Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 102

Chapter 102

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Wani wunin suka kuma yi ba labarinsa haka suka kuma kwana, Ahankali ahankali kwanakin suka ringa tafiya ba boukar ba labarinsa su kuma sun kasa cire tsammani dan haka basu iya tafiya koina ba haka su kaita zaman jira a bakin bodar wadda tin baa Ankara dasu ba har aka fara ankarewa dasu Ana musu kallan mata da miji marasa hankali sbd yunwa da wahalar data Kama jikinsu take fara bayyana dan kuwa basa Wani iya cin abinci suna cikin tsananin damuwa da baqin ciki tareda rashin sanin inda zasu. Ganin an fara saka musu ido ya saka suna cika sati shida a gurin Abaas ya tattarata suka bar qasar sbd Wani jirgin na tahowa Wanda zaiyi gaba binsa sukai sbd a yanzu tafiya Neman yan uwansa zai tafi dan haka a qasar datake gaban wannan zai fara tinda daga nan gaba akai dasu Ayanaah. Tafiya sukai ta kwanaki a jirgin kafin suka isa qasar dake gaban wadda suka Baro, Isarsu qasar dole anan bakin boda ya samu aikin wahala Wanda zaa ringa biyansa dan yana buqatar kudin dazai nema yan uwansa bazai taba dukiyar Ayshaah ba a gurin nemansu, Gida suka samu Wanda ake biyan hayar daki daya ya biya hayar ya saka ayshan a ciki shi kuma yana kwana a kofar dakin. Rayuwa a qasar qunci tafara yi musu sbd yanda ake qyamarsa ganinsa namiji da Kayan maza amma yan kunnen mata ne a kunnensa wainda ya kasa cirewa sbd Ayanah ce ta saka masa su da hannunta bazai iya cirewaba. Ita kanta ayshahh tsangwamarta mutane suka fara yi sbd tana tareda shi babu aure a tsakaninsu dan haka rayuwa tayi mata qunci da nauyi bata cikin kowace irin walwala bare farin ciki dan haka suka bar garin suka koma can quryar qasar Wani garin suka fara rayuwa shima ahankali ahankali zaman yakasa dadi sbd qabilanci na qasar sam basason baqi dan haka dole suka tattara suka sake sauya guri Wanda duk inda sukaje kaman mahaukaci haka Abaas ke Neman yan uwansa. Shekara kusan guda da rabi sukai a qasar suka barta gabaki daya zuwa qasa ta gaba Wanda itama aikin wahalar gaske yakeyi wanda yake cin lafiyarsa sosai sbd duk wannan lokacin aikin wahalar gaske yake a rayuwarsa dan rufa musu asiri kuma har lokacin dukiyarta na nan wadda tace ta basa halak malak amma ya kasa tabawa sbd yanason ya Nemi inda zai ajiyeta dan bata rayuwar kwanciyan hankali da nutsuwa amma abin ya gagara. Ahankali suka fara Gagarin rayuwa a qasashe gurin Neman su Ayanah Wanda zuwa yanzu rayuwarsa ta qarasa macewa gabaki daya sbd ciwon wahala da azabar rayuwa da qunci da suka taru suka rufar masa dan haka ya samu qasa me dan nutsuwa yace zai siya mata gida y ajiyeta tayi rayuwarta ta huta da binsa gararin duniya kada ta qare rayuwarta kamar tasa ta mutu a banza. Kasa yadda da hakan Ayshaah tayi sbd bazata taba iya rayuwa ita kadai babu sa ba sbd a yanzu shine t Rabin jikinta rayuwarta, Shine kadai hasken dayake rayuwarta shi kadaine Wanda rayuwarta take dashi dan haka ta shirya mutuwa a gurin Gagarin duniya tareda shi, Ta shirya rayuwa da mutuwa tareda shi ko an inane ko awa ce qasane zata iya zama dashi. Da wannan suka fada qasar BOYEM Wanda Sam babu ta yanda zaa barsu su shigeta kusan watan su uku anan babu damar shiga qasar dan haka suka juya suka bar qasar. A border ta farko da baa shiga qasar BOYEM aka daura musu aure sbd hanasu gurin zama da akai koina garin sbd basada aure dan haka suka daura aure Wanda har cikin zuciya da ransu suna tsananin son junansu hakama sun shirya rayuwa da mutuwa a tare, Aurensu ne ya kawo wata yar nutsuwar rayuwa a rayuwarsu data cikin tsananin duhu da qunci tareda kadaici, Kusanci da sabuwar shaquwa da kauna tareda so me tsananin gaske sukewa juna suna sake Jin karfin gwiwan fuskantar rayuwa. Bayan wata uku suka bar BOYEM sakamakon cikin daya bayyana a jikin Ayshaah, Cikin ya taho mata da rashin lafiya sosai dan haka tafara wata irin rama taba kofewa alaman jininta yana yin qasa dan haka Abaas ya sadaukar da rayuwarsa da kudirin sa dan bata nutsuwan rayuwan daya kamata kodan abinda zasu haifa kafa suyita yawon duniya dashi dan haka suka juya inda suka fito, Shima kirgen garuruwan da suka Baro a baya tsawon shekaru lokacin da aka dauko su daga garinsu ya fara yi dan komawa qasar sa garinsa gidansu da iyalinsa sbd matiqar Ayanah tana raye to tabbas yasan zata je nemansa a cikin duniya kokuma anan gidan mafarinsu dan haka zai jirata daga yanzu har ranar da Allah zai dauki rayuwarsa. *****tafiyar watanni sukai nai cikeda wahala da ukuba da tsinkewan zuciya ga yanayin ayshahh kafin Allah ya iso dasu dajin garinsu daya sha matiqar wuyar gaske kafin ya gane hakama dukiyarsu tayi qasa dan haka Koda suka iso ANJOM GHAZ cikin Ayshaah ya tsufa yakai wata takwas. A garin ANJOM babu mutane sosai sbd garin ya Riga ya mutu dan haka babu wata daula da tatttalin arziki kaman baya amma akwai kwanciyan hankali dan haka babu wahala ko tashin hankali aka karbesu tinda ansan waye shi hakama duk da shekaru sunja kamanninsa basu sauyaba. Babu kowa a fadar mahaifinsa dan haka Sauran dukiyar daya taho da ita ya bayar aka dan yi gyaran dazai yiyu suka shiga batareda tsoro ba suka zauna tareda kokarin daga ANJOM. Kokarin dayazo dashi da qwazo ya saka jamaar garin samun kuzari da qwazonsu suma ya dawo take garin ya fara komawa ANJOM dinsa na baya a bisa mulkin ABAAS GHAZ din. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 11:19 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 68 ANJOM GHAZ ta dawo ANJOM dinta duk bazata taba komawa ANJOM din baya ba amma Abaas yayi iya kokarinsa ya sake kafata da dukiyarsa da karfinsa da lafiyarsa datake qasa sosai amma ya tsayu ya kasa barin ciwon kirji da zuciyar dake damunsa yakai sa qasa, Ayshaah ma ta samu rayuwar kwanciyan hankali da nutsuwar da Abaas ke fatan ya bata sedai yanayinta itama sai ahankali lafiyarta tayi qasa sosai musamman da cikinta harya wuce watannin haihuwa bata haihuba dan haka aka ringa kawo mata addua da maganin al’adarsu tana sha, Kauna da soyayya me girma tareda wata irin tsafta da nutsuwa take tsakanin Ayshahh da Abaas Wanda kusan duk ANJOM ansan irin son dayake mata da irin yanda ita kuma ya kere mata komai da duniyarta harma da rayuwarta dan haka yanayin jikinta ya saka duk Wanda yake garin mutuwar jikin halinda Abaas yake ciki Akan rashin lafiyarta. Cikinta na cika wata goma sha daya cif ta Wanda yayi daidai da wata su uku cikin na hudu da dawowa ANJOM da samun rayuwa me nutsuwa Bayan shekarun gararin duniya da gwagwarmaya a qasashe cikin rashin gata hakama shekaru biyar cif da rasuwarta mahaifinta ta haifi ‘yarta,yar Abaas,jinin ghaz,hasken idaniyar mahaifinta a duniya wadda tana haihuwarta a idanuwanta kadai ta kalleta ko a hannunta Allah bai bata ikon daukanta ba tabar duniyar ta tafiyarta tabi mahaifinta Wanda bata taba Dena kewa da radadin rashinsa

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});