata shida zata zabar masa lokaci daya yana dawowa saiyayi sati kullum yana Bare sabuwar mace. Kai tsaye idanuwanta ta sauke akan fuskokinsu zuwa daya bayan daya tana binsu da kallan nutsuwan da kyau ne zalla take gani a tattare dasu sedai kowacensu babban tabo ne a Fuska,wuya da hannuwansu, Batace komaiba ta zubawa faree ido tana karantar yanayinta kafin ta maida idanuwanta akan tabonsu dayake nuna wuta ce a jikin kowannensu, Kyansu ta sake kalla da kyau take ta fahimci komai ta tabbatarda meya faru dan haka kai tsaye akan Ayanah ta tsayar da idanuwanta wadda kanta ke qasa. Cikin bayinta ta kalli daya kai tsaye wadda ta fahimci me take nufi take ta matso gurin Ayanah ta saka hannu ta zare Hular kanta gashinta dayake dunqule take ya zubo ahankali yana sauka a bayanta. Faree da kanta ke qasa har lokacin wani mummunan yawu ta Hadiye zuciyarta na harbawa da karfe sedai kafin su dake jan Numfashi su fitar take ten’ya ta kalli Ayanah ta bude baki tace ‘Tashi ki bisu’ Ayanaah da bata gane me hakan ke nufi ba miqewa tayi ahankali tareda bin Bayan bayi biyu da akace ta bi tana adduar kada hukuncin da zaa yiwa su sakina daya saka akace ta tafi yayi tsauri. Tafi me dan tsayi kadan sukai suka isa wani babban guri nai shegen kyau da tsari Wanda a cikinsa zaa yiwa duk macen da aka zaba gyaran fitar hankali na ciki da waje na wata daya. Tana saka kafarta cikin gurin taga mata a jere tsaye gabanta yayi mummunan faduwa ta tsaya cak tana kallan gurin da idanuwanta Wanda ke fahimtar da ita menene yake shirin faruwa a gurin. Kasa daga kafarta tayi sbd toshewan da kanta ke Neman yi ta juyo ahankali ta kalli wainda suka kawota zatai magana numfashinta ya dauke cak bakinta ma kafewa yayi komai nata ya Dena aiki ya tsaya cak sbd idanuwanta da suka sauka akan Zuhrah da aka shigo da ita itama…… #MAMUH #BEST ROYALTY STORY #BEST LOVE #LOVE/ROMANCE HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 26 *_UMMU ASLAM COLLECTION_* 08035014107 -Ina mata yan kwalisa masu son burgewa? -Shin Kayan kitchen na zamani masu sauki da rahusa na kitchen din yan gayu dama na gargajiya kike so? -shin abayas na yayi da daukan ido da burgewa kike nema? -kokuwa original misk dahara kuke buqata dan asali? -kokuwa Kayan GHT na Neman lafiya da gyara kike so? -ke harma laces da atampopi na alfarma masu sauki kikeso? To duka kinzo gidansu indai sune abinda kike buqata ba bata lokaci kinzo kin gama samu kawai tintibi UMMU ASLAM COLLECTION 08035014107 duk inda kike zata aika miki. *********** Dauke wuta kafafunta suma sukai maqoshinta na wata irin bushewa qayau yawun bakinta suma suka dauke, Wani yaji yaji taji yana cike idanuwanta sbd tashin hankalin da baida ‘dan uwa a gareta, Zuciyarta kuwa harbawa take a kirjinta da mugun karfi da wani irin rauni dayake gauraye gangar jikinta na ganin Zuhrah Ayau cikin idanuwanta a Karan farko Bayan rabuwarsu kusan shekara guda, Ayau idanuwanta sun samu haske da rahamar da suka rasa, Ayau zuciyarta ta samu abinda ta rasa na haske da bugawa daidai Bayan shekara guda, Ayau dukkanin duhu da yanar dake zuciyarta sun haskaka da ganin gudan jininta ruhinta Zuhrah wadda itama Zuhrah dake cikin tsananin qunci da baqin ciki komai nata sakewa yayi da ganin Ayanaah dinta rayuwarta,kuzarinta,gangar jikinta,bugun zuciyarta harma ganinta sbd a tsawon wannan lokacin ita ko na minti daya bata taba walwala ko farin ciki ko misqala zarratan sbd da gaske Ayanah ce rayuwarta hakama bata tareda kowa da zai kaunace ta ko kulawa da ita ko Wanda zatai wa magana ko kalla taji sassaucin komai ita kadai take rayuwarta babu kowa a cikinta Wanda hakan ya taba rayuwarta da zuciyarta sosai harma da kanta sbd babu abinda take ako Yaushe koda da dare ne Bayan zubawa guri daya idanuwa tana ganin duka ahalinta a idanuwanta ba kamar Ayanaah ba datake tareda Sakinah, Ganin Ayanah a gabanta yau cikin idanuwanta ya gama cike dukkanin gurbin matacciyar zuciyarta da bugawa kadai takeyi babu abinda ya rage a cikinta, Ganin Ayanah Ayau ya farfado da rayuwarta dake gap da barin duniya sbd tana cikin tsananin qunci da azaba sbd a inda take babu sauki ko kadan ta rame sosai tayi Wani irin fayau alaman kowane lokaci ciwon dake zuciyarta zai buga zuciyarta ta tafiyarta itama, Kokarin gazawa kafafunta sukeyi dan mutuwan da duka jikinta keyi yana sanyi amma a hakan take daga kafafunta ahankali tana tako wa ahankali sbd wainda suke tareda ita, Qasa tayi ahankali da idanuwanta a daidai lokacinda suka iso gurin da su Ayanaah din suke tanajin zuciyarta na Wani irin yanka da radadin dayafi na kullum babu abinda ruhinta da gangar jikinta da zuciya ke tsananin so a lokacin Bayan jin jikinta dana Ayanaah ya hadu sun rungume juna sunji dumin juna sun Ambaci sunan juna sun Shafa fuskan juna sunji muryoyin juna, Da zata samu hakan tabbas da ciwon dayake cin zuciyarta zai warke koda kuwa warkewan tafiya ce to tabbas zata so hakan, Ayanaah ma da zuciyarta ke wata irin bugawa kaman zata faso kirjinta ta fado sbd tsananin so da kaunar yar uwarta daya taso mata ahankali ta sauke kanta tana Jin kowane sautin takun Zuhrah na sauka kunnuwanta yana dukan kirjinta a lokacinda suke kokarin wucewa ta gefensu sunaji suna gani kowannensu ya sauke kansa daga kallan junansu, Rintse idanuwa Ayanah tayi ahankali wani radadi na sake cikesu suna yin jajir duk abinda ta juyo tayi magana akansa bace wa yayi daga kanta da tinaninta sbd ganin Zuhrah Ayau ya tsima duka abinda take danne wa da jurewa, Kamannin Zuhrah dinta sun sauya sosai ta koma tamkar ba ita ba duk da tayi haske sosai amma babu abinda kai tsaye yake bayyane a jiki da fuskanta sai damuwa da qunci me tarin yawan gaske da tabbas zata iya rasa ranta da bugawan zuciya, Bude idanuwanta tayi ahankali radadin cikinsu na qaruwa tanajin takunsu har lokacin a bayanta suna tafiya suna nisantar ta. Rufewa idanuwanta da zuciyarta sukai babu abinda take so Bayan sake saka Zuhrah a cikin idanuwanta dan haka ahankali ta juya batareda karfin jiki ba ta nufi cikin itama tana mantawa duka kwata kwata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106