Chapter 55
Chapter 55
batareda y kyafta ba dan kuwa wani abin da bai taba ji ba yaji ya soki kirjinsa yana ratsawa na asalin girgiza da mamaki, Bai taba mamakin samun ciki ga mace dayake kwana da ita ba sai kan Ayanah GHAZ wadda ya dauke idanuwansa daga tafin hannun nata ya maida Akan fuskarta data dago ahankali itama Jin shiru idanuwansu suka shiga cikin na juna ya tsareta tsaf da idanuwansa yana kasa motsawa, Duk hadarin dayake cikin samun cikinsa Reno da haihuwansa ya sani Shiyasa sai kakkarfan tsarin Allah suke labari, HAILE batada imani ko tausayi ko kadan Akan kishi da tsananin cika burin duk abinda take so amman bai taba damuwa ba dan itace macen da ikonta yakai tayi duk abinda take so dan itace uwargida kuma mace mafi daraja a BOYEM kasancewanta matarsa kuma bazai taba goge hakan ba amma kuma bayajin Ayanaah GHAZ zata iya wannan rayuwar hadarin, Hannunsa ya miqa ahankali Akan tafin hannunta ya dauki silan ya damqe a tafin hannunsa ya bude Baki cikin nutsuwa sosai yace ‘Ina tayaki Murnar daukan jinin BOYEM, Ina maraba da duk abinda zaki Haifa Ayanah Ghaz.’ Zuru tayiwa idanuwanta akansa sbd kasa fahimtar abinda yake nufi ta kuma kasa bude Baki ta tambaya sedai ta samu kanta a tsananin son fahimtar me hakan ke nufi sbd Wani irin nauyin da kirjinta yayi Abinda ya fada mata shine abinda ake fadawa kowace macen amma ganin irin dauke wutar datai ya sakasa Dora mata da cewa ‘Ina fatan cikin dayake jikinki ya zamo na cikar burina dana qasata gabaki daya’ #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 36 *_ZUZEAM VENTURES_* 08144015291 Bononza bononza Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah -Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani, -Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma, Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k. Zuzeam ventures 08144015291 ******* Wani irin jiri ne ya dibeta me karfin gaske daya sakasa tarota jikinsa yana rungumeta sosai a cikin jikinsa Wanda a yake yaji yana Jin tamkar karfin Mararta datai tudu. Ajiyan zuciya ya sauke yana miqa hannunsa ahankali cikin rigarta zuwa mararta da taurinta ya tokaresa ya shafi cikin a Karan farko kenan rayuwarsa daya shafi cikin tsatsonsa, Lumshe ido yayi tareda jan wani Numfashi mai dumi ya bude ido tamkar yana buge a kanta, Jajir idanuwanta sukai zuciyarta na wata irin harbawan datake nunawa har a kirjinta ya zubawa kirjin ido, Wasu irin hawaye masu tsananin Zafin gaske ne suka gangaro daga idonta suka sauka Akan fatar hannunsa yana kallo bai motsa ba baice komaiba sai kawai yaji sautin kukanta mai tsananin ratsa zuciya ya fasu ta qamqamesa tana kukan jikinta har wata rawa yakeyi tana cusa kanta a kirjinsa. Bai motsa ba baice komaiba kukan ne kadai sautin dayake tashi a dakin Wanda ya sakasa tinani Kala daban daban sautin kukan na ratsa kunnuwansa zuwa cikin kansa da babu komai a cikinsa yanzu Bayan na saiya tabbatarda ta Haifa jininsa koda bazai zo da rai ba saiya kuma mata Wani cikin amma tabbas yanason jininta a cikin yayansa. Kuka sosai tayi a jikinsa har karfinta ya qare tayi lahu dukkanin tinaninta ya toshe babu komai a cikin Kanta empty yake tas, A wannan daren babu abinda ya shiga tsakaninsu a Karan farko haka suka kwana ya sakata a jikinsa sosai dumin jikinta kadai yana basa nutsuwa da sukuni. Asubar fari fitowan Ayanah ta saka su tenya gyara tsayuwarsu jiki duk a mace sbd wannan shine zuwansu na karshe. Tin daga duhun doguwar hanyar isa palon sa na farko tenya zubawa Inuwar Ayanah din ido tana kalla cikeda Wani irin sanyin rashin samun yanda taso, A darare Ayanah take tako wa kafafunta sun mata Wani irin nauyin gagarumar damuwan data kame duka gabban jikinta da idanuwanta tareda kwakwalwanta ko gani sosai batayi take isowa. Kyallin dayake haskowa daga hannuwan Ayanah dan dake gaba ya saka tenya bude idanuwanta da kyau cikeda tsananin tsoro da mamaki sbd babu macen data taba samun ciki ta koma shimfidarsa a tarihi idan ba matansa ba dan haka ganin silallan zinari kaya guda a hannun Ayanah dake gap da rasa ranta sbd tashin hankali da qunci ya sakata Jin kaman tsoro n kamata sbd alamar cigaba da zuwanta tiraka kenan maana indai tenya ta fahimci sakonsa daidai kariya ce ga Ayanah da cikinta dan kuwa cigaba zuwanta na nufin babu Wanda zai zan da akwai ciki a jikinta kenan. Rawa kafafun tenya suka fara dan kuwa wannan lamari ne me girma ke shirin faruwa boyon ciki a masarautar har zuwa haihuwansa. Zufa ta sharce tana tare Ayanaah data kusa faduwa sbd jiri take suma Sauran bayin suka matso dan gaggawar barin gurin da ita, Sakinah kuwa tinda idanunwata suka sauka Akan tukuicin kwanciya da ake bada wa kullum taji zuciyarta tana sanyi da samun nutsuwa godia ta ringa jero wa sbd babu ciki kenan a jikin Ayanah din. Cikeda kulawa aka isa da ita bangarenta daqyar tayi sallah ta sunkuyar da Kai ta fasa kuka mai cin zuciya tana dagawa Allah hannuwanta biyu da Neman sassaucin wainanna kaddarorin nata da basa qarewa daga wannan se wannan dan ayanzu bata San ta ina zata faraba da ciki a jikinta, Bata taba Jin zata iya cigaba da rayuwa a BOYEM ba daga ranar da Allah ya bata ikon fiddo da jininta Zuhrah daga kurkuku, Bata taba Jin kaunar cigaba da rayuwa anan din ba daga ta samu yancin fidda tata yar uwar amma yanzu ga jinin BOYEM a jikinta datasan babu ta yanda jinin BOYEM zai taba barin BOYEM hakama itama batajin zata iya Hana kanta tsananin son abinda zai fito daga cikinta ba, Wace irin kaddara ce wannan zata kawo yarta duniya ta fuskanta a matsayin yar imebeti. Kuka takeyi sosai tana Neman sassauci a gurin ubangiji tareda Neman zabi mafi alkhairi, Haka ta wuni batareda barin kowa ya ganta ba ko sakinah sedai ta kawo mata abinci ya juya babu wata magana fata shiga tsakaninsu sbd ita sakinah samun nutsuwarta shine koma menene tinda ba cikine da Ayanaah ba to da sauki, ita kuma Ayanaah bata iya maganar cikin kwata kwata da kowa ma dan kuwa zata sakawa ranta babu komai a jikinta tabarwa Allah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106