Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tabbas burinsu ya gama cika na duniya. Masarautar da babu kamarta a iko da tarin mulki da arzikin dayafi na kowace Masarauta tarihi, Idan har BOYEM ta karbi bayinsu to tabbas zasu shiga cikin littafin tarihi da ko Bayan shudewansu zaa San kusra. Jirginsu ahakali ya daga daga nan yana keta wa tareda Kama hanyar ruwan da zasu tsallake sama da nahiya hamsin kafin su isa nahiyar BOYEM. ********* tafiya me nisa akai ta kwana da wuni baa gama fita nahiyar dajin ANJOM ba wadda a qalla sai sunyi kusan sati kafin su fita dajin. A wannan kwana da wunin babu wanda ya farfado a cikinsu Ayanah saida aka kuka wuni tukuna suka fara farfadowa shima sbd ruwan da aketa zuba musu ne masu tsananin sanyi. Suna bude idanuwansu cikin Ayanah ce ta fara bude ido taga inda take cikin wani irin rikitaccen karfin da baifi ma jaririn rago ba ta yunkura tana tashi amma bata iyawa sosai, Sunan Abaas tafara ambata cikin dan karfin datake dashi tana dudduba gefenta dataga mutane barkatai sama da Dari duk wasu a kwance. ‘Zuhrahhh,Abaas,Nurat,Sakinah…….. Haka ta ringa jerosu tana kiransu jikinta na Wani irin mummunan rawar tashin hankali. Zuhrah ce ta fara jiyo Ayanah din da sauri itama t bude idanuwanta tana kwala sunan Ayanah din da dan karfi hankalinta a tashe ko gani batayi ta miqe tana kokarin takawa ta kife sbd kacar dake kafarta. Bude ido tayi a inda ta fadi sai idanuwanta suka sauka Akan Abaas cikin sauri ta cakumosa tana kwala kiran Ayanah. Ayanah gurin ta rarrafo ta iso suka rungume juna da karfin gaske suna jin sassauci. Nurat suka fara kira itama tareda sakina sai kuwa gasu sun gani a guri daya take suka rungume juma kaman Ana partyn ‘yayan aljanu sbd yanda suke hada qasusuwan jikinsu suna rungumewa. Can Kurya suka rakube inda baida haske sbd basason Abaas na bayyana sosai kada tsautsayi yasa a gane duk da bazaka taba kallansa kai tsaye kace ga ba macen bane suka maqale juna a zazzaune kowannesu da kaca a kafansa. Tsoro ne zuciya da gangar jikinsu sbd sun gama tabbatarda sun Riga sun zama bayi, Sun zama bayinda har abada basu yancin rayuwarsu sai yanda akai dasu, Sun rasa sunansu,sun rasa asalinsu rayuwa kuma yanzu sedai wadda aka zaba ko hukuntar musu. Bude kofar qaton dakin da suke akai daga sama kofar take. Kallo wanda ya bude kofar yayi musu tsaf kafin ya fara Jeho musu daurin gayar tuwon alkama da akai da nono. Masu dan karfin cikinsu take suka fara ruguwan Abinci suna tura Bakinsu cikin tsananin yunwa da ficewa hayyaci. Sakinah ma cikin karfin Hali ta yunqura tana wawaso abincin tana jefo musu take jikinsu na rawa suka fara sararsa suna Turawa Bakinsu hannuwansu na rawa. Zuhrah dataji kaman bazata iya tsayawaba yake itama ta rarrafa ta fada cikin wawason tana Turawa bakinta a haukace. Abaas ma fadawa yayi hakama Ayanah da Nurat Take suka zama kaman mahaukata kowa wawa yakeyi yana Turawa bakinsa a haukace. #MAMUH #BEST STORY #BEST LOVE #ROMANCE #ROYALTY HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 12 A cikin Hali na wawason suka ringa Turawa Bakinsu ko taunawa basa yi hadewa kawai sukeyi yana wucewa maqoshinsu da wani irin karfin gaske, Wani irin kuka hanjinsu keyi na samun abinda suka dade basu samuba wato abinci, Danne juna ake yi sosai Ana yiwa juna rauni da hakan suka samu suka cika cikinsu sedai kusan dukkaninsu sun samu rauni dan haka suka rarrafa gefe suka rabe suna dunqulewa sbd tsananin ciwon ciki daya taso musu. A kwance suka wuni ba lafiya sosai sbd ciwon ciki da lafiyarsu da daman babuta yanzu, Tsakiyar dare haka aka sake zuwa aka kawo abincin Ana jeho musu suna wawaso sedai wannan karan ba kowane ya iya tasowa ga abincin ba sbd kusan duka dakin basa da lafiya dan kuwa duka kusan ciwon su daya ne ciwon ciki sbd dade wa me tsayi ba abinci, Zubewa suke son yi kwance su jujjuya ko azabar ciwon cikin zai rage amma dakin babu gurin da kowa zai samu ya kwanta sedai suyi rayuwar zama a cikinsa ko bacci sedai kayi daga Zaune. Dan haka su Ayanah babu Wanda ya iya zuwa cin abincin tsakar Daren se Nurat data fada cikin masu wawan tayita ci da hauka itama sbd rashin cikakken hankali ne kuma duk anji mata ciwo sosai hada bakinta aka fasa yana jini suna kallo babu me iya motsawa saida ta koshi dan kanta ta dawo cikinsu. Kwantar da kansu sukai a kafadun juna suna sake lafewa jikin juna da babu wani sauran taushi na tsoka sai qashi amma su a gurinsu hakan shine mafi nutsuwa da kwanciyan hankali Jinsu a jikin juna, Amai wasunsu suka fara wanda ya hargitsa numfashin dasuke shaqa a gurin, Amai sosai kowa yakeyi haddasu Ayanah din saida dukansu suka galabaita amma a hakan baa bude su ba saida safe gari ya waye sosai aka bude su haka aka ringa zubo musu ruwa masu yawan gaske daga sama Ana wankesu kaman dabbobi, Bakinsu suke budewa ruwan na shiga har sukasha sosai kafin ruka zauna ruwan na dukansu da ake zubowa har jikinsu ya wanke tas. Kowa saida jikinsa ya wanke kafin aka fara Fiddosu daya bayan daya daga dakin ana Jere su a fili. Babu me iya miqewa tsaye sosai sbd yunwa da wahalar data gama cinyesu, Hasken sararin samaniya suke kalla yana kashe musu idanuwa sbd duhun da suka fito cikinsa, Kirgasu aka fara yi Ana daya bayan daya Ana raba maza daban mata daban Wanda anan hankalinsu ya tashi tsoro da fargaba suka shigesu Ayanah ta miqa hannu cikin na Abaas da dukkanin jikinsa yake rawa sbd fargaban kada a ganesa, Su duka rawa jikinsu keyi dan Ana gane Abaas mutuwa ce tahau kansa, Qanqame hannunsa Ayanah tayi shima qanqame nata tayi Zuhrah kuwa mannewa tayi a jikinsa itama tana riqe sa suna kokarin hana bayyanar tsoronsu da fargabansu. Shi Kansa Abaas zuciyarsa cikin wani mummunan Hali take na halin da zasu shiga idan asirin hakan ya tonu. Duk Wanda aka Kirga sai an masa sheda a gefen hannunsa da wani karfen wuta. Ana zuwa kansu Nurat aka fara fizgo wa aka kirqa baa tsaya komaiba aka manna mata karfen wuta a gefen hannu Wanda ya sakata qwalla wata gigitacciyar qara tana zubewa a gurin. Cikin firgita Ayanah tayi kanta zata tarota tayi mummunan kife wa kanta na buguwa da katon drum din ruwan dake gurin Wanda ake watsawa duk Wanda ya sume gurin ruwa sbd azaba. Wani Juyawa kanta ya ringa yi sbd bugawan da yayi bata dawo hayyacinta ba taji saukar azababbiyar azaba Akan gefen hannunta Wanda ya sakata somewa a gurin itama. Motsawa Abaas yayi da sauri yana yin kanta itama shima ya kife sbd sarkan dake kafarsa hakama Zuhrah. Anan aka mannawa kowa tasa Shedan cikin azaba suka dunqule suna fidda Wani irin zufa Zuhrah saida ta yanka Wani irin Ihun azabar da bata taba jiba, Abaas duk tsananin azabar dayaji rana ratsa jini,tsokar jiki,qashi da kwakwalwansa kasa ihu yayi sbd Alkwarin da sukaiwa juna na har abada idan basu fita

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});