Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 59

Chapter 59

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

son danta da rikicin qasar gabaki dayanta yake jiransa. A daidai wannan lokacin bangaren HAILE shima wani Tiriri ya dauka na samuwar cikar Buri dan kuwa itama namijin ne ta haifa Wanda ya sakata kokarin tashi da kanta dan isar da sakon haihuwar ‘da namijin ga sultan tin kafin Ayanaah ta haihu sbd farin cikin samun cikar burin shekaru ya mantar dashi Ayanah da kowa menene zata haifa. Hanata Miqewa likita ke kokarin yi tareda yarta harma da fetto sbd jinin da babu sosai a jikinta kuzari tareda azabtuwar datai sosai tayi pale sosai suka dage cikin tsananin kulawa da kauna dan komai ze iya faruwa da ita idan ta tashi tsaye amma Sam taqi yadda da hakan rungume take qam da babyn tana kokarin Miqewa zuciyarta a rufe bata Jin ko zata rasa ranta zata iya jiran Ayanah ta haihu batareda sultan yafara sanin ta haifa Zakin qasar BOYEM ba, Miqewa tayi suka miqe dukansu tareda riqeta zuciyoyinsu da hankalinsu duka a tashe da mugun tsoro da tashin hankalin hukuncin laifin da suke kokarin aikatawa na Binta su fita, Wani jinin ne ya kuma gangarowa daga qafafunta Wanda ya saka hankalinsu sake tashi dake sauri bayi biyu sukai saurin durqusawa suna goge mata jiki da towel me dumi da suka matse daga ruwan Zafin da aka goge mata jiki gabaki daya. Sake shiga tashin hankali su fetto da likitar sukai harma da ‘yarta sbd hatta ita Haile din hukunci zai iya hawa kanta dan babban tsatsauran dalilin daya saka wannan tsaurin yake a masarautar lokacin haihuwan kwace mace shine hana cutatar da kowace jaririn da zaa haifa ko uwarsa kokuma sace jarirai musayarsu dan haka baa yanzu wannan dokar take ba tin asalin asalin kafa masarautar yake. Jiri ne sosai da rashin isashen jini ke Neman zubar da ita amma a haka suka riqeta dan suma bazasu taba son imebetin ta haihu batareda sultan yasan an samu magajin BOYEM ba, Taku daya biyu sukai suna daga qafafunsu su hudun a tare zasu fito dakin wata kakkarfar sautin qarar da baa taba kada wa ba tin tsawon shekarun da sultan YASAR ya hau mulki bace ta ratsa kunnuwansu cikin sanyi da rikitaccen yanayin daya saka dukkaninsu Sakinta cikin mugun firgita da ficewa hayyacin dan kuwa sautine dayake fadawa BOYEM da duniya gabaki daya MAGAJI kuma ZAKIN BOYEM ya sauka a duniya tsohuwar imebeti sabuwar wishmah AYANAH GHAZ ta haifosa. Shigar sautin kunnuwan Sultan YASAR da gabaki daya manyan masarautar boyem a lokaci daya suka zube qasa suna yiwa Allah sujjada batareda ma sun sani ba, Haile kuwa Numfashi daya ta fitar bugun zuciyarta ya tsaya cak sakamakon sautin sakon daya ratsa kunnuwanta ya Harba cikin kwakwalwanta ta zube a gurin jaririn hannunta yana subucewa daga hannunta zuwa qasa, Cikin wata gaggawa da tashin hankalin dayake Ninkuwa Akan mugun shock din dasuke ciki fetto ta tare babyn koina na jikinta na rawa da kakkarwa, ‘Yarta Aslam ce tayi saurin tarota jikinta itama jikin nata yana rawa sosai da firgici tareda tsananin tsoro sukai qasa har ita har mahaifiyar tata sbd batada karfin da zata iya riqeta tinda jikinta a sake yake kaman babu rai a jikinta, Dr Kadee ce tayi saurin bin Aslam din qasa tana tayata riqe Hailen itama jikinta rawa yakeyi da firgicin yanda duk wahala da azabar da suka sha ta tashi a iska labarin haihuwan Ayanaah ghaz ya fara shiga kunnuwan sultan YASAR da qasar BOYEM harma da duniya gabaki daya. Fetto babyn ta rungume jikinta tareda budesa sa sauri taba duba idan yana raye babu abinda ya samesa daga faduwar taga lafiyarsa kalau sedai tinda aka haifesa baya wani kuka saida ya fadin ya fasa kuka sosai Wanda ya sakasu sauke ajiyan zuciya suna tattalar HAILE din dan maidata shimfida a bata taimakon gaggawa. ***A daidai wannan lokacin kuma sautin qarar ya ratsa kunnuwan Zuhrah dake Zaune daqyar sbd azaba da rashin lafiyar da kowace gabar jikinta keyi a cikin wani irin kurkuku mara Kyan gani, Tinda aka sanar da Masarautar kaf cewa imebeti AYANAH GHAZ na naquda ta tashi Zaunen idanuwanta dake ciwo basa gani sosai ta bude su tareda daga Kai sama ta qurawa sama ido tafara jerowa Ayanah da abinda zata haifa addua jikinta na rawa tana fadawa Allah adduarta Akan yar uwarta Bata Dena addua da fadawa Allah ya tsayu Akan rayuwar babyn ayanah dinta ba har saida sautin ya ratsa kunnuwanta Wanda ya sakata rufe idanuwanta ahankali tana silalewa qasa kwance tareda fashewa da Wani irin kuka mai ratsa zuciya tana gode wa Allah da bai karbi ran ayanarta gurin haihuwa hakama wata irin tsananin kewarta da kaunar son ganinta a lokacin ta saka sabbin hawaye gangaro mat a tana Jin tsananin so da ganin abinda Ayanah ta haifa musu ta rungumesa a jikinta taji duminsa tareda sakawa rayuwarsa albarka da fada masa sun yafe masa ita da ‘yan uwanta da basa raye sbd kaddarar haihuwansa a jinin BOYEM ce ta lalata tasu rayuwar da babu gyara a cikinta har abada. Rufe idanunwata tayi hawayen data manta rabon datai yi su sbd kuka ma kansa ya gujeta sai Ayau din datake Jin kewa da tsananin son Ayanah da ‘danta suna ratsata. ****A kuma wannan lokacin ne sultan YASAR ya dago daga sujjadarsa ya daga hannu sama yayiwa Allah godia yana jerowa dan nasa addua me tsananin karfi, Danyen zinari aka fara fitowa dashi a tray mai shegen kyau aka fara kyautarsa a matsayin tukuici hakama duka manyan dake cikin farin ciki mai tsanani da annashuwa suka fara gabatar da tukuici ga AYANAH GHAZ da kyautar data ringa girgiza mutane da tabbatarda Ayau burin qasar BOYEM ya cika na shekaru, Ko da tenya ta fito daga babban kofar fitowa bangaren Wishmah gabaki daya wasu irin securities ne da bayin da zasu rakata har zuwa fada Sbd Mai BOYEM dayake hannunta. Gabaki daya Wani irin Juyawa tenya taji kanta na yi sbd tarin bayi da securities da suka cika hanyar dan kawai rakiyar Magajin BOYEM ga mahaifinsa. Kafafunta sanyi sukeyi mata a duk lokacinda tayi Taku daya na tafiya zuwa fadar mai girma sultan YASAR dauke da jaririn dayafi kowane ‘da daraja a qasar BOYEM yana dunqule cikin farin lallausan bargon daya babu hannun Wanda ya shiga duniya Bayan nata saiya shiga hannun mahaifinsa kafin ma ya shiga hannun mahaifiyar data haifesa, Kai tsaye hanyar fada suka isa babyn na rungume a jikin Tenya data ke Jin sabuwar duniya ce yake kafuwa a BOYEM daga lokacin da ‘dan nan ya gado duniya. Isowarsu bakin kofar fadar da Wani irin tsit akai tareda wangale mata kofa Sauran securities da bayin suka tsaya daga kofa ta sako kafarta ta dama ta shigo tana Takawa cikin nutsuwa tana nufar karagar mulkin BOYEM da sultan yake Kai idanuwansa masu tsananin kyau da kwarjini suna kan hannuwanta biyu dake rungume da hasken dayake tsaya zuciya da idaniyarsa, Dukkanin Wanda yake cikin makekiyar fadar da Taku ne me yawa kafin Ka isa karagar daga bakin kofa kowa idanuwansa Akan hannun tenya yake suna fidda silallan zinari a gabansu suna ajiye wa qasa inda duk tenya ta taka ta wuce matsayin tukuici gareta ita kanta Wanda hakan ke saka kafafun tenya rawa da farin cikin datake Jin kaman zata some

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});